Lamari Ya Girma: Gwamnatin Tinubu Ta Shiga Rigima da X, Facebook kan Sowore
- Gwamnatin Najeriya ta fusata game da rashin ɗaukar mataki kan kan gwagwarmaya, Omoleye Sowore
- Gwamnatin ta gurfanar da Omoyele Sowore tare da Facebook da X bisa zargin laifukan yanar gizo saboda sakonnin da ya kira Tinubu ɗan daba
- Sowore ya bayyana cewa DSS ta ƙirƙiro tuhuma inda ta ce kalamansa sun saba dokokin ƙasar amma ya ƙi goge sakonninsa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Dan gwagwarmaya a Najeriya, Omoloyele Sowore ya shiga gagarumar matsala bayan rubutu a kafofin sadarwa.
Hakan ya biyo bayan rubutunsa da ya soki Bola Tinubu tare da kiran shugaban da dan daba wanda ya ta da kayar baya.

Source: Twitter
Gwamnatin Tinubu ta maka Sowore, X a kotu
Gwamnatin Najeriya ta gurfanar da Sowore, tare da kamfanonin Facebook da X a gaban kotu, cewar Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin ta dauki matakin ne kan zargin laifukan yanar gizo saboda sakonninsa da suka kira Shugaba Bola Tinubu ɗan daba.
An gurfanar da su gaba ɗaya da tuhumar laifuka guda biyar a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Talata 16 ga watan Satumbar 2025.
Barazanar da hukumar DSS ta yi wa Sowore
Lamarin ya biyo bayan barazanar da hukumar DSS ta yi wa kamfanonin X da Meta mako guda da ya gabata, inda ta umurce su su goge sakonnin Sowore ko kuma su sha hukunci.
DSS, wadda ta saba tsare Sowore saboda ra’ayinsa, ta kuma gargade shi ya goge sababbin sakonnin da ke kiran Tinubu ɗan daba.

Source: Facebook
Martanin Sowore ga hukumar DSS kan rubutunsa
Sai dai Omoyele Sowore ya rubuta wa kamfanonin X da Meta, yana kare matsayinsa, ya bayyana cewa wannan kiran na DSS wani bangare ne na tsangwama da cin zarafi da yake sha daga gwamnati saboda ra’ayinsa da ayyukan fafutuka.
Ya kuma amsa wa DSS kai tsaye a shafin X, inda ya bayyana cewa ba zai goge sakonnin ba domin bai saba ka'ida ba kamar yadda ake zarginsa.
A ranar Talata, Sowore ya yada kwafin takardun tuhumar ta hanyar shafukan sada zumunta.
Ya rubuta cewa:
“Hukumar DSS ta shigar da ƙarar har guda biyar a babbar kotu a Abuja kan X, Facebook da ni.
"Suna cewa saboda na kira Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ɗan daba, na aikata wasu sababbin laifuka da suka ƙirƙira suka watsar a cikin zarge-zargen biyar.
“Abu ne mai wuya a gaskata cewa akwai masu hankali a cikin waɗannan ofisoshi da ya kamata su yi wa Najeriya aiki.
"Duk da haka, zan kasance a nan duk lokacin da aka sanya wannan shari’a domin sauraro."
Hukumar DSS ta ba manhajar X wa'adi
Mun ba ku labarin cewa Hukumar DSS ta baiwa shafin sada zumunta X wa'adin awanni 24 don cire wani rubutu na Omoyele Sowore da ya yi.
Sowore ya yi wani rubutu inda ya ke zargin Shugaba Bola Tinubu da karya kan abin da ya shafi cin hanci a gwamnatinsa.
Sai dai Sowore ya yi martani mai zafi kan lamarin wanda ke nuna cewa ba zai taba janyewa daga abin da yake yi ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


