Ana tsaka da Maganar Sulhu, Yaran Ado Aliero Sun Yi Wa Sarki Yankan Rago a Zamfara
- Yan bindiga da Ado Allero ke jagoranta sun kawo tsaiko yayin da ake cikin maganar sulhu da yan bindiga a Katsina
- Gungun miyagun karkashin Aliero aun kashe Hakimin Dogon Dawa a Keta, Tsafe Zamfara, tare da sace mutane 40 a masallaci
- Duk da sulhun da ake yi a Faskari, hare-haren sun ci gaba da yawa, ciki har da sace mutane 12 a Bukuyum da 4 a Tudun Moriki
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tsafe, Zamfara - Yan bindiga da Ado Aliero ke jagoranta sun ci gaba da hallaka mutane duk da maganar sulhu da ake yi.
Ana tsoron cewa yaran babban jagoran sulhu a Arewa maso Yamman sun kashe Hakimin Dogon Dawa a Tsafe, Jihar Zamfara.

Source: Facebook
Rahoton Zagazola Makama ya nuna cewa maharan sun yi kisan ne da misalin karfe 4:09 na yamma ranar 15 ga Satumbar 2025.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun kashe Sarkin da suka yi garkuwa da shi, sun jefar da gawarsa a daji
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan bindiga na kisa yayin da ake sulhu
Majiyoyi sun ƙara tabbatar da cewa yan bindigan sun kashe manoma huɗu a Barikin Daji, Ruwan Gizo, Zamfara, da jami’an kwastam biyu a Kebbi.
An tabbatar cewa hare-haren yan bindiga na ci gaba da addabar al’ummomi a Arewa maso Yamma duk da tattaunawar zaman lafiya a Katsina.
A yayin tattaunawar zaman lafiya a Faskari, an ce yan bindiga sun yi wa kwamandan sojoji kwanton bauna amma sojojin sun yi nasarar kare kansu.
Nasarar sojoji kan miyagun 'yan bindiga
Haka kuma dakarun sojoji sun yi wa yan bindiga kwanton bauna a Gatawa, Kankara, inda suka kwace babur da wayar hannu daga hannunsu.
Sojojin kuma sun fatattaki yan bindiga a Sabon Massallaci, Katera, inda bayan haka aka kashe mace daya, an jikkata mutane da sace dabbobi.
Haka nan, yan bindiga sun yi kwanton bauna wa jami’an NSCDC a Dafa, Danmusa, inda suka kashe ɗaya suka jikkata wasu huɗu.

Kara karanta wannan
Sa'o'i da sulhu, 'yan bindiga sun rufe masallaci, sun sace masu sallah 40 da Asuba
Yadda yaran Aliero suka kashe Sarki a Zamfara
An tabbatar da cewa miyagun sun kashe Hakimin ana maganar sulhu da Ado Aliero a kauyen Keta da ke karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.
Wannan hare-haren da aka bayyana da munana, ya kuma kai ga sace mutane 40 daga masallaci a cikin wannan yankin na Tsafe.

Source: Facebook
Katsina: Zaman sulhu da aka yi da Aliero
Fitaccen dan bindiga, Aliero a ranar Lahadi ya nuna fatan samun zaman lafiya a Katsina, Zamfara da yankunan arewa.
Ya ce rugujewar sulhu na baya, ciki har da kama ɗansa, ya sa shi komawa aikata miyagun ayyuka bayan tsawon tattaunawa.
Duk da ikirarin cewa tattaunawar ta Faskari ta zama "na tarihi," hare-haren da yan bindiga ke kaiwa sun ci gaba da yawa.
Shedanin 'dan bindiga ya mika wuya a Katsina
Mun ba ku labarin cewa daya cikin yan bindiga, Isiya Kwashen Garwa wanda ake nema ruwa a jallo, ya rungumi sulhu a Katsina.
Wannan matakin na Isiya ya haifar da shakku a tsakanin mazauna yankin Faskari, saboda sanin tarihinsa na aikata ta'addanci.
Malamin addinin Musulunci, Dr. Ahmad Gumi, ya fito ya yi martani kan mika wuyan Isiya Garwa, tare da fadin fargabar da yake yi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
