Mauludi: Masu Takutaha Sun Kona Masallacin Izala da Gidan Liman a Kano
- Sheikh Dr Sani Sharif Bichi ya yi magana bayan wasu da ake zargi 'yan Darika ne sun kona musu masallaci a jihar Kano
- Ya nemi hukumomin tsaro da su ɗauki mataki kan wadanda suka kona masallacin da kai hari gidan limami a Rimin Gado
- Shehin ya ce da maharan sun gano limami a Rimin Gado a lokacin harin, da sun kashe shi, amma ya buya a wani daki
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Shugaban Izala a Kano, Sheikh Dr Sani Sharif Bichi, ya yi kira ga al’ummar Ahlus Sunnah da su kasance masu hakuri tare da gujewa ɗaukar doka a hannunsu.
Ya yi magana ne bayan wasu da ake zargi 'yan Takutaha sun kai hari suka ƙona masallaci da gidan limami a Rimin Gado.

Source: Facebook
A wani bidiyo da shafin Darul Madinah Online TV ya wallafa a Facebook, Sheikh Bichi ya bukaci hukuma ta dauki mataki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malamin ya bayyana cewa abin da ya faru ya tarar da hankali, domin maharan sun shiga gidan limami, suka ɗauki babur ɗinsa, suka ƙona ta tare da fatattakar iyalansa.
Maganar Izala bayan kona masallaci
Shugaban Izala ya yi kira ga hukumomin tsaro musamman 'yan sanda da DSS da su tabbatar da adalci tare da ɗaukar mataki mai tsauri kan waɗanda suka kai musu hari.
Ya ce dole ne hukumomi su tabbatar da bin doka da oda domin kauce wa sake aukuwar irin wannan rikici da ya shafi addini.
Sheikh Bichi ya yi addu’ar Allah ya tsare al’umma, ya kiyaye addini tare da tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai a Kano da Najeriya baki ɗaya.
Gargadi ga masu tayar da husuma
Sheikh Bichi ya yi nuni da cewa babu wata fa’ida a kai hari ga masallaci ko gidajen malamai saboda sabani na addini ko fahimta.
Ya ce ya kamata ’yan Darika da ake zargi da kai harin da su kare abin da suka fahimta ta hanyar hujja da karantarwa, ba wai ta hanyar tashin hankali da kai hari ga wasu ba.
A cewarsa, irin wannan dabi’a ba ta dace da koyarwar addini ba, kuma tana iya rura wutar rikici tsakanin al'umma.

Source: Facebook
Za a gina masallaci da aka kona
Malamin ya bayyana cewa duk da barnar da aka yi musu, Izala za ta sake gina babban masallaci wanda ya fi wanda aka kona girma da kyau.
Shugaban Izala ya jaddada cewa manufar su ita ce yada sunnah da tsarkake ibada daga bidi’a, kuma hakan za su ci gaba da yi cikin lumana da zaman lafiya.
Shafin Jibwis Gombe ya wallafa a Facebook cewa Sheikh Bichi ya yi kira ga mabiya Izala su zauna lafiya duk da abin da ya faru.
An kama 'yan daba masu kai hari
A wani rahoton, kun ji cewa an kama wasu 'yan daba da ake zargi suna shirin kai mummunan harin a jihar Kano.
Rahotanni sun bayyana cewa an kama wasu matasa ne da suka yi shigar mata domin kada a gane su yayin harin.

Kara karanta wannan
'Duk da fara shirin sulhu, 'Yan bindiga sun yi kisa, an sace mutane masu yawa a Katsina
Bayan kama matasan, an bayyana cewa za a cigaba bincikensu kuma da zarar an kammala za a dauki mataki a kansu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

