Isiya: Hatsabibin Ɗan Bindiga da Ake Nema Ya Miƙa Wuya ga Zaman Lafiya a Katsina

Isiya: Hatsabibin Ɗan Bindiga da Ake Nema Ya Miƙa Wuya ga Zaman Lafiya a Katsina

  • Isiya Kwashen Garwa, ɗaya daga cikin hatsabiban jagororin 'yan bindiga da ake nema ruwa a jallo, ya rungumi sulhu a jihar Katsina
  • Wannan matakin na Isiya ya haifar da shakku a tsakanin mazauna yankin Faskari, saboda sanin tarihinsa na aikata ta'addanci
  • Malamin addinin Musulunci, Dr. Ahmad Gumi, ya fito ya yi martani kan mika wuyan Isiya Garwa, tare da fadin fargabar da yake yi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Katsina - Wani shahararren jagoran 'yan bindiga, Isiya Kwashen Garwa, wanda hedikwatar tsaro ta kasar ta ayyana a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo, ya amince da wata yarjejeniyar sulhu a jihar Katsina.

Sunan Isiya Garwa yana cikin jerin sunaye 19 na manyan 'yan ta'adda da ake nema ruwa a jallo a kasar nan, cewar rahoton Legit Hausa na ranar 26 ga Nuwambar 2022.

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: Malamin da ya fi 'tsufa' yana wa'azi ya bar duniya yana shekaru 95

Hatsabibin dan bindiga, Isiya Garwa ya mika wuya a Katsina Sheikh Gumi ya yi sharhi.
Hoton hatsabibin dan bindiga, Isiya Garwa da ya rungumi sulhu a Katsina, da Dr. Ahmad Gumi. Hoto: Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Source: Facebook

'Dan bindiga ya rungumi sulhu a Katsina

Zagazola Makama, kwararren mai sharhi kan lamuran tsaro ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, a ranar Lahadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa Isiya Garwa ya gabatar da kansa a yankin Hayin Gada da ke karamar hukumar Faskari, inda ya ce ya shirya ya yi tattaunawar sulhu da shi.

Masani kan harkokin tsaron ya bayyana cewa Isiya Garwa, ya kasance dan asalin kauyen Kamfanin Daudawa ne a Faskari.

Ya ce an dade ana danganta shi da kashe-kashe, garkuwa da mutane, da kuma kai hare-hare a garuruwan jihar Katsina da ma jihohin makwabta.

A baya, kwararrun masana tsaro sun ce Isiya Garwa na cikin rukunin manyan 'yan bindiga da ke addabar Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, ta hanyar kai hare-hare.

Martani kan yarjejeniyar sulhu da Isiya

Rahoto ya nuna cewa shugabannin yankin da masu ruwa da tsaki a fannin tsaro na la'akari da yiwuwar amincewa da sharuddan sulhunsa.

Kara karanta wannan

Ribas: Peter Obi ya zargi gwamnatin Najeriya da yi wa dimokuradiyya kisan mummuke

Sai dai, mutane da dama na shakku game da manufar Isiya ta yin sulhu, la'akari da tarihin da ya ke da shi na zubar da jini da garkuwa da mutane.

Yayin da wasu mazauna yankin ke ganin wannan sulhu wata dama ce ta dawo da zaman lafiya a cikin garuruwansu, wasu kuma suna ganin akwai makarkashiya a manufar dan bindigar.

Hatsabibin dan bindiga, Isiya Garwa ya rungumi sulhu a Katsina.
Hoton hatsabibin jagoran 'yan bindiga, Isiya Garwa, a taron sulhu da ya gudanar a Faskari, jihar Katsina. Hoto: @ZagazOlaMakama
Source: Twitter

Ahmad Gumi ya yi sharhi a kan lamarin

A halin da ake ciki, shahararren malamin addinin Musulunci, Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, ya yi tsokaci a kan yarjejeniyar sulhun da Isiya Garwa ya yi.

A wani gajeren sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Dr. Ahmad Gumi ya lura da cewa zaman lafiya yana dawowa Katsina, cikin yardar Allah.

Amma, ya nuna damuwa cewa wasu mutane da ba sa son zaman lafiya, za su sake harzuka 'yan bindigar ta hanyar kai musu hari.

"Yana da matukar muhimmanci a ilmantar da su ('yan bindigar) cewa ana amfani da su ta hanyar cin gajiyar jahilcinsu da kuma yunƙurinsu na ɗaukar fansa."

- Dr. Ahmad Gumi.

'Za mu ga alfanun sulhu' - Kabir Daudawa

Kara karanta wannan

Jagoran 'yan bindiga ya fara cika alkawari kan yarjejeniyar sulhu a Katsina

A zantawarmu da wani matashi a garin Daudawa, Kabir, ya ce duk da garin Daudawa bai fuskanci hari daga 'yan bindiga ba, amma sulhun zai zamo alkairi a gare su.

Kabir ya ce:

"Muma nan za mu ga amfanin wannan sasancin, saboda wannan shekarar, mun samu matsala a bangaren noma.
"Yan bindiga sun sanya noma ya gagaremu, gonakin da ke kusa da mu ne kawai muke iya nomawa, su dinma, a baya bayan nan, sojoji sun zo sun sare duk gonakin masara, dawa da dai masu tsayin zangarniya.
"Wannan sulhun zai sa mu samu damar fadada nomanmu, duk da yanzu damina ta riga ta ja, amma za mu iya jaraba noman rani, a garuruwan makota."

Kabir ya ce yana fatan 'yan bindigar za su rike alkawarin da suka dauka, sannan su ma jami'an tsaro da gwamnati su yi abin da ya dace.

Ado Aliero ya rungumi sulhu a Katsina

A wani labarin, mun ruwaito cewa, jagoran 'yan ta'adda, Ado Aliero ya ba da tabbacin dawowar zaman a Katsina da sauran jihohin Arewa maso Yamma.

A wani taron sulhu da kungiyoyin 'yan ta'adda da shugabanni da mutanen garuruwan Faskari, jihar Katsina suka gudanar, Aliero ya ce zai rungumi zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Dan majalisar Filato da ake nema ruwa a jallo ya mika kansa, ICPC ta tsare shi

Wannan na zuwa ne bayan kananan hukumomi da dama a Katsina sun yi zaman sulhu da 'yan ta'addar da ke addabarsu domin samun zaman lafiya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com