Magana Ta Kare: Kotu Ta Yi Hukunci kan Shari’ar Tsohon Minista da Budurwarsa
- Kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta yi hukunci kan shari'ar tsohon minista da budurwarsa kan zargin cin zarafinta
- A zamanta, kotun ta hana Hadiza Musa Baffa danganta ɗanta da tsohon Minista Kabiru Turaki daga jihar Kebbi
- Alƙali Adamu Isah ya yanke hukunci cewa gwajin kwayoyin haihuwa ƙarƙashin shari’ar Musulunci bai kamata a danganta shi da tsohon ministan ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Wata babbar kotu a Abuja ta yanke hukunci kan shari'ar tsohon minista, Kabiru Tanimu Turaki da budurwarsa.
Kotun bayar da umarnin dindindin da ta hana Hadiza Musa Baffa danganta ɗanta da tsohon minista Turaki.

Source: Facebook
Alƙali Adamu Isah, a hukuncin da ya yanke ranar 4 ga Satumbar 2025, ya ce Hadiza ba za ta yi amfani da DNA ba, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan
Watanni bayan ya rasu, an gano gidan da tsohon gwamna a Najeriya ya mallaka a Landan
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zargin da ake yi wa tsohon minista Turaki
Tun farko, an maka Turaki a kotu a ne kan zargin cin zarafin tsohuwar budurwar tasa da ta ce ya ci zarafinta kuma har sun haihu tare da shi.
Tun a watan Faburairun 2025 ne aka sake gurfanar da tsohon Ministan ayyuka na musamman, Kabiru Turaki SAN, a kotu kan zargin yin auren bogi da lalata.
Bisa bayanan ‘yan sanda, Turaki ya yaudari wata mata da sunan aure, ya zauna da ita a otal daban-daban har tsawon shekaru har da dirka mata ciki.
Kotun ta bayar da belinsa kan kudi N1m tare da sharadin samun mutane biyu da za su tsaya masa kamar yadda doka ta tanada.

Source: UGC
Kotu ta raba gardama a shari'ar tsohon minista
Alƙalin ya ce hukuncin ya shafi tantance mahaifi na ɗa da aka haifa wajen aure a ƙarƙashin tsarin shari’ar Musulunci da kotu ke bi.
"Kotu ta yi hukunci inda ta hana wanda take kara daga bugawa ko yadawa da danganta danta da wanda ake zargi, Turaki."
Tsohon ministan ya nemi kotu ta dakatar da zargin amfani da ’yan sanda wajen tsoratar da shi daga iyalan Musa Baffa da Uwani.
Hadiza ta zargi tsohon ministan da cin zarafi da kuma watsar da ita bayan ya jefa ta cikin halin ɗaukar ciki tun a wancan lokaci.
Sai dai tsohon ministan ya ce Uwani ce ta roƙe shi ya zama mai kula da ’yarta Hadiza, abin da ya amince ya yi.
Ya bayyana cewa ya kula da ita ba tare da sanin sunan ta an canza zuwa “Turaki” ba, wanda aka yi ba tare da yardarsa ba.
Kotu ta ba da belin tsohon minista, Turaki
A baya, mun ba ku labarin cewa Kotun Majistare a Abuja ta bayar da belin tsohon minista, Kabiru Turaki, SAN, akan N1m bayan zarginsa da yin lalata da wata budurwa.
Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon ministan ayyuka na musamman kan zargin ya yi zaman auren bogi da wata Hadiza Musa Bafta.
Mai shari’a Abubakar Jega ya dage karar zuwa 11 ga Maris bayan da Kabiru Turaki ya karyata dukkan zarge-zargen da EFCC ke yi masa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
