‘Wallahi duk ’Ya’yansa ne’: Matar Gwamna ga Masu Zarginta da Cin Amanar Mijinta

‘Wallahi duk ’Ya’yansa ne’: Matar Gwamna ga Masu Zarginta da Cin Amanar Mijinta

  • Uwargidan gwamnan Anambra, Nonye Soludo, ta kalubalanci Sanata Uche Ekwunife ta yi rantsuwa a bainar jama’a kan zargin cin amanar aure
  • Nonye Soludo ta nemi a yi gwajin DNA ga ’ya’yansu a manyan asibitoci a Landan, inda ta ce za ta biya kuɗin komai domin a kauda zargi
  • Sanata Ekwunife ta ce irin waɗannan al’amura na gida ne, ta kuma gargadi Mrs. Soludo ka da ta jawo jama’a cikin rikicin iyalinta

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Awka, Anambra - Matar gwamnan jihar Anambra, Nonye Soludo ta dauki zafi game da zargin tana cin amanar mijinta.

Nonye Soludo ta kalubalanci Sanata Uche Ekwunife, tana neman ta yi rantsuwa a gaban Ubangiji kan cin amanar aure.

Matar gwamna ta musa zargin cin amanar mijinta
Matar gwamnan Anambra, Nonye Soludo. Hoto: Nonye Soludo.
Source: Facebook

Matar gwamna ta musa zargin cin amanarsa

A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar a Awka wanda Tribune ta samu, ta zargi Ekwunife da ƙirƙiro ƙarya tare da jawo ’ya’yanta cikin rikicin siyasa.

Kara karanta wannan

Hukumar kwastam: Mutane kusan 600,000 sun nemi guraben aiki da ba su kai 4,000 ba

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta kira halayen Sanata Ekwunife da rashin tunani, tare da gargadin cewa za ta kai ta kotu muddin ba ta janye kalamanta ba cikin sa’o’i 72.

Nonye Soludo ta bayyana cewa rantsuwa a bainar jama’a ita ce hanyar tabbatar da gaskiya da kare halin mutum daga shakku da zargi.

Ta ce:

“Tun shekaru 55 da haihuwata, na san namiji guda ɗaya kacal, Chukwuma Soludo, ke ma ki rantsa, kin yi aure ba tare da cin amana ba.”
Matar tsohon gwamna ta kalubalanci jigon APC
Tsohuwar Sanatar Anambra tare da Bola Tinubu. Hoto: @OfficialAPCNg.
Source: Twitter

An bukaci yin gwajin DNA a asibiti

Haka kuma ta nemi a gudanar da gwajin DNA a manyan asibitoci uku a Landan, inda ta amince da ɗaukar nauyin kuɗin tafiya gaba ɗaya.

Nonye ta ƙara da cewa idan sakamakon ya tabbatar cewa mijin Ekwunife ne ya haifi duk ’ya’yanta, za ta ba ta kyautar kuɗi.

Ta bayyana kanta a matsayin mace mai natsuwa, wadda ta taso da tarbiyya ta addini da kuma kamewa daga fitinar duniya, cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Sabon tarihi: Dubban 'yan auren jinsi sun gudanar da ziyarar bauta a Vatican a karon farko

Martanin Sanata Ekwunife ga uwargidar gwamna

A martanin ta, Sanata Uche Ekwunife ta ce Nonye Soludo ta bar jama’a, ta maida bayaninta kawai ga mijinta, Gwamna Chukwuma Soludo.

Ekwunife ta yi Allah-wadai da kokarin Mrs. Soludo na kare kanta ta hanyar yin ikirarin kamewa da tsoron Allah a bainar jama’a.

Ta ce irin waɗannan batutuwa al’amuran cikin gida ne, wadanda ya kamata su tsaya tsakaninta da mijinta, ba tare da jawo siyasa ba.

“Kalubale ne gare su ko wasu domin tabbatar da gaskiya, amana ta aure ta shafi mijina kaɗai."

- Cewar Nonye

An gano cewa rikicin tsakanin matan biyu ya samo asali ne daga tambayar Gwamna Soludo kan shaidar karatun Ekwunife.

Gwamna ya tabbatar da lafiyar Tinubu

A baya, kun ji cewa gwamna Charles Chukwuma Soludo na jihar Anambra ya bayyana cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na cikin koshin lafiya.

Soludo ya fadi haka ne ranar Talata, 12 ga watan Agusta, 2025 bayan ganawa da Shugaba Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

'Talauci ya yi muni a Najeriya,' El Rufa'i ya ce akwai mafita kan matsin tattalin arziki

Sabanin rade-radin da ake yadawa game da rashin lafiyar Tinubu, Soludo ya ce ya tarar da shugaban kasa cikin koshin lafiya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.