Duk da Hare Haren Yan Bindiga, an Sake Zama da Yan Ta’adda domin Sulhu a Katsina
- A jihar Katsina ana ci gaba da sulhu da ’yan bindiga yayin da ake fama da hare-hare, matakin da wasu yankuna ke maraba da shi
- Rahotanni sun tabbatar cewa sulhu ya gudana yau Lahadi a ƙaramar hukumar Faskari, domin kare rayuka da dukiyoyi daga farmakin ’yan bindiga
- Majiyoyi sun bayyana fatan cewa tattaunawar za ta kawo ƙarshen zubar da jinin al'umma da ba su da laifi tare da samar da zaman lafiya a Katsina
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Katsina - Ana ci gaba da sulhu da yan bindiga a jihar Katsina yayin da ake ci gaba da hare-hare a jihar da ke fama da matsalar tsaro.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa wasu yankuna sun nuna jin dadi bayan zaman sulhu da suka da yan bindiga wanda aka ce har kare yan gari suke yi daga wasu baki.

Kara karanta wannan
An bankado abubuwa, matar shedanin 'dan bindiga ta shiga hannu a Zamfara, ta tsure

Source: Facebook
Rahoton Bakatsina, shafin da ke kawo bayanai game da tsaro shi ya tabbatar da haka a yau Lahadi 14 ga watan Satumbar 2025.
Katsina: Yankunan da suka yi zama da yan bindiga
Wannan na zuwa ne yayin da jihar Katsina ta yi kaurin suna wurin tattaunawa da yan bindiga duk da korafe-korafe daga wasu wurare.
A baya bayanan, an samu kananan hukumomi da dama da suka shiga sulhu da yan bindiga domin kare garuruwansu daga hare-hare.
Kafin karamar hukumar Faskari, akalla kananan hukumomi hudu ne suka yi zama da yan bindiga yayin da suke fama da matsalolin ta'addanci.
Kananan hukumomin sun hada da Batsari da Danmusa da Safana da kuma karamar hukumar Jibia.
Yankuna da dama sun nuna gamsuwa game da sulhun inda wasu ke cewa suna ganin alfanun haka ba tare da matsala ba.

Source: Original
An yi sulhu da yan bindiga a Katsina
Majiyoyi suka ce a yau Lahadi an yi zaman sulhu a karamar hukumar Faskari da ke jihar Katsina a Arewa maso Yamma a Najeriya.

Kara karanta wannan
Katsina: Yan bindiga sun afka wa masallata, sun sace musulmai a sallar isha, an rasa rai
An yi hakan musamman domin samun zaman lafiya da yan bindiga da ke kai hare-hare wanda ke jawo asarar rayuka da dukiyoyi.
Sanarwar ta ce:
"Ƙaramar Hukumar Faskari a Jihar Katsina na gudanar da tattaunawar zaman lafiya da ’yan bindiga yau Lahadi.
"Allah ya sa hakan ya kawo ƙarshen zubar da jinin wandanda ba su ji ba, ba su gani ba da ake yi a jihar."
Yan bindiga sun farmaki masallaci a Katsina
Mun ba ku labarin cewa duk da kokarin zaman sulhu da wasu yankuna ke yi a jihar Katsina, yan bindiga na ci gaba da kai hare-hare a jihar wanda ke shan fama da matsalolin tsaro.
Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa yan bindiga sun kai hari kan wasu Musulmai da ke sallar Isha a jihar da ke yankin Arewacin Najeriya da ya ke jaw asarar rayuka da dukiyoyi.
An tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a garin Matazu da ke jihar Katsina, inda aka kashe wasu tare da jikkata wasu wanda ya sake sanya shakku kan maganar sulhu da ake yi.
Asali: Legit.ng