Shekarun da Karamin Ma'aikaci Zai Dauka Yana Asusu kafin Ya Iya Sayen iPhone 17

Shekarun da Karamin Ma'aikaci Zai Dauka Yana Asusu kafin Ya Iya Sayen iPhone 17

Kaduna - Wani bincike da Legit Hausa ta gudanar ya nuna cewa, zai ɗauki ma'aikaci mai karɓar mafi ƙarancin albashi na N70,000 fiye da shekaru biyu kafin ya iya mallakar sabuwar wayar iPhone 17.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Binciken ya nuna cewa ko da ma'aikacin ya ajiye dukkan albashinsa, ba zai mallaki wayar ba sai bayan wani lokaci mai tsawo, wanda hakan ke nuni da tsananin hauhawar farashi da kuma ƙarancin albashi a faɗin Najeriya.

Karami ma'aikaci a Najeriya zai shafe watanni akalla 26 yana asusu kafin ya iya sayen wayar iPhone 17
Sabuwar wayar iPhone 17 da Apple ya fitar, da matashi rike da waya cikin damuwa. Hoto: Liubomyr Vorona
Source: Getty Images

Farashin wayar iPhone 17 a Najeriya

A cewar rahoton Apple Premium Store, farashin sabuwar wayar iPhone 17 mai nau'in 256GB zai fara ne daga NGN1,869,660 a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai, ana iya samun ƙaruwar farashin fiye da wannan hasashen idan darajar Naira ta ci gaba da faɗuwa idan aka kwatanta da Dala.

Kara karanta wannan

'Dan Majalisa, Adamu Aliyu ya aikata laifi mai girma, kotu ta ayyana nemansa ruwa a jallo

Idan karamin ma'aikaci, yana son sayen iPhone 17 daga shafin Apple Premium, kenan, zai ajiye kudinsa ba tare da ya kashe sisin kwabo ba, na tsawon watanni 26.

Farashin dukkanin nau'ikan iPhone 17

Farashin wayoyin iPhone 17 ya dogara ne da nau'insu da kuma girman ƙwaƙwalwarsu. Ga jerin farashin yadda aka fitar da su a duniya, tare da canjin kudin daga Dala zuwa Naira:

  • iPhone 17: Farashinta na farko zai fara ne daga $799, wanda ya yi daidai da N1.2m a farashin canjin yau.
  • iPhone 17 Air: Wannan nau'in zai zo ne da farashi biyu, inda na farko zai fara daga $899, wanda ke daidaita da N1.5 miliyan. Nau'in na biyu kuma zai fara daga $949, wanda ya kai N1.43 miliyan.
  • iPhone 17 Pro: Wannan nau'in ana sa ran farashinsa zai fara ne daga $1,099, wanda ya kai kimanin N1.6 miliyan.
  • iPhone 17 Pro Max: Ana sa ran wannan nau'in zai zama mafi tsada, inda farashinsa zai fara daga $1,199, wanda ya yi daidai da N1.8 miliyan.

Lissafin ajiyar kuɗin sayen iPhone 17

Idan aka yi lissafi, idan mutum yana son mallakar wayar iPhone 17 mai mafi ƙarancin farashi, kuma ya ajiye dukkanin albashinsa (N70,000), zai buƙaci kusan watanni 19 ko 26, kafin ya tattara kuɗin wayar.

Kara karanta wannan

NDLEA ta kama wiwi mai nauyin kilo 112 a wajen hadarin mota a Kano

Amma, a zahiri ba zai yiwu a ajiye duk albashi ba saboda bukatun rayuwa na yau da kullum.

Idan mutum ya raba albashinsa gida biyu, wato ya ajiye rabin albashinsa (N35,000), zai ɗauki kusan watanni 38 ko 52, kafin ya tattara kuɗin wayar.

Ana amfani da watanni kala biyu ne, saboda farashin da ake sayar da iPhone 17 normal, ya kai NGN1,869,660 a Apple Premium Store, amma farashin da aka sake ta a duniya, shi ne $799, kwatankwacin N1.2m a Naira.

iPhone 17: Abubuwan lura ga karamin ma'aikaci

Akwai wasu abubuwa da ma’aikaci zai yi la’akari da su kafin fara tara kudin sayen iPhone 17:

  • Haraji da cire kudade: Idan ma'aikacin yana aiki da gwamnati, akwai haraji, cirewar kuɗin fensho, da sauran kuɗaɗen da za su iya rage albashinsa. Wannan zai ƙara tsawaita lokacin da zai ɗauka yana tara kudin sayen iPhone 17.
  • Canjin farashin: Farashin wayar na iya ƙaruwa a kowane lokaci saboda canjin farashin dala idan aka kwatanta da naira.
  • Bukatun rayuwa: Bukatun rayuwa na iya tilasta taba kudin da aka fara ajiye wa, kamar rashin lafiya, biyan kudin haya, da sauransu.

Kara karanta wannan

Waye Larry Ellison? Makusancin shugaban kasa da ya fi kowa kudi yau a duniya

Karshen bincike kan tara kudin sayen iPhone 17

Bisa dukkanin waɗannan bayanai, kodayake lissafin ya nuna cewa mutum zai iya mallakar iPhone 17 ta hanyar ajiye kuɗi, amma a zahiri, yana da wahala a ajiye kuɗin duka.

Don haka, binciken ya nuna cewa dole ne a kasance da ƙarin hanyoyin samun kuɗi, ko kuma a rage kashe kuɗi, idan har ana so a mallaki irin wannan wayar mai tsada.

Kamfanin iPhone ya kaddamar da sabuwar wayar iPhone 17, kuma farashinta ya haura N1m a Najeriya.
Wata ma'aikaciyar Apple, na daga sabuwar wayar iPhone 17 da aka kaddamar da ita a Amurka. Hoto: picture alliance / Contributor
Source: Getty Images

Ra'ayoyin wasu 'yan Arewa

Legit Hausa ta tattauna da wasu 'yan Arewa, wadanda wasusun ma'aikata ne kan ko za su iya tara kudin sayen sabuwar iPhone 17.

Amina Lawal, da ke sana'ar dinki, ta ce:

"Ko da wasa, ba zan ma gwada ba. Duk so na da waya, ba zan iya cire Naira miliyan 1.8 na sayi iPhone 17 ba. To balle a ce wai har in rika tara N70,000 a wata, gwanda na ci a ciki na gaskiya."

Imram Yunusa, daga Funtua, ya ce:

"Duk da albashi na ya haura N70,000, amma gaskiya ba zan iya yin asusun sayen iPhone 17 ba, wannan ba irin wayarmu ba ce, ta masu samu sama da N500,000 ce a wata."

Kara karanta wannan

Tashin farashin mai a duniya ya shafi Najeriya bayan harin Isra'ila a Qatar

Amma, Nafisa Kabir, da ke jihar Bauchi, ta ce:

"Sosai ma, zan iya. Ai wallahi, ko da bashi ne sai na hada kudin nan. Ni fa ka san, ba na so ana yin abu ana bari na a baya, da a ba ni labari, gwanda ni na bayar, yawwa. Don haka, tsaf zan tara kudin. Kai ni tuni na fara taru, zan bayar da tawa, iPhone 15, in yi ciko, me ya fi raina?."

Hanyoyi 3 na samun kudi a WhatsApp

A wani labarin, mun ruwaito cewa, kamfanin Meta ya kirkiro hanyoyin uku da masu amfani da manhajar sadarwa ta WhatsApp za su rika samun kudi.

A wata sanarwa da kamfanin ya fitar, ya ce sabon tsarin zai ba masu kirkirar bidiyon nishaɗi, ƴan kasuwa da masu talla dama masu wallafa fasahohi.

Kamfanin Meta ya bayyana cewa wannan tsari ba zai shafi sakonnin sirri da mutane ke aikawa junansu ba, tare da tabbatar da tsaron bayanai.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com