Lita Za Ta Koma N820: Motocin Dangote 1,000 Za Su Fara Raba Fetur Kyauta
- Matatar man Dangote ta fitar da fiye da manyan motoci 1,000 na CNG yau Litinin domin fara rarraba man fetur kai tsaye ga dillalai
- Ana ce farashin man zai ragu zuwa N820 a matatar, inda za a sayar da litar fetur din tsakanin N841 da N851 a wasu jihohi
- Kungiyar IPMAN ta ce ta shirya karɓar motocin Dangote a tashoshinta, kuma rage farashin zai kawo sauki ga rayuwar 'yan Najeriya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Matatar man Dangote za ta fitar da motoci fiye da 1,000 masu amfani da iskar gas ɗin CNG yau Litinin, a matakin farko na shirin rarraba fetur kai tsaye.
A saboda haka, kungiyar dillalan man fetur ta IPMAN ta ce ta shirya karɓar motocin Dangote a tashoshinta daban-daban da ke a fadin kasar.

Kara karanta wannan
'Lafiyar jama'a na cikin hadari,' Likitoci sun shiga yajin aikin sai baba ta gani

Source: Twitter
Jami’an matatar man Dangote sun shaida wa jaridar The Punch cewa rarraba man kai tsaye zai fara ne a matsayin wani ɓangare na bikin cika shekara guda da fara samar da fetur a matatar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Motocin CNG na Dangote sun iso Najeriya
A da an tsara fara shirin a ranar 15 ga watan Agusta 2025, amma aka samu jinkiri saboda matsalolin sufuri a kasar Sin.
Dangote ya ba da sautun sayo motocin CNG guda 4,000 daga kasar Sin domin kai su Legas don gudanar da rarraba fetur dinsa kyauta ga dillalai.
Sai dai shirin bai tabbata ba saboda rashin isassun jiragen ruwa da za su yi dakon motocin daga kasar Sin zuwa Najeriya.
Wani babban jami’in kamfanin Dangote ya bayyana cewa fiye da motoci 1,000 aka fara kawo wa a cikin watan Agusta, sannan aka rika shigo da daruruwa kowane mako.
Dangote zai rage farashin litar fetur
Da wadannan motocin da ake da su yanzu, kamfanin ya ce zai kaddamar da shirin rarraba mai kyauta daga yau Litinin domin rage farashin man a duk fadin Najeriya.

Kara karanta wannan
Rikici da Dangote: NUPENG ta dauki sabon mataki da zai jawo karancin fetur a Najeriya
Tun daga yau, wannan shiri zai sa farashin litar fetur a matatar ya sauka zuwa N820, wanda hakan zai haifar da saukin farashin fetur a gidajen mai a jihohi da dama.
A Legas da sauran jihohin Kudu maso Yamma, za a rika sayar da litar fetur a kan N841, yayin da lita za ta koma N851 a Abuja, Rivers, Delta, Edo da Kwara.
A cikin wata sanarwa, kamfanin Dangote ya ce:
“Matakin farko na rarrabawa zai shafi babban birnin tarayya, Lagos, Kwara, Delta, Edo, Rivers da jihohin Kudu maso Yamma, sannan za a fadada shi a sauran jihohi yayin da aka samu karin motoci.”

Source: Twitter
IPMAN ta shirya karbar fetur din Dangote
A halin da ake ciki, mambobin kungiyar dillalan man fetur ta IPMAN sun bayyana cewa sun shirya karɓar motocin Dangote a tashoshin su, inji rahoton Daily Trust.
Shugaban IPMAN na kasa, Abubakar Shettima, ya tabbatar da cewa, 'yan kungiyar sun riga sun yi rajista domin shiga sahun wadanda za a raba wa man a gidajen mansu.
“Muna a shirye, muna jiran motocin Dangote su zo. Da yawa daga cikin mambobinmu sun yi rajista don su samu man kai tsaye. Muna sa ran motocin za su iso gobe (Litinin), da yardar Allah."
- Abubakar Shettima.
A kan rage farashin man, shugaban IPMAN ya ce hakan zai faranta ran talakawa, kuma shi ne abinda kungiyar ke fatan ganin an samu a kowane lokaci.
NUPENG ta na shirin ba Dangote matsala
Tun da fari, mun ruwaito cewa, sabuwar matsala ta kunno kai tsakanin matatar Dangote da kungiyar NUPENG bayan DSS ta shiga tsakaninsu.
Kungiyar NUPENG ta yi zargin cewa, bayan sulhu da Dangote, wani jami'in matatar, Alhaji Sayaya Dantata ya hana direbobin MRS lika tambarin kungiyarta.
Yayin da kungiyar ta ce Alhaji Dantata ya yi wa mambobinta barazana, ta kuma sha alwashin tsunduma yajin aiki idan ba a taka masa burki ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
