Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Ya Yi Hatsari, An Ji Halin da Yake Ciki

Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Ya Yi Hatsari, An Ji Halin da Yake Ciki

  • Hatsarin mota ya rutsa da ayarin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Jigawa, Rt. Hon. Haruna Aliyu Dangyatin a hanyarsa ta zuwa Maigatari
  • Rahoto ya nuna cewa motar yan sanda da ke rakiyar kakakin Majalisar ce ta yi hatsari, lamarin da ya jikkata jami'an da ke ciki
  • Hadimin Kakakin Majalisar ya tabbatar da aukuwar lamarin, amma ya ce babu wanda ya rasa ransa, kuma an sallami masu rauni daga asibiti

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jigawa - Rahotanni sun nuna cewa hatsarin mota ya rutsa da ayarin motocin kakakin Majalisar Dokokin Jihar Jigawa, Rt. Hon. Haruna Aliyu Dangyatin.

An tattaro cewa Kakakin Majalisar ya tsallake rijiya da baya a hatsarin wanda ya rutsa da motar ayarinsa a lokacin da yake hanyar zuwa garin Maigatari da ke cikin Jigawa.

Kara karanta wannan

Wutar lantarki ta samu matsala, mutane za su shiga duhu a jihohi 4 a Najeriya

Shugaban Majalisar Dokokin Jigawa.
Hoton Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Jigawa, Rt. Hon Haruna Aliyu Dangyatin Hoto: Haruna Aliyu Dangyatin
Source: Facebook

Rahotan The Nation ya nuna cewa Shugaban Majalisar na kan hanyarsa ne domin halartar wani taron siyasa da Gwamnatin Jihar Jigawa ta saba shiryawa na jin ta bakin jama'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda hatsari ya rutsa da Kakakin Majalisa

An yi wa taron taken “gwamnati da jama'a” kuma wakilan gwamnati na zuwa domin tattaunawa da jama'ar jigawa kan harkokin mulki.

Bayanai sun nuna cewa Hon. Haruna Dangyatin na hanyar zuwa wannan taro da aka shirya yi a garin Maigatari ne lokacin da hatsarin ya faru.

Shaidun gani da iso sun bayyana cewa daya daga cikin motocin da ke rakiyar Kakakin, Toyota Hilux ta ‘yan sanda, ce ta sauka daga titi, ta fara tunguragutsi a gefen hanya.

Wani da ya shaida abin ya ce:

“Sauran motocin, ciki har da wadda Kakakin Majalisae yake ciki, sun yi nasarar kaucewa motar yan sandan, sannan suka tsaya a gaban wurin da abin ya auku.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi bayan ɗan sa kai ya buɗe wuta a masallaci, an samu raunuka

'Yan sanda sun samu raunuka a hatsarin

Majiyar da ta sanar da lamarin ta bayyana cewa ‘yan sandan da ke cikin motar sun samu raunuka kala daban-daban, wasu daga ciki duk ba su cikin hayyacinsu.

A cewartsa, tuni aka garzaya da su zuwa Asibitin Gwamnati na Gumel, inda aka ce sun isa a sume, amma daga bisani likitoci suka farfaɗo da su, in ji rahoton Daily Post.

Jihar Jigawa.
Hoton tawirar jihar Jigawa Hoto: Legit.ng
Source: Original

Mai taimaka wa kakakin Majalisar Dokokin Jigawa na kai da kai, Aqeel Akilu, ya tabbatar da aukuwar hatsarin, amma ya ce babu wanda ya rasa ransa.

A cewarsa:

“Babu wanda ya rasa rai a hatsarin, dukkan jami'an ‘yan sandan da hatsarin ya rutsa da su su na cikin koshin lafiya yanzu, kuma an sallame su daga asibiti.”

Hatsari ya rutsa ayarin Mataimakin Kakakin Majalisa

A wani labarin, kun ji cewa ayarin mataimakin kakakin Majalisar Dokokin jihar Abia, Austin.Okezie Meregini ya gamu da hatsari a hanyar dawowa daga Fatakwal.

Kara karanta wannan

Tsohon soja zai bada wuri, Simi Fubara zai koma kujerar gwamnan Rivers

Rahotanni sun nuna cewa hatsarin ya faru ne a kan titin Enugu zuwa, Umuahia zuwa Fatakwal, a yankin Obehia, kuma wasu daga cikin hadiman mataimakin kakakin suka jikkata sosai.

Mutum biyu yan gida daya sun rasu a hatsarin kuma an ce dukansu ba Najeriya su ke zaune ba, sun dawo ne domin birne mahaifiyarsa, bisa tsautsayi suka gamu da ajali.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262