Shanu Sun Cika Abuja: Fadar Shugaban Kasa, Sultan Sun Gana da Miyetti Allah

Shanu Sun Cika Abuja: Fadar Shugaban Kasa, Sultan Sun Gana da Miyetti Allah

  • Fadar shugaban kasa ta nuna damuwa kan yadda shanu ke yawan cika titunan Abuja wanda ke jawo matsaloli a birnin wanda ke jawo matsaloli
  • An yi wata ganawa da shugabannin Miyetti Allah domin kawo karshen kiwon shanu a cikin Abuja, tare da samar da mafita mai dorewa
  • A wajen taron, an tattauna batun makarantun yara makiyaya, wurin kiwo, asibitoci da ingantattun wuraren zama domin inganta rayuwar makiyaya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin ganawa da shugabannin Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN).

Gwamnatin tarayya ta ce an gudanar da ganawar domin dakatar da shanu cika titunan birnin Abuja wanda ke jawo cikas a lamuran yau da kullum.

An yi ganawa da fadar shugaban kasa da Sultan kan makiyaya
Shugaba Bola bu yayin taro a Abuja. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Makiyaya: An tattauna da Sultan da Miyetti Allah

Kara karanta wannan

Iran da kasashen Musulmi za su hadu a Qatar domin daukar mataki kan Isra'ila

Hadimin Tinubu a bangaren kula da kiwon dabbobi, Idris Abiola-Ajimobi shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da Daily Nigerian ta samu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tattaunawar ta gudana ne karkashin jagorancin shugaban kwamitin amintattu na kungiyar MACBAN, Sultan Sa’ad Abubakar III tare da ministan kiwon dabbobi, Idi Maiha.

Idris Abiola-Ajimobi ya jaddada cewa gwamnatin Shugaba Tinubu na aiki tare da ma’aikatun gwamnati don samar da mafita mai dorewa ga matsalar makiyaya.

"Mun zo nan ne domin tattaunawa da masu ruwa da tsaki, an taru ne domin shawo kan matsalolin kiwon shanu a Abuja.
"Muna aiki tare da ma'aikatar ci gaban kiwon dabbobi da sauran hukumomi don zakulo tushen matsalolin.
”Dole mu kawo karshen yawan cika titunan Abuja da shanu ke yi, muna kokarin samar da wuraren kiwo."

Ya kara da cewa ana kokarin samar da kiwo, abinci, ruwa, asibitoci da wuraren zaman lafiya domin makiyaya su samu rayuwa da walwala mai kyau.

Gwamnatin Tinubu ta gana da Miyetti Allah da Sultan a Abuja
Shugaba Bola Tinubu da Sarkin Musulmi, Sa'ad Muhammad Abubakar III. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Korafin Miyetti Allah kan ilimin Fulani a Najeriya

Dr Balarabe Kakale ya ce taron ya tattauna batun ilimi, musamman makarantun almajirai da na yara makiyaya, tare da samun shawarwari daga kowa, cewar Peoples Gazette.

Kara karanta wannan

Tsohon soja zai bada wuri, Simi Fubara zai koma kujerar gwamnan Rivers

Shugaban MACBAN, Baba Othman-Ngelzarma, ya tabbatar da cewa taron ya tattauna batun yara makiyaya da kuma shanu masu yawo a tsakiyar Abuja.

"Kashi 80 daga cikin dari na yara miliyan 20 da ba su zuwa makaranta daga Fulani masu kiwo ne."

Ya ce an gayyato shugabannin MACBAN daga kananan hukumomi da iyalai domin a fahimci dalilan shigarsu birni da nemo hanyoyin magance matsalar.

Othman-Ngelzarma ya bayyana cewa za a kafa kwamiti na musamman domin samar da mafita ta dindindin da za ta hana shanu yawo a Abuja.

Yan bindiga sun kashe shugaban Miyetti Allah

Kun ji cewa 'yan bindiga sun kashe shugaban Miyetti Allah na Barkin Ladi a Plateau, Muhammad Adamu, a gidansa bayan ya gama buda baki a watan Azumi.

Kugniyar MACBAN ta bayyana cewa marigayin ya tsallake yunkurin kisa sau uku a baya, amma wannan karo 'yan bindigar suka kashe shi ba tare da ba ta lokaci ba.

An bayyana kisan Muhammad Adamu a matsayin abin bakin ciki, kasancewar ya taka rawar gani wajen samar da zaman lafiya a yankin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.