Rikicin NUPENG da Dangote: Kungiyar Kiristoci Ta Fara Azumin Kwanaki 14

Rikicin NUPENG da Dangote: Kungiyar Kiristoci Ta Fara Azumin Kwanaki 14

  • Kungiyar Kiristoci YCFNB za ta fara addu’o'i da azumi na kwana 14 don kare matatar Dangote daga 'sharrin wasu'
  • Wannan na zuwa bayan kungiyar masu dakon man fetur ta dawo da hannun agogo baya a kan yarjejeniya da matatar Dangote
  • Sai dai NUPENG ta ce kamfanin Dangote ne ya fara karya yarjejeniyar da DSS da wasu jami'an gwamnati su ka samar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Kungiyar Young Christian Fellowships in Nigeria Without Borders (YCFNB) ta bayyana cewa za ta fara azumi da addu'o'in kwanaki 14.

Ta bayyana cewa za ta fara na addu’o'i da azumi daga ranar 15 zuwa 29 ga Satumba, 2025 domin kare matatar man fetur ta Dangote daga abokan gaba da ke kokarin tarwatsa cigaban da ake samu.

Kara karanta wannan

Lita za ta koma N820: Motocin Dangote 1,000 za su fara raba fetur kyauta

Kiristoci za su yi wa Dangote addu'a
Hoton Alhaji Aliko Dangote, da gidan man NNPCL Hoto: Dangote Industries/NNPC Limited
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa a cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a ranar Lahadi, ta zargi kungiyar kwadago ta NUPENG da daukar matakin da za su iya jefa Najeriya cikin wahala.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dangote: Kiristoci sun caccaki NUPENG

The Cable ta ruwaito cewa YCFNB ta bayyana cewa barazanar yajin aikin da NUPENG ke yi makirci ne da ke neman bata sunan Aliko Dangote.

Kungiyar ta bayyana Alhaji Aliko Dangote a matsayain 'mai kishin kasa da ke fama da hare-haren makiyan ci gaba' saboda ya ki amincewa da muradun wasu manyan ’yan kasuwa.

Kungiyar ta YCFNB ta bukaci dukkannin Kiristoci a fadin Najeriya da su hada kai wajen gudanar da addu’o’i domin neman kariyar Allah ga matatar Dangote.

YCFNB ta zargi NUPENG da uzzura wa talaka
Hoton Shugaban rukunin kamfanin Dangote Hoto: Getty
Source: Getty Images

A cewar sanarwar:

“Gwagwarmayar Dangote na kare martabar kasa da jajircewarsa wajen tabbatar da ci gaba sun jawo masa suka, amma ya nuna da’a da jajircewa a kan abin da ya tsaya a kai.”

Kara karanta wannan

Murna ta koma ciki? Gwamnatin tarayya ta karyata shirin daukar sababbin ma'aikata

Kiristoci sun ja kunnen kungiyq4 NUPENG

Kungiyar ta kuma ja kunnen NUPENG kan tafiya yajin aiki, inda ta ce “talakawa za su fusata” bisa wannan yunkuri na haifar da karancin mai da zai kai ga hauhawar farashin kayayyaki.

A farkon wannan wata, NUPENG ta zargi matatar da karya yarjejeniyar da DSS da wasu jami’an gwamnati suka tsara, wadda ta amince ma’aikata su shiga ƙungiyoyi.

Dangote ya musanta zargin, yana mai cewa bai hana ma’aikata shiga ƙungiyoyi ba, kuma matatar ba ta da wata manufa ta danniya ko handame harkar mai da iskar gas.

DSS ta shiga tsakanin NUPENG da Dangote

A baya, mun ruwaito cewa DSS ta shiga tsakani domin kawo karshen sabanin da ya kunno kai tsakanin kamfanin Dangote da Ƙungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Iskar Gas (NUPENG).

Bayan tattaunawa mai zurfi, an cimma matsaya inda NUPENG ta dakatar da yajin aikin da ta fara a fadin Najeriya saboda matar Dangote ta amince da wasu daga cikin bukatunsyu.

Kara karanta wannan

NDLEA ta kama wiwi mai nauyin kilo 112 a wajen hadarin mota a Kano

Rikicin ya taso ne kan zargin cewa kamfanin Dangote yana hana ’yancin ma’aikata shiga kungiyoyi, musamman kungiyar NUPENG da kuma kokarin safarar mai zuwa sassan kasar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng