'Za a Samu Sababbin Attajirai,' Gwamna Zai Rabawa Matasa 8,300 Tallafin N3.5bn
- Gwamnatin jihar Anambra ta shirya tallafawa matasa 8,300 da jarin Naira biliyan 3.5 a matsayin tallafin fadada kasuwancinsu
- Ana sa ran Gwamna Charles Soludo da kansa zai raba kuɗin a ranar 23 ga Satumba, 2025, a cibiyar taro ta kasa da kasa a Awka
- Wannan shi ne kashi na biyu na shirin '1Youth2Skills Plus', bayan da aka tallafawa matasa 5,000 a da Naira biliyan biyu a kashin farko
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Anambra - Matasa na cikin alheri dumu dumu a Anambra, bayan sanarwar gwamnatin jihar na raba tallafin Naira biliyan 3.5.
A ranar Talata ne gwamnatin Anambra, ta ce ta yanke shawarar tallafawa matasa 8,300 da jarin Naira biliyan 3.5 karkashin shirin ‘1Youth2Skills Plus’.

Source: Facebook
Gwamna zai rabawa matasa N3.5bn
Kwamishinan ci gaban matasa na Anambra, Mista Patrick Aghamba ne ya bayyana hakan a cikin sanarwar da aka raba wa 'yan jarida a birnin Awka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mista Patrick Aghamba ya ce tallafin na Naira biliyan 3.5 zai ba wadanda suka samu horo karkashin shirin ‘1Youth2Skills Plus’ damar samun jari.
Ya ce gwamnati na fatan matasan za su yi amfani da kudin wajen fadada kasuwancinsu bayan sun yi nasarar kammala samun horo kan sana'o'i daban daban.
Kwamishina ya shaida cewa, za a gudanar da gagarumin taron raba tallafin kudin a ranar Talata, 23 ga Satumbar 2025 a cibiyar taro ta kasa da kasa da ke Awka.
Gwamna zai raba tallafin kudin da kansa
Sanarwar Mista Patrick Aghamba ta ce:
"Gwamna Chukwuma Charles Soludo da kansa ne zai raba tallafin kudin ga wadanda suka yi nasarar kammala samun horon.
"Gwamnan zai kuma ƙaddamar da wasu shirye-shiryen da aka ƙirƙiro su domin ƙyanƙyasar sababbin attajirai da ƙwararrun ‘yan kasuwa a Anambra."
Kwamishinan ya bayyana cewa wannan ne kashi na biyu na shirin, inda a kashin farko aka tallafawa matasa 5,000 da jarin Naira biliyan biyu.
Baya ga jarin biliyoyin Naira da suka samu, kwamishinan ya ce an ba matasan horo, har suka goge a fannoni daban daban na kasuwanci.
Ya kara da cewa gwamnatin Soludo ta fadada shirin ne domin matasa masu yawa su samu damar shiga, don cika burinsu na fadada kasuwanci.

Source: Original
Shirin ‘1Youth2Skills’ na jihar Anambra
Shirin ‘1Youth2Skills’ shiri ne da aka samar da shi domin ba matasa horo a fannoni daban daban, kamar noma, ICT, dinki, saka, hada gurasa, da dai sauransu, inji rahoton shafin gwamnati.
"Gwamnatin Soludo ta daura damarar mayar da Anambra wata cibiyar kirkire-kirkire, samar da ayyuka da kuma ci gaban matasa, da zai kyankyashe sababbin attajirai.
"Muna godiya ga gwamna bisa fadada wannan shiri, da kuma daukar matakan sauya rayuwa da goben matasan Anambra."
- Mista Patrick Aghamba.
Soludo ya fadi masu sanya matasa a ta'addanci
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnan Anambra ya ce bokaye da malaman tsibbu na yaudarar matasa suna shiga harkokin ta'addanci a jihar.
Gwamna Charles Soludo ya ce tuni ya ɗauki matakan shawo kan wannan babbar matsala kuma an fara bincike kan bokaye da irin waɗannan malamai.

Kara karanta wannan
Albashin N70,000: An gano halin da aka jefa ma'aikatan kananan hukumomi a jihohin Arewa 3
Cikin laifukan da bokayen ke yaudarar matasa su fara har da safarar miyagun kwayoyi da shiga kungiyoyin ƴan bindiga da garkuwa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

