"Idan Ka Isa": Sukar Tinubu Ta Jawo Babban Malami Ya Taso El Rufai a Gaba

"Idan Ka Isa": Sukar Tinubu Ta Jawo Babban Malami Ya Taso El Rufai a Gaba

  • Satguru Maharaj Ji ya yi gargadi ga tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, kan yin maganganun da za su iya raba kan ’yan kasa
  • Ya ce shugaba Bola Tinubu yana kan hanya madaidaiciya kuma ya cancanci goyon baya
  • Hakazalika, ya kalubalanci El-Rufai kan ya rantse cewa bai taba yin sama da fadi kan amanar da aka ba shi ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Ibadan, jihar Oyo - Shugaban addini kuma wanda ya kafa One Love Family, Satguru Maharaj Ji, ya gargadi tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, kan sukar Shugaba Bola Tinubu.

Satguru Maharaj Ji ya bukaci Nasir El-Rufai kan ya daina yin kalaman da za su iya haifar da rabuwar kai a tarayyar Najeriya.

An gargadi El-Rufai kan sukar Tinubu
Hoton shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da Nasir El-Rufai Hoto: @DOlusegun, @elrufai
Source: Facebook

Jaridar The Nation ta kawo rahoton cewa Satguru Maharaj Ji ya yi wannan gargadin ne bayan kalaman El-Rufai da ke cewa Najeriya ba za ta tsira ba idan jam’iyyar APC ta sake lashe zaben 2027.

Kara karanta wannan

'Talauci ya yi muni a Najeriya,' El Rufa'i ya ce akwai mafita kan matsin tattalin arziki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"El-Rufai na kokarin haifar da rikici ta fuskar siyasa da addini. Shi mutum-mutumi ne na masu son rarraba kan bakar fata ta hanyar addini. Amma a Afrika muna da dokoki da ka’idojinmu na dabi’a."

- Satguru Maharaji Ji

An kalubalanci El-Rufai kan satar dukiya

Satguru Maharaj Ji ya kalubalanci El-Rufai da ya rantse a gaban jama’a cewa bai taba satar kudin gwamnati ba.

"Ya fito talabijin dauke da gilashin ruwa ya rantse. Idan har yana da gaskiya, za mu abin da zai faru cikin makonni hudu."

- Satguru Maharaj Ji

Shugaban addinin ya kuma soki shugabannin siyasa da na addini da suka yi shiru lokacin hare-haren makiyaya a Kudancin Najeriya, amma yanzu suna yin surutu saboda tasirinsu na raguwa.

"Sun yi shiru kan kashe-kashen Benue da Plateau. Yanzu kuma da tasirinsu ya ragu, sun dawo suna cewa sun damu."

- Satguru Maharaj Ji

Shugaba Tinubu ya samu goyon baya

Game da shugaba Bola Tinubu, Maharaj Ji ya ce shugaban kasan yana daukar matakai masu karfi wajen gyara kasar nan da suka hada da samar da ilimi kyauta, taimakawa ’yan kasuwa, inganta wutar lantarki.

Kara karanta wannan

Yaron El Rufa'i: Uba ya yi raddi ga kalamai da zarge zargen tsohon Gwamnan Kaduna

"Tinubu yana dawo da fata kuma yana aiki don ci gaban kasa."

- Satguru Maharaj Ji

Satguru Maharaj Ji ya caccaki Nasir El-Rufai
Hoton shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da Nasir El-Rufai Hoto: @DOlusegun, @elrufai
Source: Twitter

Maharaj Ji ya yi kira ga ’yan Najeriya

Satguru Maharaj Ji ya bukaci ’yan Najeriya da su kasance tsintsiya madaurinki daya, su guji bari ana amfani da su wajen cimma manufofin siyasa.

“Najeriya ba kasa ce da ake yaki ba. Ya kamata El-Rufai da tawagarsa su kyalemu mu huta. Mun aminta da shugabancin Tinubu."

- Satguru Maharaj Ji

Nasir El-Rufai ya caccaki 'yan sanda

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya nuna fushinsa kan wani matakin da 'yan sanda su ka dauka.

Nasir El-Rufai ya soki 'yan sandan Kaduna bayan sun hana gudanar da wani taron jam'iyyar hadaka watau ADC.

Tsohon gwamnan ya dage cewa matakin da 'yan sanda duka dauka na hana gudanar da taron ya ci karo da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng