Buba Galadima Ya Yi Hasashe Mai Hadari kan Nada Sabon Shugaban Hukumar INEC

Buba Galadima Ya Yi Hasashe Mai Hadari kan Nada Sabon Shugaban Hukumar INEC

  • Buba Galadima ya yi magana kan rade-radin da ake yi dangane da wanda za a nada a matsayin shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC)
  • Jigon na NNPP ya yi zargin cewa gwamnatin tarayya na shirin nada wani tsohon alkalin kotun daukaka kara a matsayin shugaban INEC
  • Ya bayyana matsalolin da za su iya faruwa idan aka dauki ragamar jagorancin INEC, aka ba tsohon alkalin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jigo a jam'iyyar NNPP, Buba Galadima, ya bayyana damuwa kan yadda gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke tafiyar da al’amuran kasa.

Buba Galadima ya nuna damuwarsa ne musamman game da tsarin tafiyar mulki da sahihancin zabe.

Buba Galadima ya yi magana kan gwamnatin Tinubu
Hoton shugaban kasa Bola Tinubu da Buba Galadima Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Buba Galadima
Source: Facebook

Buba Galadima ya bayyana hakan ne yayin wata hira da tashar Arise News a ranar Litinin, 15 ga watan Satumban 2025.

Kara karanta wannan

Buba Galadima: Na kusa da Kwankwaso ya fallasa makarkashiyar Tinubu kan 'yan adawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Buba Galadima ya ce kan shugaban INEC

Jigon na NNPP ya ce akwai jita-jita cewa gwamnati na shirin nada wani tsohon alkalin kotun daukaka kara da ake zargi da mummunar dabi’a a matsayin hukumar INEC.

"Zuwa watan Nuwamba, ana ta jita-jita a ko’ina cewa wannan gwamnati na shirin ba da sunan wani tsohon alkalin kotun daukaka kara da aka san shi da munanan halaye a matsayin shugaban INEC. Ina fatan hakan ba gaskiya ba ne."
“Idan wannan mutumin ya zama shugaban INEC, ku tabbata cewa gwamnati na tsokano yakin basasa a kasar nan."

- Buba Galadima

Buba Galadima ya soki gwamnatin APC

Buba Galadima ya kara da cewa gwamnatin yanzu ba ta girmama tsarin mulki da doka.

“Ba za mu iya ci gaba da zama a kasar da gwamnati ba ta mutunta doka ba."

- Buba Galadima

Ya kuma soki shugabancin INEC na yanzu, yana zargin cewa an karkatar da hukumar domin amfani da ita wajen cimma muradun APC.

Kara karanta wannan

Maganar N Power ta dawo, Abba Hikima, Ɗan Bello za su koma kotu da gwamnatin Tinubu

“A halin yanzu shugaban INEC ya riga ya yi wa APC magudi. Sun kawo wani tsohon sakataren jam'iyyar da yake zuwa kotu a madadin APC, sannan aka saka masa da matsayin shugaban INEC."

- Buba Galadima

Buba Galadima ya ce irin wannan lamari zai lalata tsarin dimokuradiyya a Najeriya.

“Idan aka nada wannan mutumin shugaban INEC, to a manta da batun zabe a Najeriya. Ba za a taba samun zabe a kasar nan ba, sai dai rikici da tashin hankali."

- Buba Galadima

Buba Galadima ya yi magana kan nada shugaban INEC
Hoton jigo a jam'iyyar NNPP, Buba Galadima Hoto: Buba Galadima
Source: Facebook

Buba Galadima ya yi kira ga ’yan Najeriya

Buba Galadima ya bukaci ’yan Najeriya su kasance masu sa ido don kare tsarin dimokuradiyya.

“Ba za mu lamunci a nada mutum mai tarihi na barna da rashin gaskiya a matsayin shugaban INEC ba."

- Buba Galadima

Buba Galadima ya yi zargi kan Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa babban kusa a jam'iyyar NNPP, Buba Galadima, ya yi zarge-zarge kan gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Buba Galadima ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu na shirin ruguza 'yan adawa kafin babban zaben shekara 2027.

Jigon na NNPP, ya yi gargadin cewa idan har gwamnatin Tinubu ba ta sauya salon mulkinta ba, tabbas ba za ta kai labari ba.a zaben shekarar 2027 da ake tunkara.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng