'Dan Majalisa, Adamu Aliyu Ya Aikata Laifi Mai Girma, Kotu Ta Ayyana Nemansa Ruwa a Jallo
FCT Abuja - Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ayyana Hon. Adamu Aliyu, ɗan majalisar dokokin jihar Filato, a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo.
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kotun ta ba da umarnin cafke dan Majalisar duk inda aka gan shi bisa zargin damfarar wani ɗan kasuwa Naira miliyan 73.6 ta hanyar kwangilar TETFund ta bogi.

Source: Facebook
Mai shari’a Emeka Nwite ne ya bayar da wannan umarni a ranar Juma’a a wata buƙata daga hukumar yaki da rashawa, ICPC, ta shigar, in ji rahoton Premium Times.
Wane laifi dan Majalisar ya aikata?
Tun farko wani ɗan kasuwa, Mohammed Jidda, ya shigar da korafi ga ICPC yana zargin ɗan majalisar da yi masa alƙawarin taimakawa wajen samun kwangilar TETFund mai darajar N850m a Jami’ar Jos.
An ce ɗan majalisar ya rattaba hannu kan yarjejeniya (MoU) da Mohammed, wacce dan kasuwar ya yi alkawarin ba shi ladan Naira miliyan 73.6 idan aka samu kwangilar.
'Dan kasuwar ya ce, Hon Aliyu ya ba shi takardar bogi da ke nuna cewa jami’ar Jos ta ba shi kwangilar gina dakin motsa jiki a ƙarƙashin shirin TETFund mai darajar N500m.
Da wannan takarda, dan Majalisar ya bayar da lambar asusun ajiyarsa a GTBank da kuma asusun kamfanin Imanal Concept Ltd a Zenith Bank, kuma dan kasuwar ya tura kudin.
Sai dai daga baya dan kasuwar ya gano cewa babu wata kwangila da aka ba shi a Jami'ar Jos lokacin da ya je domin fara aiki, hakan ya sa ya kai kara hukumar ICPC.
Abin da ICPC ta gano a binciken da ta yi
ICPC ta buɗe bincike kuma ta samu bayanan asusun banki da ke nuna yadda kuɗin suka shiga asusun Aliyu mai wakiltar Jos ta Arewa a Majalisar dokokin Filato.
Rahoton ya nuna cewa:
- N47.8m sun shiga asusun GTBank na Aliyu kai tsaye,
- N22.4m sun shiga asusun kamfanin Imanal Concept Ltd a Zenith Bank,
- Sai kuma N3.2m da akakara turawa kai tsaye ga Aliyu.
Bukatar da hukumar ICPC ta shigar a kotu
Hukumar ICPC ta gayyace shi ta hannun magatakardar majalisar dokokin Filato da kuma ta WhatsApp, inda aka ce ya karɓi saƙon, amma ya ki zuwa.
Hukumar ta kuma shaidawa kotu cewa ta samu bayanan sirri na cewa Aliyu na shirin tserewa daga ƙasar nan don guje wa bincike.
Saboda kin amsa gayyata, ICPC ta nemi kotu ta ba ta izinin bayyana shi a matsayin wanda ake nema a jaridun ƙasa, shafukan sada zumunta da sauran kafafen watsa labarai.

Source: Facebook
Kotun Abuja ta amince da bukatar ICPC
A ranar Juma’a, Mai shari’a Nwite ya amince da bukatar ICPC, ya bayar da umarnin kama shi, tare da ba da izini a wallafa sanarwar neman Aliyu a jaridun ƙasa da kafafen sada zumunta.
Hukuncin ya kuma bai wa jami’an tsaro da ‘yan sanda da mafarauta masu zaman kansu ikon kama shi tare da mika shi ga ICPC domin bincike.
EFCC ta ayyana neman attajirin dan kasuwa
A wani labarin, kun ji cewa hukumar EFCC ta ayyana neman shugaban kamfanin Sujimoto Luxury Construction Limited, Olasijibomi Suji Ogundele ruwa a jallo.
Hukumar EFCC ta roƙi duk wanda ke da sahihin bayani game da inda Ogundele ya buya da ya gaggauta kai rahoto ofishinta mafi kusa da shi.
A cikin sanarwar da ta fitar, hukumar EFCC ta ce tana neman Ogundele ne kan zargin karkatar da kuɗi da kuma safarar kudin haram.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


