Aikin Titi: Gwamnatin Tinubu za Ta Kashe Naira Tiriliyan 3 a Jihohin Arewa 2
- Ministan ayyuka Sanata David Umahi ya bayyana cewa aikin babbar hanyar Sokoto zuwa Kebbi zai lashe sama da Naira tiriliyan 3
- Ya ce aikin wani bangare ne na shirin shugaba Bola Tinubu na inganta hanyoyin mota da layin dogo a dukkan yankunan Najeriya
- David Umahi ya bayyana cewa Arewa maso Yamma ce ke da kaso mafi girma na ayyukan raya kasa a mulkin Shugaba Bola Tinubu
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Ministan ayyuka na tarayya, Sanata David Umahi, ya bayyana cewa aikin babbar hanyar da za ta hada Sokoto da Kebbi zai ci kudi sama da Naira tiriliyan 3.
Ya fadi haka ne a yayin da ya duba wani bangare na aikin da aka riga aka share a karamar hukumar Silame ta jihar Sokoto.

Source: Facebook
Vanguard ta wallafa cewa ministan ya ce akwai jita-jitar da ake yadawa cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta yi watsi da yankin Arewa maso Yamma wajen aiwatar da manyan ayyuka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai ya musanta hakan, inda ya ce aikin babbar hanyar hujja ce ta irin goyon bayan da gwamnati ke baiwa yankin.
Umahi ya fadi ayyukan da Tinubu ke yi
Umahi ya jero wasu daga cikin manyan ayyukan da gwamnati ta sanya hannu a kansu, kamar su babbar hanyar ruwan teku daga Legas zuwa Calabar mai tsawon kilomita 750.
Haka zalika ya ambaci hanyar Sokoto-Badagry mai tsawon kilomita 1,068, hanyar Calabar-Abuja duk a fadin Najeriya.
Ya ce an tsara wadannan hanyoyi da kyau, tare da sanya fitilu, na’urorin CCTV, tashoshin lafiya da tsaro, domin bada taimakon gaggawa a duk lokacin da aka bukata.
Haka kuma ya ce hanyar Sokoto-Badagry za ta fara daga Illela a Sokoto zuwa Badagry a jihar Legas, abin da ya kira shaida ta jajircewar shugaban kasa wajen farfado da tattalin arziki.
Za a kashe N3tn a titin Sokoto da Kebbi
A cewar minista ayyuka, jihohin Kebbi da Sokoto ne suka fi cin gajiyar aikin titin da shugaba Tinubu ke yi.
Ya ce Kebbi za ta samu aikin da kudinsa ya kai Naira tiriliyan 2, yayin da Sokoto ta samu Naira tiriliyan 1 a bangaren hanyar.
Ya kara da cewa kafin karshen shekarar 2026 za a kammala kimanin kilomita 120 na hanyar daga bangaren Sokoto.

Source: Facebook
Sahara Reporters ta wallafa cewa ya ce aikin zai tabbatar da cewa gwamnatin Shugaba Tinubu ta cika alkawarin ta.
Umahi ya kara da cewa shugaban kasa ya umurce shi da kada a dakatar da ko wane aiki, ciki har da wadanda ake gudanarwa karkashin tsarin kudin NNPCL.
Minista ya ce Tinubu ya karya farashin abinci
A wani rahoton, kun ji cewa ministan noma, Sanata Abubakar Kyari ya tabbatar da cewa shugaban kasa ya ya karya farashin abinci.
Ministan ya bayyana cewa an shigo da kayan abinci daga ketare na wata shida domin karya farashinsa a Najeriya.
Sanata Kyari ya kara da cewa ba domin karya manoma aka shigo da abinci ba, sai dai a cewarsa, suma an tallafa musu da taki.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


