Yadda Tinubu Ya Nemi Hada Kai da Coci domin Dakile Talauci, Ya Samo Mafita
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sha alwashin bin duk hanyar da ta dace domin kawo sauyi a Najeriya musamman bangaren tattalin arziki
- Tinubu ya ce zai yi haɗin gwiwa da coci domin yaƙar talauci, daidaita rashin adalci da sulhunta al’umman da rikici ya taba.
- Ya bayyana muhimmancin shugabannin addini wajen gina daraja da haɗin kai, inda ya fadi muhimmancin coci wurin gina zaman lafiya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta yi aiki tare da coci wajen yaƙi da talauci.
Shugaban ya ce gwamnatinsa ta himmatu wurin sulhunta al’umma da rikici ya tarwatsa da kuma raba su da gidajensu.

Source: Facebook
Tinubu ya fadi muhimmacin malaman addini
A wajen taron Bishof-bishof na Katolika a Ikot Ekpene, Tinubu ta bakin SGF George Akume ya roƙi shugabannin Kirista su ci gaba da kira ga sulhu, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya ce shugabannin addini na taka muhimmiyar rawa wajen samar daraja da amana, inda ya jaddada coci a matsayin gada ta zaman lafiya da haɗin kai.
Shugaban ya bukaci haɗin gwiwa wajen koyar da ilimi, kare muhalli da ƙarfafa matasa, domin gina al’ummar da ke da daraja da ilimi.
Ya kara da cewa gwamnatinsa ta shiga ofis da burin farfaɗo da buri, ƙarfafa dimokiradiyya da gina ƙasar da za ta amfane kowane ɗan Najeriya.

Source: Facebook
Abin da Tinubu ke bukata daga yan kasa
Tinubu ya jaddada cewa gwamnati ta ɗauki matakai na tabbatar da ci gaban tattalin arziki, hannun jari da aiwatar da sauye-sauyen da za su amfanar nan gaba.
Ya ce mulki na gari ba wai tattalin arziki kaɗai ba ne, illa dai gaskiya, adalci, gaskiya da mutuncin kowane ɗan Najeriya, Punch ta ruwaito.
Ya ce:
"Bari in sake tabbatar muku cewa gwamnatin tarayya a shirye take ta zurfafa haɗin gwiwa da cocin Katolika da sauran ƙungiyoyin addini a manyan fannoni kamar ilimi.
"Za mu ingata kiwon lafiya, walwalar jama’a da koyar da sana’o’i. Tare, za mu iya yaƙar talauci, rage rashin daidaito da kuma gina ƙarfaffun al’ummomi.”
Ya bayyana cewa ba za a bar kowa a baya ba, ko daga birane ko ƙauyuka, babba ko ƙarami, mai arziƙi ko matalauci.
Tinubu ya jaddada cewa gwamnati a shirye take ta yi aiki tare da coci da ƙungiyoyin addini wajen ilimi, lafiya da walwalar jama’a.
Gwamnati ta fasa kakaba harajin shigo da kaya
Mn ba ku labarin cewa gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta saurari korafe-korafen 'yan kasuwa a kan tsarin harajin 4% a kan kayan da ke shigo wa kasar nan.
Ministan Kudi kuma Ministan Tsare-Tsaren Tattalin Arziki, Mista Wale Edun ya ce bayan dogon nazari da tattauna wa, an dakatar da shi.
Edun ya ce wannan ba ya nufin an cire harajin gaba daya, sai dai wani tsari na bayar da damar sake duba al'amarin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

