Karon Farko cikin Watanni 7, Naira Ta Tumurmusa Dalar Amurka zuwa Ƙasa da N1,500
- Darajar Naira ta ƙaru a kasuwar hada-hadar kudi, inda ta koma ƙasa da N1,500 idan aka yi musayarta da dalar Amuka a hukumance
- Wannan ne karon farko da dalar Amurka ta rikito zuwa kasa da N1,500/$1, tun bayan da aka yi cinikinta kasa da hakan a Fabrairun 2025
- Masana sun ce shigowar dala daga ‘yan kasuwar ƙasashen waje da kuma tsare tsaren Babban Bankin Najeriya ne silar nasarar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Bayanan Babban Bankin Najeriya (CBN) sun nuna cewa Naira ta lallasa dalar Amurka zuwa N1,497.46/$1, sabanin N1,501.49/$1 da aka yi cinikinta a baya.
Wannan na nufin cewa Naira ta kara daraja da 0.27%, karon farko da kudin Najeriyar ya tumurmusa dalar Amurka a kasuwar canji a cikin watanni bakwai.

Kara karanta wannan
Naira ta rike wuta, darajarta ta karu yayin da asusun kudin wajen Najeriya ke habaka

Source: Getty Images
Naira ta kara dajara kan Dala a kasuwa
A watan Fabrairun 2025 ne aka yi cinikin Naira a ƙasa da N1,500 a kasuwar musayar kuɗi ta hukuma, amma tun lokacin, dalar Amurka ke tashi sama, inji rahoton Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan farfadowar da Naira ta yi ta zo ne bayan mako guda da darajarta ta ke zuwa N1,500/$1, amma tana gaza sauka zuwa kasa.
An kuma samu irin wannan ci gaban a kasuwar bayan fage, inda aka rika cinikin Naira da Dala kan N1,535/$, kamar yadda rahoton CardinalStone Research ya nuna.
Rahotannin kasuwa sun nuna cewa Naira ta kasance tana kara daraja da 0.98% a kowanne mako, inda ta koma N1,501.50/$ a kasuwar gwamnati, da N1,535/$ a kasuwar bayan fage.
A cewar rahoton mako-mako na Coronation, darajar canjin kuɗi a hukumance ta karu da N35.50 ko 2.23%, mafi girma da na kasuwar bayan fage.
Yadda aka samu walwalar Dala a Najeriya

Kara karanta wannan
Maryam Shetty ta shirya gasar Alkur'ani, ta ba da kyautar sama da Naira miliyan 1.75
Rahoton ya kuma nuna cewa jimillar musayar kuɗaɗen waje da suka shigo Najeriya sun kai dala miliyan 550.90 a makon da ya gabata, wanda ya dan yi ƙasa da dala miliyan 567.20 da aka samu a makonni biyu da suka gabata.
Zuba hannun jari daga 'yan kasuwar ƙasashen waje (FPIs) ne suka mamaye kudaden da suka shigo ƙasar, wanda ya kai dala miliyan 303.8 ko kuma 55.15%.
Jaridar Punch ta rahoto sauran hanyoyin da aka samu walwalar dalar sun hada da bangaren masu fitar da kayayyaki zuwa waje (17.61%), da kamfanoni da ba na banki ba (17.57%).
Sauran kamfanoni sun bayar da 4.32%, sannan masu zuba jari na kai tsaye su ba da 3.39%, CBN ya ba da 2.36%, sannan kuma daidaikun mutane sun ba da 0.60%.

Source: Getty Images
Abubuwan da suka jawo faduwar Dala
Masana sun ce karuwar darajar Naira ya samo asali ne daga yawan shigowar kudaden zuba jari daga kasashen waje, da karuwar ajiyar kuɗaɗen waje, da kuma tasirin tsare-tsaren CBN.
Masana a kamfanin AIICO Capital sun ce wadatar dalar Amurka daga FPIs, masu fitar da fetur, da kuma kuɗin shiga daga kasashen waje sun kara daraja Naira.
Ana ganin Naira, a kasuwar hada-hadar kudi za ta ci gaba da samun karfi saboda manufofin CBN da kokarin gwamnati na tabbatar da wadatar dala.
Har ila yau, rahotanni sun nuna cewa ajiyar kudin waje na Najeriya ya karu zuwa $41.69bn, abin da zai ci gaba da karfafa kasuwar da kuma tabbatar da daidaito ga Naira.
Bincike ya karyata Tinubu kan darajar Naira
A wani labarin, mun ruwaito cewa, bincike ya karyata Shugaba Bola Tinubu, a ikirarin da ya yi na cewa ya samu Dalar Amurka tana kan N1,900 a 2023.
Yayin da ya ke jawabin, shugaban kasar ya nuna cewa tsare-taren da gwamnatinsa ta aiwatar ne suka sa Dalar Amurka ta dawo daidai da N1,450.
Sai dai, binciken Legit Hausa, ya gano akasin ikirarin da shugaba Tinubu ya yi game da farashin Dala bayan shekara biyu a kan karaga.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
