Yajin Aiki: Bayan Likitoci, Kungiyoyin Ma'aikatan Jami'a za Su Ja Zare da Gwamnatin Tinubu
- Kungiyoyin ma’aikatan jami’o’i sun bai wa gwamnati wa’adin kwana bakwai domin ta waiwayi kaulubalen da ke ci masu tuwo a kwarya
- Kungiyoyin SSANU da NASU sun bayyana cewa tun bayan zaman da wani kwamitin hadin gwiwa ya yi a 2024, babu wanda ya ce masu uffan har yanzu
- Kungiyoyin sun yi barazanar daukar mataki na gaba, muddin gwamnati ta ci gaba da yi wa bukatunsu riko mara muhimmanci
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Kungiyar manyan ma’aikata (SSANU) da kuma ta ma’aikatan da ba malamai ba a jami’o’i (NASU) sun bayyana takaicin yadda gwamnati ta yi biris da su.
Kungiyoyin sun bai wa gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki bakwai domin warware matsalolin jin daɗin ma’aikata da ake neman manta wa da su.

Kara karanta wannan
Maganar N Power ta dawo, Abba Hikima, Ɗan Bello za su koma kotu da gwamnatin Tinubu

Source: Facebook
Jaridar Punch ta wallafa cewa kungiyoyin biyu sun yi barazanar cewa matukar aka share su, za su tsunduma yajin aiki a manyan makarantun da ke fadin Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ma'aikatan jami'o'i sun fara shirin yajin aiki
Daily Post ta ruwaito cewa a cikin wata wasika da shugaban SSANU, Muhammed Ibrahim, ya sa wa hannu, kungiyoyin sun ga baiken gwamnati.
Sun ce kwai rashin adalci a yadda aka raba kudin alawus da aka samu, da kuma kin biyan wasu kudin da ma'aikatan ke bi.
Muhammed Ibrahim ya tuna cewa tun cikin wasikar da suka aika wa gwamnati a ranar 18 ga Yuni, 2025, an jawo hankalinta ga wadannan matsaloli.
Ya ce:
“Mun yi magana kan rarraba Naira biliyan 50 cikin rashin adalci; kin biyan albashin watanni biyu da aka dakatar da su; da karin albashi 25/35% da kuma sabunta yarjejeniyar 2009 da gwamnati ta yi da kungiyoyin NASU da SSANU.”
Gwamnati ta fusata kungiyoyin ma'aikatan jami'a
A taron ranar 4 ga Yuli, an yanke shawarar kafa kwamitin hadin gwiwa tsakanin Ma’aikatar Ilimi, Hukumar Kula da Jami’o’i (NUC), da JAC.
An kafa kwamitin domin duba yadda aka raba N50bn, inda aka gano yadda aka tauye hakkin ma'aikatan jami'o'i baki daya.

Source: Getty Images
Sai dai kungiyoyin sun ce, duk da alkawarin gwamnati na gyara lamarin da kuma magance batun karin albashi, har yanzu babu wani abu da aka yi.
Kungiyoyin sun ce:
“Tun bayan zaman farko da muka yi a ranar 10 ga Disamba, 2024 da Kwamitin sabunta yarjejeniyar da Alhaji Yayale Ahmed ke jagoranta, komai ya tsaya, amma gwamnatin tarayya ta kammala tattaunawa da ASUU har suna dab da rattaba hannu, yayin da aka watsar da mu.”
Sun ce idan gwamnati ta gaza daukar mataki daga ranar Litinin, 15 ga Satumba, 2025, za su fara kokarin tafiya yajin aiki.
Likitoci sun shiga yajin aiki
A baya, kun samu labarin cewa Kungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa reshen Abuja ta ayyana shiga yajin aikin sai baba ta gani daga safiyar yau Litinin, 15 ga Satumba, 2025.

Kara karanta wannan
Asiri ya tonu: Gwamnati ta bankado ma'aikatan bogi a Bauchi, za su fuskanci hukunci
Kungiyar ARD-FCTA ta bayyana cewa ta dauki matakin fara yajin aikin ne sakamakon rashin daukar mataki daga bangaren gwamnati kan bukatun da suka gabatar a baya.
A wata sanarwa da sakataren kungiyar, Agbor Affiong, ya fitar, ya ce sun yanke wannan shawarar ne bayan taron gaggawa da ta gudanar a ranar Lahadi, 14 ga Satumba, 2025.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
