Sulhu Ya Kankama, Gwamna Ya Kawo Shirin da Za a Tallafawa Tubabbun 'Yan Bindiga

Sulhu Ya Kankama, Gwamna Ya Kawo Shirin da Za a Tallafawa Tubabbun 'Yan Bindiga

  • Gwamna Dikko Radda na jihar Katsina ya fara daukar matakan tallafa wa 'yan bindiga domin ka da su sake komawa ta'addanci
  • Hakan dai na zuwa ne bayan sulhun da ake ci gaba da yi da yan bindigar da suka addabi jama'a a kananan hukumomin jihar Katsina
  • Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Dr. Nasir Mu'azu ya bayyana wasu daga cikin matakan da gwamnatin Katsina ta dauka

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina - Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Radda, ya kirkiro sababbin shirye-shirye da nufin ƙarfafa zaman lafiya da kuma hana tsofaffin ’yan bindiga komawa ruwa.

Hakan na cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu, Salisu Zango, tare da Daraktan Yaɗa Labaran Gwamna, Maiwada Dan-Mallam, suka sanya hannu.

Gwamna Dikko Radda.
Hoton mai girma gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda Hoto: Ibrahim Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Sanarwar ta bayyana cewa gwamnatin Katsina za ta gina sababbin gidaje 152 ga iyalan da rikice-rikice suka raba da muhallansu a karamar hukumar Jibia, in ji rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

'Yan fansho sun fusata, suna shirin fara zanga zanga tsirara a fadin Najeriya

Tubabbun 'yan bindiga za su samu tallafi

Haka kuma gwamnatin ta kawo shirin da za a raba kayan sana'o'i, shanu da tallafin kasuwanci ga ’yan ta’adda da suka tuba domin su dogara da kansu.

Sanarwar ta zo ne bayan wani babban taron sirri na masu ruwa da tsaki a wanda aka gudanar a Katsina.

Taron ya haɗa dattawa, sarakunan gargajiya, shugabannin addini, tsofaffin hafsoshin tsaro da fitattun ’yan jihar domin tattauna nasarori, ƙalubale da dabarun samar da tsaro mai dorewa.

Asalin abin da ya haddasa matsalar tsaro

A yayin taron, Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Dr. Nasiru Muazu, ya gabatar da takarda kan yanayi da halayen yan bindiga da kuma mafitar da ya dace a dauka.

Ya danganta tushen matsalar tsaro da son zuciya, rikicin albarkatun kasa da sauyin yanayi, da kuma tsofaffin ƙorafe-ƙorafen wasu jama'a kan zamantakewa.

Nasir Mu'azu ya bayyana cewa ’yan bindiga sun faɗaɗa kai hare-harensu daga ƙananan hukumomi guda biyar zuwa 25 bayan rushewar shirin afuwa da aka yi a baya, cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Karfin hali: 'Yan bindiga sun gabatar da manyan bukatu 3 kan sulhu a Katsina

Wane matakai gwamnatin Katsina ta dauka?

Ya bayyana matakan gwamnati ƙarƙashin jagorancin Gwamna Radda, ciki har da horas da CWC, da ’yan banga, tare da samar musu da motocin aiki, bindigogi, jiragen sama marasa matuƙi da na’urorin sadarwa.

Haka kuma ya yi bayani kan haɗin gwiwa da sojojin Najeriya, ’yan sanda, DSS da kuma NSCDC, wanda ya ce hakan ya tilasta wa jagororin ’yan ta’adda da dama neman zaman lafiya.

Gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda.
Hoton gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda a wurin taro Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda (PhD)
Source: Twitter

Yayin da yake fayyace abubuwan da aka yi kuskuren fahimta a game da shirin zaman lafiya, kwamishinan ya jaddada cewa yarjejeniyoyin sulhu daga al’umma suke fitowa, inda shugabannin yankuna ke shiga tsakani kai tsaye.

Ya kawo misalin sababbin yarjejeniyoyin da aka cimma a Danmusa, Jibia, Batsari, Kankara, Kurfi da Musawa, inda al’ummomin yankunan suka jagoranci shirin zaman lafiya.

Wani jami'in C-Watch, rundunar da gwamnatin Katsina ta kafa domin yaki da matsalar tsaro ya ce ba ya goyon bayan wannan sulhu da ake yi.

Kara karanta wannan

'Dabarar da aka yi Katsina ta kawo karshen 'yan bindiga da kashi 70,' Gwamnati

Jami'in wanda ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa Legit Hausa cewa ba ya tsammanin mutanen nan za su rike amanar sulhu ko da kuwa an yi.

Ya ce:

"Ka duba abin da ya faru a baya, sau nawa ana sulhu da su tun a gwamnatin da ta shude, amma daga baya su ci gaba da kashe mutane, ni ina ganin a barmu da su.
"Da taimakon Allah sai zaman lafiya ya samu a Katsina, ko an kashe mu, wasu na nan za su fito su kare mana yan uwa da 'ya'yanmu."

Manyan 'yan bindiga sun fara neman afuwa

A wani labarin, kun ji cewa daya daga cikin jagororin yan bindiga da ake nema ruwa a jallo, Adamu Aliero ya nemi afuwar jama'a kan abin da ya aikata a baya.

Ya bayyana hakan ne a wajen zaman sulhu da aka gudanar da wasu gungun ‘yan ta’adda a karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina.

Ya yi kira da a rungumi juna, a yafewa juna, inda ya ce duk wadanda aka yi wa wani abu da suke ganin an munana musu, su yi hakuri a sake gina zaman lafiya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262