'Lafiyar Jama'a na cikin Hadari,' Likitoci Sun Shiga Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani

'Lafiyar Jama'a na cikin Hadari,' Likitoci Sun Shiga Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani

  • Kungiyar likitoci masu neman kwarewar aiki reshen Abuja (ARD-FCTA), ta fara yajin aikin sai baba ta gani daga Litinin, 15 ga Satumba 2025
  • ARD-FCTA ta ce gwamnati ta ki biyan hakkokinsu, ta gaza daukar sababbin likitoci, lamarin da ya jefa asibitoci cikin mawuyacin hali
  • Kungiyar ta ce asibitoci 14 na babban birnin kasar na fama da karancin ma’aikata inda likita daya ke duba marasa lafiya sama da 30 a rana

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kungiyar likitoci masu neman kwarewar aiki reshen Abuja (ARD-FCTA), ta ayyana yajin aikin sai baba ta gani daga yau Litinin, 15 ga Satumba 2025.

Wannan ya biyo bayan yajin aikin gargadi na mako guda da suka gudanar a makon da ya gabata domin matsa wa gwamnati ta biya bukatunsu.

Kara karanta wannan

Lita za ta koma N820: Motocin Dangote 1,000 za su fara raba fetur kyauta

Likitoci sun tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a Abuja
Hoton likita ta duka cikin damuwa, da Shugaba Bola Tinubu a wajen wani taro. Hoto: Getty Images, @officialABAT/X
Source: Getty Images

Likitoci sun shiga yajin aiki a Abuja

A sanarwar da sakataren kungiyar, Agbor Affiong, ya fitar, ARD-FCTA ta ce hakan ya zama dole ne saboda gwamnati ta ki daukar wani mataki duk da gargadin da aka yi, cewar rahoton Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar Agbor Affiong ta ce:

"Kungiyar likitocin ARD-FCT, a taron gaggawa da ta gudanar ranar 14 ga Satumba, 2025, ta yanke shawarar shiga yajin aikin sai baba ta gani daga karfe 8:00 na safiyar Litinin, 15 ga Satumba, 2025.
"Wannan matakin ya biyo bayan gazawar hukumomi wajen biyan bukatunmu, duk da yajin aikin gargadi na mako guda da muka gudanar."

A cikin sanarwar, likitocin sun sha alwashin ci gaba da aikin "har sai gwamnati da shugabanni sun nuna cikakkiyar damuwa ga jin dadin likitoci da kiwon lafiyar mazauna Abuja."

Rashin ma’aikata da halin da likitoci ke ciki

Punch ta rahoto shugaban kungiyar, George Ebong, ya bayyana cewa akwai asibitoci 14 a Abuja, amma karancin likitoci da kwararru ya jefa harkokin kiwon lafiya cikin mawuyacin hali.

Kara karanta wannan

'Za a sheƙa ruwa na kwana 5,' An faɗi jihohin Arewa 10 da za su gamu da ambaliya

Ya ce:

“Muna bukatar akalla likitoci 200, amma ba mu da ko rabin wannan adadi. Likita daya na duba marasa lafiya sama da 30 ko 40 a rana. Wani likita kan yi tiyatar haihuwa har sau 10 a rana.”

Ya kara da cewa sakamakon nauyin da ke kansu, wasu daga cikin likitocin sun fara dogaro da magungunan rage damuwa da rage hawan jini domin saukaka matsin lambar da suke ciki.

Kungiyar likitocin ta ce akwai likitan da ya na yin tiyatar haihuwa sau 10 a rana, saboda rashin likitoci.
Likitoci na gudanar da tiyata kan mara lafiya a asibiti. Hoto: Getty Images
Source: UGC

Likitoci sun yi kira ga gwamnati

Kungiyar ta ce kiwon lafiyar jama’ar Abuja na cikin hadari idan gwamnati ta ci gaba da yin rikon sakainar kashi ga bukatunsu.

Likitocin sun jaddada cewa wannan yajin aikin ba zai tsaya ba sai an dauki matakai na zahiri wajen magance matsalolin da suka hada da rashin daukar sababbin ma’aikata, rashin biyan hakkoki da inganta yanayin aikinsu.

Likitoci sun shiga yajin aiki a Ondo

A wani labarin, mun ruwaito cewa, likitocin Ondo sun shiga yajin aikin gargadi na kwanaki uku saboda rikon sakainar kashi da gwamnati ta yi wa fannin lafiya.

Kara karanta wannan

A karshe, Likitoci sun shiga yajin aiki, sun rufe asibitocin gwamnati baki daya

Karkashin kungiyar NAGGDDPP, likitocin sun koka kan ƙarancin ma'aikata, gazawar gwamnati a biyan biyan albashi, alawus, da kuɗin karin matsayi.

Sai dai gwamnatin Ondo ta ce ta fara biyan kuɗaɗen da ake bin su, kuma a shirye take ta ɗauki ƙarin likitoci idan akwai masu son aikin a asibitocin jihar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com