Hasashen Yanayi na Litinin: Za a Samu Ambaliyar Ruwa a Taraba da Jihohin Arewa 2
- Hukumar NiMet ta yi gargaɗin yiwuwar ambaliya a jihohin Adamawa, Taraba da Gombe a ranar Litinin ,15 ga Satumba, 2025
- Ambaliyar za ta afku ne yayin da NiMet ta ce ruwan sama mai yawa, hade da tsawa zai sauka a Abuja da jihohi 14 na Arewa
- An shawarci jama’a da su zauna cikin shirin ambaliyar, direbobi kuma su yi taka-tsantsan don gujaye wa hadurran ababen hawa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar da ke kula da hasashen yanayi ta Najeriya (NiMet), ta fitar da hasashen yanayi na ranar Litinin, 15 ga watan Satumba.
NiMet ya yi hasashen cewa za a samu ruwan sama tare da tsawa a Abuja da jihohi 14 na Arewa da kuma wasu jihohi daga Kudancin kasar.

Source: UGC
A cikin hasashen da ta fitar a shafinta na X a daren ranar Lahadi, NiMet ta gargadi mazauna yankunan da za a samu ambaliyar ruwa da su yi taka tsantsan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Arewa: Hasashen ruwan sama da safe
A cewar rahoton NiMet, za a iya samun ruwan sama mai karfi a sassan jihohin Kaduna, Gombe, Bauchi, Kebbi, Adamawa, da Taraba da safiyar Litinin.
Hakazalika, za a samu haduwar hadari sosai, amma rana na iya fitowa a Abuja da sauran jihohin Arewa ta Tsakiya a safiyar yau.
Duk da hakan, ana sa ran cewa za a samu ruwan sama mai matsakaicin karfi a sassan Abuja da jihohin Neja, Kogi, Kwara, da Benue.
Arewa: Hasashen ruwa sama da yamma
A yammacin ranar Litinin din, hukumar NiMet ta ce za a iya samun tsawa tare da ruwan sama mai matsakaicin karfi a sassan Borno, Jigawa, Kano, Kaduna, Adamawa, Gombe, Bauchi, da kuma Katsina.
A Arewa ta Tsakiya kuwa, ana sa ran za a samu tsawa tare da ruwan sama mai matsakaicin karfi a mafi yawan sassan yankin a yammacin ranar.
Hasashen ruwan sama a jihohin Kudu
A Kudancin Najeriya, hukumar ta ce za a samu yanayi na hadari tare da ruwan sama mai matsakaicin karfi a sassan jihohin Ekiti, Ondo, Rivers, Akwa Ibom, da Cross River.
Da yammaci har zuwa dare, hukumar ta yi hasashen cewa za a samu ruwan sama mai matsakaicin karfi a mafi yawan sassan yankin.

Source: Getty Images
Gargadin NiMet ga 'yan Najeriya
NiMet ta yi gargadi cewa akwai yiwuwar ambaliya a jihohin Adamawa, Taraba da Gombe, sakamakon ruwan sama mai yawa da ake sa ran zai sauka.
Hukumar ta shawarci jama’a musamman mazauna bakin koguna da wuraren da ruwa kan taru su kasance cikin shiri don guje wa haɗarin ambaliyar.
Haka kuma, an gargadi direbobi da su yi tuki a hankali saboda titi zai yi santsi, sannan za a samu ragin gani sakamakon ruwa da iska mai karfi.
NiMet ta kara da cewa mutane su guji fakewa a karkashin bishiyoyi don gudun karyewar rassa, sannan a rika bibiyarta don samun hasashen yanayi a kai a kai.
Ambaliya za ta shafi jihohi 11
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta gargadi jihohi 10 na Arewacin Najeriya, cewa za su fuskanci ambaliya daga Lahadi zuwa Alhamis.
Cibiyar kula da ambaliyar ruwa ta kasa, da ke karkashin ma'aikatar muhalli ta tarayya ce ta fitar da gargadin, tana mai cewa, ambaliyar za ta iya yin barna mai yawa.
Jihohin da ambaliyar ruwan za ta shafa sun hada da Adamawa (Ganye, Natubi), Benue (Abinsi, Agyo, Gogo, Ito, Makurdi, Udoma, Ukpiam), Nasarawa (Agima, Rukubi, Odogbo Taraba: Beli, Serti, Donga), da sauransu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


