Najeriya da Kasashe 141 Sun ba Isra'ila Kunya, Sun Goyi bayan Kafa Kasa a Gaza

Najeriya da Kasashe 141 Sun ba Isra'ila Kunya, Sun Goyi bayan Kafa Kasa a Gaza

  • Rahotanni sun nuna cewa kasashe 142 daga cikin 193 sun amince da kudurin kafa kasashe biyu tsakanin Isra’ila da Falasɗinu
  • Hakan na zuwa ne bayan Firayim Ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce ba zai taɓa yarda da kafa ƙasar Falasɗinu ba
  • A daya bangaren kuma, kasar Amurka ta bayyana adawa da kudurin, tana cewa matakin zai ƙarfafa kungiyar Hamas ne kawai

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Amurka - Majalisar Dinkin Duniya ta kada kuri’a a ranar Juma’a inda mafi rinjayen ƙasashe suka goyi bayan kafa ƙasar Falasɗinu a matsayin mafita kan hare haren da Isra'ila ke kai musu.

Wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da rikicin Gaza da mamayar Isra'ila ta jawo ya kai kusan shekaru 80.

Kasashe daban daban a wani zama na majalisar dinkin duniya
Yan kasashe daban daban a wani zama na majalisar dinkin duniya. Hoto: United Nations
Source: Facebook

Rahoton Yahoo News ya nuna cewa kudurin na ɗauke da tsare-tsaren matakai da za a bi don kawo ƙarshen rikicin, tare da buƙatar Isra’ila ta amince da kafa ƙasar Falasɗinu.

Kara karanta wannan

Netanyahu ya yi barazanar sake kai hari Qatar, ya kafa wa kasar Larabawan sharadi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Benjamin Netanyahu, ya yi watsi da kudurin gabanin kuri’ar, inda ya ce ba zai taɓa amincewa da kafa ƙasar Falasɗinu ba.

Kasashe sun goyi bayan Falasdinu

Daga cikin ƙasashe 193 da ke cikin Majalisar Dinkin Duniya, ƙasashe 142 ne suka goyi bayan kudurin, 10 suka ƙi, yayin da 12 suka kaurace masa.

Kudurin dai ba na wajibi ba ne amma yana nuna matsayar duniya kan bukatar samar da mafita mai ɗorewa ga rikicin Falasɗinu da Isra’ila.

Kasashen Faransa da Saudiyya ne suka jagoranci kasashen bayan taron koli da suka shirya a watan Yuli domin tattauna hanyoyin aiwatar da mafita a Gaza.

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya tabbatar da goyon bayan kudirin a wani sako da ya wallafa a X.

Matsayar Falasɗinu kan kudirin

Jakadan Falasɗinu a majalisar dinkin duniya, Riyad Mansour, ya bayyana wannan sakamako a matsayin shaidar cewa yawancin ƙasashen duniya suna son a bude hanyar zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Shirin kifar da Tinubu: Peter Obi ya gana da Goodluck Jonathan a Abuja

Falasɗinu ta kuma bayyana fata cewa ƙasashe fiye da 10 za su ƙara shiga cikin jerin ƙasashe 142 da suka riga suka amince da kafa ƙasar.

Yadda hare haren Isra'ila suka ruguza wani yanki na Gaza
Yadda hare haren Isra'ila suka ruguza wani yanki na Gaza. Hoto: Getty Images
Source: AFP

Matsayar Isra’ila da abokan hulɗarta

Jakadan Isra’ila a majalisar dinkin duniya, Danny Danon, ya ce wannan kuduri ba zai kawo zaman lafiya ba, sai dai ya ƙara nuna rauni ga majalisar.

Amurka, wadda ita ce aminiyar Isra’ila mafi kusa, ta bayyana adawa da kudurin, tana mai cewa

“Ba daidai ba ne kuma mataki ne da zai iya lalata ƙoƙarin diflomasiyya na gaskiya.”

Kudurin ya kuma yi suka kan hare-haren Isra’ila a Gaza, inda aka ce sun shafi fararen hula da abubuwan more rayuwa kuma suna jawo mummunan bala’i.

Isra'ila ta yi barazanar kai hari Qatar

A wani rahoton, kun ji cewa ana cigaba da maganganu bayan harin da Isra'ila ta kai birnin Doha na kasar Qatar.

Rahotanni sun nuna cewa Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa ba za a sake kai irin harin ba.

Sai dai shugaban Isra'ila ya nuna cewa zai iya sake kai hari Qatar matukar 'yan Hamas na shiga kasar kuma ba a kama su ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng