Wata Sabuwa: Gwamna Ya Ayyana Dokar Ta Baci a Jiharsa, Zai Dauka Ma'aikata 2,000

Wata Sabuwa: Gwamna Ya Ayyana Dokar Ta Baci a Jiharsa, Zai Dauka Ma'aikata 2,000

  • Gwamnatin Akwa Ibom ta ayyana dokar ta-baci a fannin lafiya domin sauya tsarin kiwon lafiya zuwa na shirin ARISE na Gwamna Umo Eno
  • Za a dauki ma’aikatan lafiya 2,000 tare da gyara asibitoci, daukar tsofaffin likitoci da kuma sabunta makarantu na koyon kiwon lafiya
  • Gwamnati ta amince da karin kasafin kudi na N695bn, wanda ya kai kasafin zuwa N1.65trn domin albashi, ayyuka, da magance ambaliyar ruwa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Uyo - Gwamnatin jihar Akwa Ibom ta ayyana dokar ta-baci a fannin kiwon lafiya bayan kammala nazari kan taswirar ci gaban lafiya a jihar.

Kamar yadda gwamnati ta bayyana, matakin zai hanzarta sauya tsarin kiwon lafiya da kuma samar da ingantattun ayyukan lafiya da suka dace da ARISE Agenda na Gwamna Umo Eno.

Kara karanta wannan

Duniya ta sauya: An nada 'AI' a matsayin minista domin dakile cin hanci

Gwamnan Akwa Ibom ya ayyana dokar ta baci kan fannin kiwon lafiya
Hoton gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno. Hoto: @_PastorUmoEno
Source: Twitter

Gwamna Eno ya ayyana dokar ta baci

Kwamishinan labarai, Elder Aniekan Umanah, ya bayyana hakan wa manema labarai bayan taron majalisar zartarwa (Exco) da aka yi a fadar gwamnati, a Uyo, inji rahoton Channes TV.

"Gwamna Umo Eno ya amince da ayyana dokar ta baci a fannin kiwon lafiya, don daukar ma'aikata, sabunta makarantar kiwon lafiya, da aiwatar da shirin lafiya na ARISE."

- Elder Aniekan Umanah.

Taron ya samu halartar mataimakiyar gwamna, Sanata Akon Eyakenyi, sakataren gwamnati, shugaban ma’aikata, manyan jami’ai da kwamishinoni na jihar.

Elder Umanah ya ce karkashin wannan tsarin na ARISE, za a inganta cibiyoyin lafiya a fadin jihar tare da bude shafin daukar sababbin ma’aikatan lafiya.

Za a dauki ma’aikatan lafiya 2,000

Sanarwar kwamishinan yada labaran ta kara da cewa:

“Za mu dauki ma’aikatan lafiya 2,000, kuma an cire sharadin lambar katin zabe daga cikin bukatun da masu neman aikin ke gabatarwa.”

Kara karanta wannan

Birtaniya ta dage takunkumin tafiye tafiye da ta kakaba wa jihar Kaduna

Kwamishinan ya kuma bayyana cewa majalisar zartarwar jihar, karkashin jagorancin Gwamna Umo Eno, ta amince a sabunta makarantu na koyar da kiwon lafiya.

Hakazalika, ta amince a kara yawan daliban lafiya, da kuma daukar tsofaffin likitoci da suka yi ritaya amma suke son ci gaba da aiki kan kwangila.

Domin tabbatar da aiwatar da shirin, gwamnatin ta kafa kwamitin gudanarwa mai kunshe da mambobi daga ma’aikatun gwamnati daban-daban da hukumomin da abin ya shafa.

Gwamnatin Akwa Ibom za ta dauki ma'aikatan lafiya 2,000 don inganta kiwon lafiya.
Taswirar jihar Akwa Ibom, mai babban birni, Uyo. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Gwamna ya kara kasafin kudi zuwa ₦1.65trn

Bugu da kari, Premium Times ta rahoto majalisar ta amince da karin kasafin kudi na ₦695bn, wanda ya daukaka girman kasafin kudin 2025 zuwa ₦1.65trn.

Daga cikin karin kasafin, an ware ₦125.6bn don kudin gudanarwa yayin da aka ware ₦569.3bn don manyan ayyuka.

Kwamishinan ya ce wannan karin kudi zai rufe bukatu da dama ciki har da aiwatar da sabon albashin ma’aikata, biyan hakkokin masu NYSC a jihar da wajen jihar, magance ambaliya da zaizayar kasa, da kuma kammala ayyukan da hauhawar farashi ya shafa.

Gwamna Namadi ya ayyana dokar ta baci

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: Gwamnati ta bankado ma'aikatan bogi a Bauchi, za su fuskanci hukunci

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamna Umar Namadi ya ayyana dokar ta baci a jihar Jigawa bayan karanta rahoton bincike kan ilimi.

Gwamna Umar Namadi ya bayyana cewa hankalinsa ya tashi sosai da ya ga rahoton cewa 'yan aji daya a firamare ba sa iya karatu da rubutu.

A matsayin matakin gagawa, Gwamna Namadi ya ce ya raba ma'aikatar ilimi zuwa gida biyu, kuma ya dauki wasu matakai don inganta ilimi a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com