Jadda Garko: Yadda Aka Shirya Makircin Hana Kusa a APC Samun Mukami a Gwamnatin Tinubu
- Kusa a jam'iyyar APC a jihar, Jadda Garko, ya yi zargin cewa an shirya masa makarkashiya don ka da ya samu mukami a gwamnatin tarayya
- Jadda Garko ya yi zargin cewa a ofishin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, aka shirya masa zagon kasan da ya hana shi samun mukami
- Ya musanta jita-jitar cewa zai fice daga jam’iyyar APC, yana mai cewa biyayyarsa ga Shugaba Bola Tinubu da manufofinsa ba ta canja ba har yau
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Wani kusa a jam'iyyar APC a Kano, Jadda Garko, ya bayyana yadda aka hana shi samun mukami a gwamnatin Bola Tinubu.
Jadda Garko wanda mawaki ne ya zargi ofishin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, da yi masa zagon kasa.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta ce Jadda Garko ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manema labarai a Kano ranar Litinin, 15 ga watan Satumban 2025.

Kara karanta wannan
Buba Galadima: Na kusa da Kwankwaso ya fallasa makarkashiyar Tinubu kan 'yan adawa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane zargi kusan na APC ya yi?
Ya yi zargin cewa an yi masa zagon kasa ta hanyar sanar da Shugaba Bola Tinubu cewa ya mutu domin hana shi samun mukami a gwamnatin tarayya.
Hakazalika ya musanta rade-radin cewa zai sauya sheka daga APC, inda ya jaddada cewa har yanzu yana tare da Tinubu da manufofinsa.
Neman gyara titin Kaduna–Abuja ta jawo matsala
Jadda Garko ya ce kalubalen siyasa da yake fuskanta ya fara ne bayan ya nemi a gyara hanyar Kaduna–Abuja.
Ya ce an yi biris da bukatarsa sai daga baya lokacin da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya fito ya yi kira iri daya da nasa.
"Na shawarci Ministan ayyuka, David Umahi, da a gyara hanyar Kaduna–Abuja, amma aka yi banza da ni. Bayan watanni tara, Kwankwaso ya ce a yi haka kuma gwamnati ta amsa masa."
'Idan da an dauki mataki tun da farko, da an ceci rayuka kuma da yanzu aikin ya kusa kammaluwa ."
- Jadda Garko
Abin da aka gayawa Tinubu kan Jadda Garko
Jadda Garko ya ce an gabatar da sunansa domin samun mukami, amma aka danne shi a ofishin shugaban ma’aikata bayan an danganta shi da Hon. James Abiodun Faleke.
"Sun fadawa shugaban kasa cewa na mutu kuma an birne ni. Amma lokaci zai yi da za mu hadu da shugaban kasa a bainar jama’a, gaskiya za ta bayyana."
- Jadda Garko
Bai yi nadamar tallata Tinubu ba
Duk da zargin zagon kasan da aka yi masa, Jadda Garko ya ce bai yi nadama ba kan goyon bayansa ga Tinubu.

Source: Facebook
“Mun tallata Asiwaju da zuciya daya. Babu nadama. Ko da ba a ba ni mukami ba, zan ci gaba da aiki da duk abin da zan iya."
- Jadda Garko
Ya kuma yi gargadin cewa akwai wata matsala da ke kunno kai a Arewacin Najeriya wacce ’yan adawa za su iya amfani da ita a zabe idan ba a gaggauta magance ta ba.
Fadar shugaban kasa ta yi wa Atiku martani
A wani labarin kuma, kun j cewa fadar shugaban kasa ta ki hakura kan zargin da Atiku Abubakar ya yi na cewa ta kasa magance yunwa da talauci.
Ta bayyana cewa kalaman tsohon mataimakin shugaban kasan, sun nuna cewa bai san halin da ake ciki a kasa ba.
Hakazalika, ta bayyyana cewa ta gamsu da irin ci gaba da Shugaba Bola Tinubu ya kawo, a shekaru biyun da ya kwashe yana mulki.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

