Tashin Hankali: Ƴan Bindiga Sun Sace Ƴar NYSC da Ɗalibar Jami'a, Suna Neman N50m
- Mutane sun shiga firgici a wani kauyen Jos bayan 'yan bindiga sun kai masu hari tare da sace 'yar bautar kasa da dalibar jami'a
- Solomon Dansura wanda 'yan bindigar suka suka sace 'yan matan daga gidansa, ya ce bai taba ganin tashin hankali irin na ranar ba
- Ya bayyana cewa, masu garkuwa da mutanen sun kira shi a waya, suna neman Naira miliyan 50 matsayin kuɗin fansar matan
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jos - 'Yan bindiga da ake kyautata zaton cewa masu garkuwa da mutane ne sun sace wata 'yar bautar kasa da kuma wata dalibar aji uku a Jami'ar Jos.
Miyagun sun yi awon gaba da 'yan matan biyu ne bayan da suka kutsa cikin wani gida a yankin Dongg na karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar Plateau.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun kashe Sarkin da suka yi garkuwa da shi, sun jefar da gawarsa a daji

Source: Twitter
Mista Solomon Dansura, wanda aka sace surukarsa da kuma baƙuwar da take tare da ita, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a Jos ranar Talata, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka sace 'yar NYSC a jihar Plateau
Ya ce masu garkuwar sun shiga gidansa ne ranar Lahadi da daddare lokacin da iyalinsa ke shirin kwanciya bacci.
Dansura, wanda ya bayyana lamarin a matsayin mai ban tsoro, ya ce, mintuna uku bayan ya kwanta bacci, sai ya ji wani motsi ta taga da bai gamsu da shi ba.
Ya ce a nan ne ya fahimci cewa wasu mutane sun shiga gidansa kuma suna ƙoƙarin shiga cikin wani ɗaki don yin garkuwa da mutane.
Ya ƙara da cewa, bayan ya gane cewa 'yan bindiga ne, sai ya gudu ta ƙofar baya don neman taimako, amma da ya dawo, sai ya ga sun sace 'yar bautar kasar da kuma dalibar da suke tare.

Kara karanta wannan
Sa'o'i da sulhu, 'yan bindiga sun rufe masallaci, sun sace masu sallah 40 da Asuba
'Yan bindiga sun nemi N50m kudin fansa
Solomon Dansura ya ce:
“Abin ya daga mun hankali, saboda ban taɓa ganin garkuwa da mutane ba sai lokacin. Surukata ‘yar bautar kasa ce da ke hidima a Bauchi kuma tana shirin yin aure.
"Jami'an sojoji da na 'yan sanda sun zo gidan bayan da masu laifin suka yi nasarar yin garkuwa da waɗanda abin ya shafa.
"Masu garkuwar da mutanen sun kira a safiyar yau, inda suka nemi kuɗin fansa Naira miliyan 50. Sun ce in tabbata na tanadin kudin kafin su sake buga waya."
An ruwaito cewa, wannan lamari ya sake haifar da fargaba a garin Dongg, inda mazauna yankin ke cewa sace-sacen mutane ya zama ruwan dare a yankin.

Source: Original
Fargaba ta mamaye mazauna Jos
Basarake Adagwom Kaze Nyam da shugaban al'umma Nenfort Clifford, sun nuna damuwa kan lamarin, inda suka buƙaci hukumomi su gaggauta tura ƙarin jami'an tsaro don kare rayuka da dukiyoyin jama'a.
Wata shugabar mata a yankin, Franca Diwa, da wani mai fafutukar matasa, Mildred Bako, sun yi gargaɗi cewa, idan gwamnati ba ta gaggauta ɗaukar mataki ba, Dongg na iya zama kufai.
Sun ce duk da garin na da kusancin da birnin Jos, hare-haren 'yan bindiga ya fara tilasta mutane yin hijira, wasu kuma har sun fara sayar da gidajensu.
An sace 'yar NYSC a hanyar Neja
A wani labarin na daban, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun yi garkuwa da wata mai yi wa ƙasa hidima (NYSC) a hanyar hanyar Neja zuwa Onitsha.
An ce an yi garkuwa da Chiamaka Obi, wacce ƴar asalin garin Edenta ne a Okwu Etiti, a ƙaramar hukumar Orsu ta jihar Imo, tare da wasu mutane takwas.
Dan majalisar dokokin jihar Imo, Uche Agabige, ya nuna damuwa kan cewa masu garkuwa da mutanen suna neman a ba su maƙudan kuɗin fansa kafin su sake ta.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
