Duniyar Musulunci Ta Yi Rashi: Babban Malamin Addini Ya Kwanta Dama
- Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya bayyana bakin ciki bisa rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci na Ilorin a jihar
- AbdulRazaq ya jajanta wa iyalai, almajirai da mabiyan malamin, inda ya bayyana shi a matsayin mutum mai tasiri da gagarumar gudummawa
- Gwamnan ya yi addu’a Allah ya gafarta masa, ya ba shi Aljannah Firdaus, tare da ba iyalansa da mabiyansa juriya kan rashin da aka yi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ilorin, Kwara - Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya yi ta'aziyyar rasuwar malamin Musulunci a jihar.
Gwamnan ya nuna babban bakin ciki bisa rasuwar shahararren malamin addinin Musulunci na Ilorin, Sheikh Hamzah Ariyibi.

Source: Facebook
Gwamna ya kadu bayan rasuwar malamin Musulunci
Hakan na cikin wata sanarwa da gwamnan ya fitar wanda shafin gwamnatin jihar Kwara ta wallafa a Facebook a karshen mako.

Kara karanta wannan
Sardauna: Gwamna ya karrama Ahmadu Bello, ya yi alƙawarin ci gaba da yaɗa manufofinsa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin sakon ta’aziyyar da ya fitar, gwamnan ya jajanta wa iyalan marigayin, almajirai da mabiyansa, inda ya yabawa tasirinsa.
AbdulRazaq ya bukaci al’ummar Musulmi su yi wa marigayin addu'a duba da gudunmawar nagarta da aikin da marigayin ya bayar wajen yada tauhidi.
Ya roƙi Allah ya sauƙaƙa lissafi, ya gafarta masa, ya karɓe shi cikin Aljannah Firdaus, tare da tsare iyalansa bisa kyawawan ayyuka.
Sanarwar ta ce:
"Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bayyana bakin cikinsa kan rasuwar fitaccen malamin Musulunci kuma mai wa’azi na Ilorin, Sheikh Hamzah Ariyibi.
"Gwamnan ya aika da addu’o’i da ta’aziyya ga iyalai, almajirai da masoyan marigayi shugaba na addini."

Source: Original
Rokon Gwamna ga al'umma kan rasuwar malamin
Gwamna Abdul Rahman ya roki al'umma da su yi wa marigayin addu'a duba da gudunmawar da ya ba al'umma da kuma addinin Musulunci.
Ya kara da cewa:
"Ya kuma bukaci al’ummar Musulmi da su samu ta’aziyya da tuna ayyukan alheri da shekaru na jajircewa da wa’azi kan tauhidi da Sheikh Hamzah ya bari.

Kara karanta wannan
Musulunci ya yi rashi: Daraktan agaji na kungiyar Izala, Alhaji Abdullahi ya rasu
"Gwamna AbdulRazaq ya roki Allah ya sauƙaƙa hisabi, ya kuma ba Sheikh Hamzah Ariyibi Aljannah Firdaus, tare da tsare iyalinsa a kan alheri."
Abin da mutane ke cewa kan marigayin
Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu inda suka yi jimamin mutuwar malamin tare da yi masa addu'ar samun rahama a gobe kiyama.
Mafi yawan wadanda suka yi tsokaci sun bayyana marigayin a matsayin mutum mai tawali'u da kuma saukin kai duba da yadda yake mu'amala da mutane kafin ya bar duniya.
Gwamna ya karrama Ahmadu Bello a Kwara
Mun ba ku labarin cewa gwamnan Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ya bayyana aniyarsa ta ci gaba da yada manufofin marigayi Sardaunan Sokoto, Ahmadu Bello.
Gwamna AbdulRahma ya yabawa Bola Tinubu kan gyare-gyaren tattalin arziki da ci gaban jihohi, sannan ya jaddada shirin daukar jami'an tsaron gandun daji don kare dazuzzuka.
Shugaban kungiyar GAMA, Mohammed Tunde Akanbi, ya bayyana goyon baya ga gwamna tare da yabawa ayyukan ci gaba da sake suna fadar gwamnati 'Ahmadu Bello House'.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng