Gwamnati Ta Saki Sunayen Likitoci 2 da Take Nema Ruwa a Jallo, Sun Aikata Laifi
- Gwamnatin Akwa Ibom ta saki sunayen wasu likitoci biyu da take nema ruwa a jallo bayan sun bar aiki ba tare da izini ba
- Kwamishinan lafiya na jihar, Ekem John, ya ce gwamnati ta kashe kudade masu yawa wajen horar da likitocin biyu
- Ya ce ko dai su dawo bakin aikinsu, ko su biya kudin da gwamnati ta kashe a karatunsu, ko kuma su gamu da fushin doka
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Akwa Ibom - Gwamnatin Akwa Ibom ta ayyana wasu likitoci biyu a matsayin wadanda take nema ruwa a jallo bayan da suka gudu daga bakin aikinsu a ma'aikatar lafiya ta jihar.
A ranar Litinin, kwamishinan lafiya na jihar, Ekem John, ya bayyana wa manema labarai cewa gwamnatin Akwa Ibom ce ta dauki nauyin karatun likitocin biyu har na tsawon shekaru takwas.

Source: Getty Images
Gwamnatin Akwa Ibom na neman likitoci ruwa a jallo
Premium Times ta ruwaito cewa, Ekem John ya ce daga cikin likitocin da ake nema akwai, Uduakabasi Ita, kwararren likita a fannin binciken cututtuka da hoton X-ray.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai kuma Mfonobong George Bassey, kwararren likita a fannin binciken cututtukan jini, wanda shi ma ake nema ruwa a jallo.
Ya ce likitocin suna da zaɓi na ko dai su dawo bakin aiki, ko kuma su maida kudin da gwamnatin ta kashe wajen daukar nauyin karatunsu.
Gwamnati ta gargadi likitocin 2 da ake nema
Ekem John ya shaidawa 'yan jarida a babban birnin Uyo cewa:
"Za mu bi diddiginsu har sai mun kama su. Babu wata kasa da za su ce da ba za mu iya tuntubar kungiyar likitoci ba, za mu tabbatar sun rasa lasisin aiki.
"Yana da matukar amfani a gare su, su gaggauta miƙa kansu ga ma'aikatar lafiya ta jihar Akwa Ibom, tun kafin fushin doka ya sauka a kansu."
Kwamishinan ya fada wa likitocin su kuka da kansu, kan abin da zai iya biyo baya, domin tuni ta mika lamarin ga majalisar likitocin Najeriya ta MDCN, wacce za ta iya janye lasisin aikin su.
Ya ƙara da cewa, nan gaba, duk wani ma'aikacin lafiya da gwamnatin jihar ta daukin nauyin karatunsa zai yi aiki a jihar har tsawon shekarun da aka amince da su kafin a ba shi izinin yin murabus.

Source: Original
Ƙarancin likitoci a Najeriya
Najeriya na fuskantar matsanancin ƙarancin likitoci da sauran ma’aikatan lafiya, saboda yawancinsu suna son yin aiki a ƙasashen waje don samun albashi mai kyau da ingantaccen yanayin rayuwa.
A jihohi da dama a Najeriya, ƴan likitocin da ake da su a asibitocin gwamnati, su ne dai za a samu suna da nasu asibitocin masu zaman kansu.
A kwanan baya ne dai aka samu matsala a Akwa Ibom, inda wata mata da jaririnta suka mutu bayan an yi mata tiyatar haihuwa a wani asibitin gwamnati a jihar. Iyayen wadda abin ya shafa sun zargi ma'aikatan asibitin da rashin kula.
Likitoci sun shiga yajin aiki a Najeriya
A wani labarin, mun ruwaito cewa, kungiyar likitoci ta ARD reshen Abuja, ta sanar da shiga yajin aikin sai baba ta gani daga ranar 15 ga Satumba, 2025.
Likitocin sun bayyana cewa, gwamnati ta ki biyan hakkokinsu, ta gaza daukar sababbin likitoci, lamarin da ya jefa asibitoci cikin mawuyacin hali.
Kungiyar ta ce asibitoci 14 na babban birnin kasar na fama da karancin ma’aikata, lamarin da ke tilasta likitoci yin aikin da ya wuce kima, har ya shafi lafiyarsu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


