'Ana Rasa Rayuka,' Asibitin Aminu Kano Ya Roki KEDCO kan Yanke Wutar Lantarki

'Ana Rasa Rayuka,' Asibitin Aminu Kano Ya Roki KEDCO kan Yanke Wutar Lantarki

  • Hukumar asibitin koyar wa na Malam Aminu Kano ya mika rokon ceton rayuka ga kamfanin wutar lantarki a jihar, KEDCO
  • Asibitin ya bayyana cewa jama'a sun fara rasa rayukansu sakamakon rashin wutar da za a kula da marasa lafiya yadda ya dace
  • Jami'ar hulda da jama'a ta asibitin, Hauwa Iniwa Dutse ta tabbatar da cewa suna sane da basussukan da ake binsu, amma a duba lamarin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano (AKTH), ya roƙi kamfanin raba wutar lantarki na Kano, wato KEDCO, da ya dawo da wutar lantarkin da ya yanke.

Hukumar gudanarwar asibitin ta ce akwai bukatar a dawo da wutar a cikin gaggawa bayan da wasu marasa lafiya da ke dogara da na’urorin taimakon numfashi suka rasa rayukansu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta dauki harama, nan ba da jimawa ba za a daina dauke wuta a Najeriya

An samu matsala wutar lantarki a AKTH
Taswirar jihar Kano Hoto: Legit.ng
Source: Original

Daily Trust ta wallafa cewa wannan roƙon ya fito ne a cikin wata sanarwa da Hauwa Inuwa Dutse, shugabar sashen yada labarai na asibitin, ta fitar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

AKTH ya roki KEDCO a jihar Kano

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa asibitin ya bayyana damuwarsa matuƙa dangane da yadda AKTH ya raba asibitin da hasken wutar lantarki.

Sanarwar ta kara da bayyana cewa za a iya kauce wa asarar rayukan da aka yi da a ce akwai wutar lantarki a asibitin.

AKTH ya bayyana cewa yana biyan kudin wutar lantarki da ake amfani da sh daga cikin kuɗin da asibitin ke samu ta kudin da ake shigo masa.

Sanarwar ta kara da cewa sannan ana da kashe makudan kuɗi wajen siyan danyen man dizal domin ɗora injinan janareto domin cike gibi idan KEDCO ta katse wuta.

AKTH ta ce za ta biya basussukan da KEDCO ke binta
Hoton gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Sanarwar ta kara da cewa:

“Hukumar AKTH na roƙon KEDCO da ya tallafa wajen samar da ingantaccen kulawa ga lafiya ta hanyar dawo da wutar lantarki ga asibitin, yayin da muke ci gaba da ɗaukar matakai domin biyan basussukan da ke kanmu.”

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: Gwamnati ta bankado ma'aikatan bogi a Bauchi, za su fuskanci hukunci

Asibitin AKTH ya ba KEDCO tabbacin biyan bashi

AKTH ya tabbatar da cewa suna ƙoƙarin biyan duk wani bashi da ake binsa domin a ci gaba da samar da kula wa ga marasa lafiya.

Haka kuma asibitin ya bayyana cewa yanke wutar lantarki daga irin wannan muhimmin asibiti yana da mummunar illa ga lafiyar marasa lafiya da danginsu.

Asibitin ya kuma bayyana cewa yana buƙatar haɗin kai da goyon baya daga kamfanonin da ke da alaka da harkar lafiya domin tabbatar da tsare lafiyar al’umma.

A cewar hukumar AKTH, jinkirin dawo da wutar lantarki na iya ci gaba da jefa lafiyar mutane cikin haɗari.

KEDCO ya yanke wutar jami'ar Kano

A wani labarin, mun wallafa cewa Kamfanin rarraba wutar lantarki na Kano, KEDCO, ya dauki matakin yanke wutar lantarki a jami’ar kimiyya da fasaha ta Aliko Dangote a Wudil a jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa akwai bashin kusan Naira miliyan 60 a kan jami'ar na kudin wutar lantarki da KEDCO ke bin ta, amma Naira miliyan 20 kawai ta iya biya.

Kara karanta wannan

NDLEA ta kama wiwi mai nauyin kilo 112 a wajen hadarin mota a Kano

Farfesa Abdulkadir Dambazau, shugaban sashen kula da harkokin dalibai na jami’ar, ya ce wannan yanke wuta ya jefa jami’ar cikin matsala ganin yadda jami’ar ke dogaro da wutar KEDCO.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng