'Ba Abin da za a Fasa,' Dangote Ya Fadi Shirin Matatarsa kan Raba Man Fetur
- Matatar Dangote ta karyata ikirarin da kungiyoyin mai irinsu DAPPMAN da NUPENG ke yi na cewa mansa ya fi arha a Togo
- Matatar ta ce dukkanin wasu korafe-korafe da kungiyoyin ke yi a kanta ba su da tushe, illa tsoron asarar riba da su ke ji
- Sanarwar da matatar ta fitar ta bayyana cewa fitar da mai zuwa sassan Najeriya yana nan daram babu fashi
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Matatar Dangote ta bayyana korafin da wasu ƙungiyoyin masana’antar mai ke yi akanta ba zai hana ta aiwatar da manufar da ta kudiri aniya ba na fitar da mai sassan Najeriya.
A wata sanarwa da matatar ta fitar, ta bayyana cewa irin wannan mataki da koke daga ƙungiyoyin kamar NUPENG da DAPPMAN ba su da madogara.

Source: Getty Images
The Nation ta wallafa cewa matatar ta ce sam wadannan korafe-korafe ba su da alaƙa da batun ‘yancin kafa ƙungiya kamar yadda suke ikirari.
Matatar Dangote ta kafe a kan bakarta
Sanarwar da matatar Dangote ta fitar ta ce tana sane da yunkurin da kungiyoyin ke yi da sunan 'yanta ma'aikata, amma a kashin gaskiya matatar su ka sa a gaba.
Sanarwar ta ce:
“Abin da waɗannan ƙungiyoyi ke yi ba taimakon ma'aikata ba ne, sai dai wata dabarar dakushe ci gaban da matatar Dangote ke samarwa. Wannan wani yunƙuri ne na ɓata ci gaban da jama'a ke samu da kuma fargabar asarar da za su iya yi sakamakon haka."
Matatar ta kuma yi watsi da bayanin da DAPPMAN ta fitar a jaridu a ƙarshen mako, inda ta ce an shirya bayanan ne domin karkatar da hankalin jama'a daga gaskiya.
Matatar Dangote ta yi martani ga DAPPMAN
Matatar ta ambato rahoton NNPC na Janairu 2022, inda aka ce ɗaya daga cikin 'yan kungiyar DAPPMAN ne ya kawo man fetur mai guba da ke ɗauke da fiye da 15% na methanol.
Sanarwar ta kara da cewa wannan sinadari ya yi barna, wanda ya haifar da lalacewar injin motoci dubban mutane.

Source: Getty Images
Matatar ta ce:
“Amma har yanzu babu wani bincike mai zaman kansa ko kuma na gwamnati da aka gudanar don gano ainihin yadda lamarin ya faru da kuma sakamakon sa."
Matatar ta kuma bayyana cewa ikirarin da ke cewa farashin man fetur a Togo ya fi sauƙi ba gaskiya ba ne.
Ta ce a birnin Lomé, farashin lita ɗaya na fetur yana kusan 680 CFA (N1,826), wanda ya haura farashin Najeriya.
Ta ƙara da cewa duk da cewa tana shigo da fiye da 60% na danyen mai da take tace wa daga waje, har yanzu tana iya sayar da man fetur a ƙasa da farashin duniya a yammacin Afrika.
Kiristoci na yi wa Dangote addu'a
A baya, kun ji cewa Kungiyar Young Christian Fellowships in Nigeria Without Borders (YCFNB) ta sanar da cewa za ta gudanar da addu’o’i da azumi na tsawon kwanaki 14.
Ta ce ta dauki aniyar fara azumi da addu'o'in daga ranar 15 ga watan Satumba zuwa 29 watan Satumba, 2025 domin roka wa matatar Dangote kariya daga makiyanta.
A cikin sanarwar da aka fitar a ranar Lahadi, kungiyar ta ce barazanar yajin aikin da NUPENG ke yi babban mataki ne da zai jawo matsaloli ga tabbatar da wadatar mai a kasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


