Sa'o'i da Sulhu, 'Yan Bindiga Sun Rufe Masallaci, Sun Sace Masu Sallah 40 da Asuba

Sa'o'i da Sulhu, 'Yan Bindiga Sun Rufe Masallaci, Sun Sace Masu Sallah 40 da Asuba

  • Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindiga sun kai hari a wani masallaci da ke kauyen Gidan Turbe, karamar hukumar Tsafe
  • Lamarin ya auku ne da safe yayin da jama’a ke cikin sallar Asuba, inda maharan suka kewaye masallacin suka yi awon gaba da mutane
  • Hakan na zuwa ne sa'o'i kaɗan bayan tattaunawar zaman lafiya da aka ce an kulla a karamar hukumar Faskari a jihar Katsina

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Tsafe, Zamfara – Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun sake kai hari a jihar Zamfara duk da cewa an ce an samu yarjejeniyar zaman lafiya a wasu sassan Arewa maso Yamma.

Rahotanni sun tabbatar da cewa maharan sun sace kusan mutane 40 daga wani masallaci da ke cikin kauyen Gidan Turbe na karamar hukumar Tsafe.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun farmaki bayin Allah suna ibada, an rasa rayukan mutane 22 a Nijar

Taswirar jihar Zamfara da ke Arewa maso Yamma
Taswirar jihar Zamfara da ke Arewa maso Yamma. Hoto: Legit Hausa
Source: Original

Zagazola Makama ya wallafa a X cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Litinin, a lokacin da jama’a ke tsaka da gudanar da sallar Asuba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa maharan sun kewaye masallacin kafin daga bisani su yi awon gaba da mutane.

Yadda aka kai hari masallaci da Asuba

Shaidu sun bayyana cewa maharan sun zo da bindigogi suka rufe kofa da tagogin masallacin, suka tilasta wa masu ibada bin su.

Wani mazaunin kauyen ya ce an dauki mutanen zuwa cikin dazukan da ke kusa da yankin Gohori a Tsafe.

Rahotanni sun ce ba a samu jinkiri wajen aiwatar da harin ba, inda aka dauki jama’ar da ke tsaka da ibada kai tsaye zuwa cikin daji.

Tasirin harin kan shirin zaman lafiya

Rahotanni sun nuna cewa duk da tattaunawa da wasu kungiyoyin a Katsina, wasu daga cikin su na ci gaba da kai hare-hare a Zamfara, Kebbi, Sokoto da Kaduna.

Kara karanta wannan

Mutane sun mutu da wani karamin jirgin sama ya gamu da hatsari, an samu bayanai

Daily Trust ta rahoto cewa wani mazaunin yankin ya bayyana cewa babu tsarin jagoranci daya tilo a tsakanin kungiyoyin ‘yan bindiga.

Ya ce:

“Za ka iya tattaunawa da wasu a Katsina, amma a lokaci guda wasu daga cikinsu na ci gaba da kai hare-hare a sauran jihohi.”
Dan bindiga Ado Aliero da aka yi zaman sulhu da shi a Katsina
Dan bindiga Ado Aliero da aka yi zaman sulhu da shi a Katsina. Hoto: Zagazola Makama
Source: Facebook

Halin da ake ciki bayan kai harin

Bisa ga rahotannin da aka samu, ba a samu wani karin bayani daga hukumomin tsaro a Zamfara ba a kan harin.

Hakan ya bar al’umma cikin fargaba, inda ake ci gaba da addu’o’i da kokarin ganin an ceto mutanen da aka sace.

Rahotanni sun ce iyalan wadanda aka sace sun shiga cikin tashin hankali, yayin da ake kira ga gwamnati da hukumomin tsaro su dauki matakan gaggawa don kubutar da su.

Babaro ya halarci zaman sulhu

A wani rahoton, kun ji cewa kasurgumin dan ta'adda a jihar Katsina, Kachalla Babaro ha halarci zaman sulhu a jihar Katsina.

Rahotanni sun nuna cewa dan ta'addan na cikin wadanda suka shahara da kai hare hare kan al'umma a jihar.

Kara karanta wannan

An nuna fuskar Kachalla Babaro da ya kai hari masallaci, ya kashe Musulmai

A watan Agustan 2025 ne aka kai hari wani masallaci a karamar hukumar Malumfashi kuma aka ce shi ya jagoranci harin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng