Tinubu Ya Gwangwaje Kungiyar Izalah da Kyautar Miliyoyi, Ya Yaba da Gudunmawarta
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yabawa kungiyar Izala ta bangaren Jos kan gudunmawar da suka ba shi a Najeriya
- Shugaban ya bayar da gudunmawar miliyoyi ga kungiyar JIBWIS reshen Gombe, a wajen kaddamar da sabon dakin ajiyar gawa
- Ministan sufuri, Sanata Sa’idu Alkali, ya ce ya gina cibiyar ne saboda alherin da ke ciki, sannan ya yabawa kungiyar JIBWIS
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gombe - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da tallafin miliyoyin kudi ga kungiyar JIBWIS a Najeriya.
Shugaban ya yabawa kungiyar Izalah da irin gudunmawar da ta ba shi a gwamnatinsa wanda ba zai manta ba.

Source: Facebook
Tinubu ya ba Izalah kyautar miliyoyin kudi
Hakan na cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara a bangaren sadarwa, Umar Alkali Jibrin ya tabbatar a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan
Ganduje ya kafa kwamiti, zai binciki gwamnatin Kano kan korar kwamandojin Hisbah 44
Tinubu ya ba kungiyar reshen Gombe gudunmawar Naira miliyan 10 domin inganta ayyukansu duba da gudunmawar da suke ba shi.
Shugaban ya ba da gudunmawar ne domin nuna goyon bayansa ga kungiyar Musuluncin da ta ba shi goyon baya.

Source: Facebook
Musabbabin ba da tallafi da Tinubu ya yi
Sanarwar ta fito daga Ministan Sufuri, Sanata Sa’idu Alkali, bayan sallar Juma’a a ranar 12 ga Satumba, lokacin kaddamar da sabon dakin ajiye gawa.
Alkali ya bayyana cewa aikin ya samo asali daga imanin cewa mutuwa dole ce ga kowa, ya kuma jaddada muhimmancin tallafawa kungiyoyin addini.
Kungiyar ta yabawa kokarin shugaba Tinubu
A madadin jagoran kasa na JIBWIS, Sheikh Nasiru Abdulmuhyi ya gode wa Tinubu da ministan, tare da tunatar da Musulmi su kiyaye koyarwar addini.
Sheikh Abdulmuhyi ya kuma yaba wa ministan bisa gina asibitin kwararru a Mallam Sidi, domin kusantar da ingantattun ayyukan lafiya ga talakawa.

Kara karanta wannan
'Sau 2 ba mu sallar Juma'a': Musulmai sun roki sauya ranar nadin Sarki da za a yi
Ministan Sufuri, Alkali ya dare kan kujerar minista ne a mulkin Tinubu da aka rantsar da shi a 2023 bayan Sanatan ya fadi zabe a Gombe.
'Dan agaji ya tattauna da Legit Hausa
Wani dan agaji da ya halarci bikin da aka gudanar, Umar Sa'id ya ce abin yabawa ne duba da muhimmancin aikin da aka kaddamar.
Sa'id ya ce ya ji dadin wannan aiki da kuma gudunmawar Tinubu kamar yadda shugabanninsu suka nuna farin cikinsu da kuma yi wa shugaban godiya.
"Tabbas wannan abin alheri ne duba da cewa mutua mutuwa tana kan kowa hakan wata hanya ce ta samun lada wanda ba zai yanke ba.
"Muna godiya ga Minista Alkali da irin kokarin da yake yi kamar yadda shugabanmu, Sheikh Abdulmuhyi ya ce ya gina asibitin kwararru a Malam Sidi."
Mataimakin gwamnan Kano ya gana da manyan Izala
A baya, kun ji cewa mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya kai ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Plateau inda ya gudanar da taruka da dama.
Gwarzo ya ziyarci Sheikh Sani Yahaya Jingir domin yin ta’aziyya bisa rasuwar ɗan uwansa a watannin baya.
Haka kuma ya kaddamar da ofishin Kwankwasiyya a Jos, ya gana da shugabannin jam’iyya da kungiyoyi daban-daban, ya halarci bikin yaye dalibai.
Asali: Legit.ng
