Hankula Sun Tashi bayan Ɗan Sa Kai Ya Buɗe Wuta a Masallaci, an Samu Raunuka

Hankula Sun Tashi bayan Ɗan Sa Kai Ya Buɗe Wuta a Masallaci, an Samu Raunuka

  • Al’umma sun ga abin al'ajabi bayan wani dan sa-kai ya budewa mutane wuta a cikin masallaci a jihar Kebbi
  • Lamarin ya tayar da hankukan al'ummar yankin Faransi a karamar hukumar Danko Wasagu da ke jihar
  • Rahotanni sun ce an garzaya da matashin da aka ji wa rauni mai suna Bawa Kiri asibitin Ribah a Zuru domin kulawar likitoci

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kebbi - Ana cikin fama da matsalar hare-haren yan bindiga, wani dan sa-kai ya bude wuta a cikin masallaci wanda ya yi sanadin samun raunuka.

Mazauna kauyen Faransi da ke karamar hukumar Danko Wasagu a Jihar Kebbi sun shiga firgici bayan matashin ya yi harbi.

Dan sa-kai ya bude wuta a masallaci a Kebbi
Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi. Hoto: Nasir Idris Kauran Gwandu.
Source: Facebook

Rahoton Zagazola Makama ne ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Lahadi 14 ga watan Satumbar 2025 a shafin X.

Kara karanta wannan

Tsohon soja zai bada wuri, Simi Fubara zai koma kujerar gwamnan Rivers

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ake fama da matsalar tsaro a Kebbi

Jihar Kebbi na daga cikin jihohin da ke fama da matsalar tsaro wanda ya tilasta samar da yan sa-kai domin taimakawa sojoji.

Gwamnatin jihar na kokarin samar da wasu hanyoyi domin ganin an kawo karshen hare-haren yan bindiga gaba daya a jihar.

Gwamna Nasir Idris ya sanar da gagarumin shirin da ya yi na murkushe 'yan ta'adda da wanzar da zaman lafiya a jihar Kebbi.

Mai girma gwamnan ya bayyana cewa zai kafa sansanin sojoji a karamar hukumar Augie domin karfafa tsaro da kare rayukar al'ummar da yake mulki a jihar.

Ya kuma ce za a yi cikakken gyara ga asibitin gwamnati na garin Augie domin inganta lafiyar al’umma daga matakin farko.

Ana cikin firgici bayan dan sa-kai ya bude wuta a masallaci
Taswirar jihar Kebbi da ke Arewa maso Yamma a Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Yadda aka samu raunuka a masallaci a Kebbi

Majiyar ta tattaro cewa lamarin ya bar wani matashi, Bawa Kiri, da rauni sakamakon harbin bindiga da aka yi masa a masallaci.

Kara karanta wannan

Malami ya debo ruwan dafa kansa, 'yan Majalisa sun nemi jami'an tsaro su kama shi

Mahaifin wanda aka ji wa rauni, Kiri Nyako, ya kai rahoton ga sojojin Rundunar Brigada ta 1 a Unashi domin daukar mataki.

Daga nan sojoji suka fara kokarin gano da kuma kama wanda ake zargi ɗan sa-kai da ya aikata wannan mummunan harin a masallaci.

Wane hali matashin yake ciki a yanzu?

A halin yanzu an kai wanda aka jikkata Asibitin Gwamnatin Ribah a karamar hukumar Zuru inda yake karɓar kulawa daga wajen likitoci.

Bayanan wannan lamari har yanzu babu wasu bayanai domin binciken hukumomi na ci gaba da gudana a kan abin da ya faru.

Yan bindiga sun afka wa masallata a Katsina

Kun ji cewa duk da kokarin zaman sulhu da wasu yankuna ke yi a jihar Katsina, yan bindiga na ci gaba da kai hare-hare a jihar wanda ke shan fama da matsalolin tsaro.

Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa yan bindiga sun kai hari kan wasu Musulmai da ke sallar Isha a jihar da ke yankin Arewacin Najeriya.

An tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a garin Matazu da ke Katsina, inda aka kashe wasu tare da jikkata wasu wanda ya sake sanya shakku kan maganar sulhu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.