Mukabala: Gwamnatin Kano Ta Gayyaci Masu Yabon Annabi SAW, Ta Kafa Musu Dokoki
- Hukumar tace fina-finai ta Kano ta hana duk wani muhawara tsakanin mawakan yabo musamman na Annabi Muhammad (SAW)
- Gwamnatin jihar ta dauki wannan mataki saboda rikice-rikicen da ake yawan samu game da hakan tare da ba su wa'adi
- Hukumar ta gayyaci shahararrun mawaka biyu, Usman Mai Dubun Isa da Shehi Mai Tajul-Izzi domin tattaunawa tsakani
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Hukumar Tace Fina-finai da Bidiyo ta Kano ta haramta duk wata muhawara a bainar jama’a tsakanin mawakan yabon Annabi Muhammad (SAW) a jihar.
Hukumar tace fina-finai ta kuma gayyaci manyan mawaka biyu, Usman Mai Dubun Isa da Shehi Mai Tajul-Izzi, don su bayyana gaban ta cikin sa’o’i 24.

Source: Facebook
Hukumar tace fina-fina ta gayyaci masu mukabala
Rahoton Daily Trust ya ce hukumar ta dauki matakin ne domin kare rikice-rikice da suke tasowa yayin mukabalar wanda ke kara jawo matsaloli a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan matakin ya zo bayan wata zafaffiyar muhawara tsakanin mawakan biyu da suka shahara ta bayyana a yanar gizo, abin da hukumar ta ce karya doka ne.
An gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi tare da masu shirya muhawarar da aka gudanar a ranar Litinin domin su bayyana a gaban hukumar cikin sa’o’i 24.
Musabbabin daukar mataki kan masu mukabalar
Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha, ya bayyana cewa wannan matakin yana da nufin tabbatar da zaman lafiya, doka da kuma tsari a tsakanin mawaka da masu wa’azi.
Kakakin hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya jaddada cewa duk wata muhawara ta addini daga yanzu ba za ta halatta ba sai hukumar ta amince.
Ya ce hakan zai kawo tsafta a lamarin da kuma kokarin dakile rikici da ka iya tasowa a lokacin ko bayan kammalawa.

Source: Facebook
Matakin da hukumar ta dauka kan lamarin
El-Mustapha ya kafa kwamitin bincike na musamman karkashin Daraktan Harkokin Musamman, Isah Abdullahi, domin tattauna lamarin tare da wadanda aka gayyata.
Hukumar ta gargadi masu shirya irin wannan muhawara cewa hakan karya doka ce, kuma na iya jawo masu hukunci mai tsanani a jihar.
Hukumar ta sake nanata kudirinta na tsara ayyukan masu nishadantarwa a fadin jihar, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da ba su goyon baya.
Ta kuma yi kira da a kiyaye zaman lafiya da hadin kai, domin tabbatar da daidaito da fahimtar juna tsakanin al’umma a jihar Kano.
Gwamnatin Kano ta dakatar da wasu fina-finai
A baya, mun ba ku labarin cewa Hukumar tace fina-finai ta Kano ta dakatar da haska fina-finan Hausa 22 bisa zargin saba wa al’adu da ɗabi’un Musulunci a jihar.
Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha, ya ce doka ta ba su hurumi, kuma suna aiki da jami’an tsaro da malamai don tabbatar da bin ƙa’ida.
An ce ana haska fina finan ba tare da izinin hukumar ba, sai aka dakatar da haska wasu, ciki har da Labarina, Garwashi da Dadin Kowa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

