Kamfanin iPhone ya kera iPhone 13 Pro Max, wayar da ba a taba irinta ba a fasaha

Kamfanin iPhone ya kera iPhone 13 Pro Max, wayar da ba a taba irinta ba a fasaha

  • Babban kamfanin fasaha na Apple ya sake fitar sabuwar fasahar waya mai ban al'jabi
  • A wannan karon, iPhone za ta fito da ma'ajiyar bayanai da baa taba yin wata mai irinsa ba
  • Wannan ci gaba ya fito ne daga bakin wani shugaban na Apple a jiya Talata 14 ga Satumba

Babban kamfanin fasaha na Apple ya sanar da kirkirar sabuwar waya mai suna iPhone 13 Pro, irinta na farko wanda ke ba da ma'ajiyar bayanai Terabyte daya (1TB), yana bawa masu amfani da iPhone damar adana bayanai kwatankwacin na iPhone 13 sau biyu.

An sanar da sabon samfurin yayin taron yanar gizo da kamfanin a ranar Talata 14 ga watan Satumba, in ji rahotom Peoples Gazette.

Kodayake kamfanin fasahar a baya ya daura ma'ajiyar bayanai 1TB a kan iPad, samfuran iPhone suna da adadin ajiyar da a kai 512GB.

Kara karanta wannan

Kwamandan NDA ya yi wa majalisa bayanin halin da ake ciki kan harin 'yan bindiga a NDA

Kamfanin Apple ya sake kirkirar sabuwar waya mai sabuwar fasaha
Samfurin iPhone 13 Pro da iPhone 13 Pro Max | Hoto: popsugar-assets.com
Asali: UGC

Greg Joswiak, Babban Mataimakin Shugaban kamfanin Apple shashen tallace-tallace na duniya, a wurin taron ya bayyana cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"IPhone 13 Pro da iPhone 13 Pro Max sune mafi kyawun samfuran iPhone na yau da kullum tare da mafi girman ci gaba a tsarin kyamarar mu, mafi kyawun kargin batir a cikin iPhone, da mafi kyawun wajen saurin aiki, saita sabon ma'auni na iPhone da ba da damar abubuwan ban mamaki da ba a taba yi ba."

Apple kuma ya ba da sanarwar yana habaka ma'ajiyar iPhone akan daidaitattun samfuran sa.

Ya batun farashi?

Farashin farko na iPhone a ranar fitar da ita zai fara a $999 kuma za a fara jigilar ta a ranar 24 ga Satumba. Zabin 1TB akan iPhone 13 Pro zai sauki farashin $1,499 da $ 1,599 akan babban iPhone 13 Pro Max.

Kara karanta wannan

Yadda wani mutum ya dirka wa direban keke-napep duka nan take ya mutu

Sabuwar iPhone din na da jerin sabbin abubuwan ingantayya da sabuntawa wadanda suka hada da karamin kira, sabbin fasalolin kyamara wadanda ke ba masu amfani sigar bidiyo na yanayin hoto da zabin daukar bidiyo mai inganci da ake kira ProRes.

Za a iya samun iPhone 13 Pro da iPhone 13 Pro Max a cikin launuka hudu; ruwan toka, ruwan zinariya, ruwan azurfa, da shudi, kamar yadda CNET Tech ta ruwaito.

Kamfanin Apple ya sake kirkirar sabuwar waya mai sabuwar fasaha
Jadawalin farashin sabbin iPhone | Hoto: cnet.com
Asali: UGC

Majalisar dattawa ta bayyana burinta kan sabis na 5G, ta ce NCC ta samar da N350bn

A wani labarin, Majalisar Dattawa ta nemi Hukumar Sadarwa ta Najeriya da ta yi amfani da tsarin sadarwa na 5G don samar wa Gwamnatin Tarayya kudin shiga N350bn a cikin kasafin kudi na shekarar 2022. Idan baku manta ba, mun ruwaito muku cewa, gwamnatin tarayya ta amince a dasa tare da fara amfani tsarin sadarwar 5G a Najeriya, jaridar Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Shin Tinubu zai gaji Buhari? Sanannen sanatan arewa ya fede biri har wutsiya kan mulkin karba-karba

Wannan shi ne hukuncin kwamitocin hadin gwiwa na Majalisar Dattawa da ke aiki kan Tsarin Kudin Matsakaicin Shiri na 2022-2024, lokacin da gudanarwar Hukumar NCC ta bayyana a gaban kwamitin zauren majalisar.

Shugaban kwamitocin hadin gwiwa, Sanata Solomon Adeola, ya ce kasafin kudin 2022 na NCC ba zai zama N115bn ba, wanda shine adadin da ta yi hasashe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel