2027: Ana Rade Radin Komawarsa PDP, Peter Obi Ya Yi Ganawar Sirri da Obasanjo

2027: Ana Rade Radin Komawarsa PDP, Peter Obi Ya Yi Ganawar Sirri da Obasanjo

  • Jagoran jam'iyyar LP, Peter Obi ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su rungumi zaman lafiya ba tare da la’akari da addini ko kabila ba
  • Obi ya bayyana hakan ne yayin da ya ziyarci tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo da kuma sabon Sarkin Ibadan, Rashidi Ladoja
  • Bayan ganawarsa da Obasanjo da Ladoja, dan takarar shugaban kasar a 2023, ya fadi matsayarsa kan burin sake gina Najeriya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Oyo - Tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su rungumi haɗin kai da zaman lafiya, inda ya ce babu wata ƙasa da za su iya kira tasu sai Najeriya.

Peter Obi ya bayyana haka ne yayin da ya ziyarci tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, da kuma sabon Olubadan na Ibadan, Oba Rashidi Ladoja, a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Lauya ya faɗi illar da IMF da Bankin Duniya suka yi wa Najeriya a mulkin Tinubu

Peter Obi ya gana da Olusegun Obasanjo, sun tattauna kan halin da kasa take ciki.
Peter Obi tare da tawagarsa sun kai wa Olusegun Obasanjo ziyara. Hoto: @PeterObi
Source: Twitter

Peter Obi ya ziyarci Obasanjo da sabon sarki

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Peter Obi ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“A yau, ni tare da Dakta Yunusa Tanko, Gbadebo Rhodes-Vivour, da Segun Adebanjo, mun ziyarci Shugaba Obasanjo. Bayan haka, mun ziyarci sabon Olubadan na Ibadan, Kabiyesi Oba Rasheed Adewolu Ladoja.”

Ya ƙara da cewa, a duka ziyarorin biyu, sun tattauna kan yanayin ƙasar da kuma yadda za a samar da haɗin kai, soyayya, adalci, da ci gaban jama'a.

"Wadannan ziyararori sun sa na sake yarda cewa za a iya samar da hadakar tawagar mutane masu karfi, masu kishi da burin son sake gina Najeriya."

- Peter Obi.

Dalilin ziyarar Peter Obi ga sabon sarki

Da yake jawabi ga manema labarai a Ibadan bayan ziyarar da ya kai wa Oba Ladoja a gidansa da ke Bodija, Peter Obi, ya bayyana cewa Ibadan tana da matuƙar muhimmanci ga ci gaban Najeriya.

Kara karanta wannan

'Abin da Goodluck Jonathan da Peter suka tattauna yayin ganawarsu'

Ya bayyana cewa ya kai ziyarar ne don girmama sabon Olubadan, saboda Ibadan tana da muhimmiyar rawa a fannin siyasa, zamantakewa, da tattalin arzikin ƙasar.

Peter Obi ya shaidawa manema labarai cewa yana da kwarin gwiwa cewa Oba Ladoja zai yi amfani da gogewarsa a matsayin tsohon sanata, gwamna, kuma hamshaƙin ɗan kasuwa, wajen jagorantar Ibadan zuwa matsayi mai girma.

Peter Obi ya ziyarci sabon Olubadan na Ibadan, Oba Rashidi Ladoja a Oyo.
Peter Obi tare da sabon Olubadan na Ibadan, Oba Rashidi Ladoja a Oyo. Hoto: @PeterObi
Source: Twitter

"Ba mu da kasa sai Najeriya' - Peter Obi

Jaridar The Nation, ta rahoto tsohon dan takarar shugaban kasar, ya ci gaba da fadawa manema labarai cewa:

"Da farko, na zo ne don nuna girmamawata ga masarauta, ga sabon Olubadan, kafin a rantsar da shi a hukumance. taya shi murnar zama Olubadan na Ibadanland na 44 ne."
“Shin ba za mu iya haɗa kai da kuma ƙaunar juna don gina ƙasa mai kyau ba? Lallai fa ba mu da wata ƙasa da za mu kira tamu sai wannan. Dole ne mu haɗa kai don gina ta, don amfanin kowa da kowa.”

- Peter Obi.

Peter Obi ya gana da Olusegun Obasanjo

Kara karanta wannan

Shirin kifar da Tinubu: Peter Obi ya gana da Goodluck Jonathan a Abuja

A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan da Peter Obi sun yi ganawar sirri a birnin tarayya Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa Peter Obi ya tabbatar da cewa tattaunawar ta mayar da hankali kan halin da ƙasar ke ciki da yadda za a kawo gyara.

Ganawar ta jawo ce-ce-ku-ce kan yiwuwar sabon haɗin gwiwar siyasa kafin 2027 domin kifar da Bola Ahmed Tinubu, yayin da ake zargin Obi zai shiga PDP.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com