Gwamnati Ta Gaza Shawo kan Rikicin PENGASSAN da Dangote, An Tashi Taro Baran Baran
- Ƙungiyar PENGASSAN ta ce ba za ta janye yajin aiki ba har sai an mayar da ma’aikatan da matatar Dangote ta sallama
- Rikicin ya samo asali ne daga korar ma’aikata fiye da 800 da PENGASSAN ke cewa an kore su saboda shiga ƙungiyar kwadago
- Duk da umarnin kotu da tattaunawa da gwamnati, PENGASSAN na ci gaba da matsayinta, tana jiran sahihin sulhu
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Ƙungiyar manyan ma’aikatan kamfanonin iskar gas da man fetur, wato PENGASSAN, ta bayyana cewa tana nan daram a kan matsayinta na ci gaba da yajin aiki.
Kungiyar ta jaddada matsayarta ne duk da tattaunawar da aka yi da gwamnatin tarayya a ranar Litinin, 29 ga Satumba, 2025.

Kara karanta wannan
Gwamna ya shiga rikicin Dangote da PENGASSAN, ya fadi abin kunyar da zai faru ga Najeriya

Source: Facebook
BBC Hausa ta wallafa cewa tattaunawar, wadda aka gudanar da jagorancin Ministan Kwadago na Najeriya, Mohammed Dingyadi, ba ta haifar da maslaha ba.
Dangote: PENGASSAN ta ci gaba da yajin aiki
Jaridar Vanguad ta ruwaito cewa bangarorin biyu, wato Dangote da PENGASSAN sun tashi bdaga taron sulhu aran-baran ba tare da cimma matsaya ba.
PENGASSAN ta shiga yajin aiki ne sakamakon korar ma’aikata kimanin 800 da matatar Dangote ta yi, wanda ƙungiyar ke kallon keta hakin ma’aikata da tauye yarjejeniyar kwadago.
Shugaban PENGASSAN na reshen Adamawa, Kwamred Injiniya Dauda Adamu Aliyu, ya ce kungiyar ba za ta janye matakin yajin aikin ba har sai an mayar da ma’aikatan da aka sallama.
Ya ce:
“Matatar Dangote ba ta nuna wata alamar nadama ba tukuna, kuma muna so a dawo da ‘yan’uwanmu da aka kora kafin mu tattauna wani janye yajin aiki."
PENGASSAN: Dangote ya shigar da kara kotu
A yayin da ake ci gaba da rikicin, matatar Dangote ta garzaya kotun ma’aikata da ke Abuja inda ta samu umarnin dakatar da yajin aikin.
Haka kuma matatar Dangote ta samu nasarar samun umarnin kotu da ya hana PENGASSAN katse iskar gas da ɗanyen mai zuwa matatar.

Source: Getty Images
Kotun ta ce Dangote kamfani ne mai zaman kansa wanda ke da lasisin sarrafa da raba mai a Najeriya, don haka ana bukatar a bi doka wajen warware sabani.
PENGASSAN ta ce tana da niyyar komawa tattaunawa idan an kira su da aniya mai kyau, amma har yanzu tana jiran matakin sulhu daga bangaren matatar Dangote.
Ta ce:
“Za mu sake tattauna wa a kwamitin zartarwa kafin mu yanke shawarar yadda za mu ci gaba da fuskantar lamarin."
Shawarar Ndume kan rikicin Dangote da PENGASSAN
A wani labarin, mun wallafa cewa Sanata Ali Ndume ya shawarci Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, da ya ɗauki mataki mai tsauri kan rikicin matatar Dangote da PENGASSAN.
Ya bayyana cewa alamu sun tabbatar da PENGASSAN na yajin aiki ne domin bukatar kashin kai, amma ba ta da hurumi a kan yadda kamfani mai zaman kansa zai gudanar da aiki.
Ndume ya nemi Shugaban Kasa ya yi amfani da ƙarfinsa wajen kawo karshen sabanin, har da rushe kungiyar manyan ma'aikatan mai, PENGASSAN idan akwai bukatar hakan.
Asali: Legit.ng

