Sardauna: Gwamna Ya Karrama Ahmadu Bello, Ya Yi Alƙawarin ci Gaba da Yaɗa Manufofinsa
- Gwamnan Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ya bayyana aniyarsa ta ci gaba da yada manufofin marigayi Sardaunan Sokoto, Ahmadu Bello
- Gwamnan ya yabawa Bola Tinubu kan gyare-gyaren tattalin arziki da ci gaban jihohi, sannan ya jaddada shirin daukar jami'an tsaron gandun daji don kare dazuzzuka
- Shugaban GAMA, Mohammed Tunde Akanbi, ya bayyana goyon baya ga gwamna tare da yabawa ayyukan ci gaba da sake suna fadar gwamnati 'Ahmadu Bello House'
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ilorin, Kwara - Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya sha alwashin ci gaba da ayyukan alheri.
Gwamnan ya ce zai ci gaba yada manufofi na marigayi Firimiyan Arewa, Sir Ahmadu Bello domin kawo sauyi.

Source: Facebook
Gwamna ya yabawa kungiyar Gamji da mutunta Sardauna
AbdulRazaq, wanda shi ne Sardaunan Ilorin, ya bayyana haka ne lokacin da shugabannin kungiyar Gamji Members Association (GAMA) suka kai masa ziyara a Ilorin, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya gode wa kungiyar bisa yadda suka ci gaba da rike ruhin Gamji, inda ya shawarce su da ka da su daina jajircewa wajen aikin cigaba.
Ya ce:
“Yana da muhimmanci mu ci gaba da yada abin da marigayi Sardaunan Sakkwato ya tsaya a kai, mu karkatar da albarkatunmu ga ci gaba.”
Ya kuma shawarci shugabannin GAMA su kafa reshen matasa don tabbatar da dorewar ayyukan kungiyar a nan gaba, tare da goyon bayansa na musamman.
AbdulRazaq ya yi karin haske kan irin tallafin da yake baiwa GAMA, inda ya tabbatar musu cewa zai ci gaba da tsayawa tare da su.
Gwamnan ya yaba da Shugaba Bola Tinubu bisa gyare-gyaren tattalin arziki da shirye-shiryen ci gaba, yana mai cewa jihohi suna amfana sosai daga tsarin.
“Akwai manyan cigaba a jihohi, yanzu ana biyan albashi akan lokaci, har ma kananan hukumomi suna kaddamar da ayyukan gina tituna."
- AbdulRahman AbdulRazaq

Source: Original
Gwamna ya yi alkawari kan rashin tsaro
Kan batun tsaro, ya ce matsalar tana wucewa, inda ya bayyana shirin daukar jami'an tsaron gandun daji don hana ’yan ta’adda mamaye dazuzzukan jihar.
Gwamnan ya jaddada muhimmancin aikin rijistar masu kada kuri’a, inda ya bukaci kungiyar da sauran jama’a su karfafa wa mutane yin rajista.
Tun da farko, Shugaban GAMA, Alhaji Mohammed Tunde Akanbi, ya bayyana goyon bayan kungiyar ga gwamna bisa salon shugabanci da ya dace da na Sardauna.
Akanbi ya jinjinawa gwamna saboda sake sunan fadar gwamnatin jihar zuwa 'Ahmadu Bello House', a matsayin shaida ta gaskiyar biyayyarsa ga Sardauna.
Mambobin tawagar GAMA da suka raka shi sun hada da Alhaji Saadu Salahu, Dr Ghali Alaaya, Engr Usman Baba Jibril, da sauran fitattun ’yan kungiyar.
Gwamna ya maka tsohon dan majalisa a kotu
Kun ji cewa gwamnan jihar Kwara ya maka Moshood Mustapha da ɗan'uwansa a kotu bisa zargin tayar da zaune tsaye da yaɗa bidiyon ɓatanci.
An gurfanar da su be a ranar Litinin a Ilorin, ammma sun musanta tuhume-tuhumen, inda alkali ya bayar da su beli a kan N5m.
Tuhume-tuhumen sun haɗa da haɗin baki don ƙirƙira da yaɗa bidiyon ɓatanci, wanda zai iya tunzura jama'a kan gwamnan jihar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


