An Bankado Abubuwa, Matar Shedanin 'Dan Bindiga Ta Shiga Hannu a Zamfara, Ta Tsure

An Bankado Abubuwa, Matar Shedanin 'Dan Bindiga Ta Shiga Hannu a Zamfara, Ta Tsure

  • Sojojin 1 Brigade sun samun gagarumar nasara musamman game da yaki da yan bindiga a jihar Zamfara a cikin kwanan nan
  • Rundunar ta kama wata mata mai suna Fatima Isah Ile a Kanoma, bisa zargin taimakawa ‘yan ta’adda wajen ayyukansu.
  • An ce ta ɓoye a wani gini da ba a kammala ba, tana amfani da yara wajen sayen man fetur, an gano abubuwa da dama

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gusau, Zamfara - Yaki da ta'addanci musamman a Arewacin Najeriya na ci gaba da samun nasara yayin da ake kama masu hannu a ciki.

Sai dai hakan bai zuwa da sauki saboda yadda mutanen gari da dama ke taimakawa yan bindiga da bayanai da ke kai hare-hare.

Sojoji sun kama matar rikakken dan bindiga
Ministan tsaro a Najeriya, Mohammed Badaru Abubakar. Hoto: Defence Headquaters Nigeria.
Source: Facebook

Rahoton Zagazola Makama ya tabbatar da cewa jami'an tsaro sun yi nasarar cafke wata mata da ke taimakon yan bindiga a harkokinsu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace sanannen 'dan siyasa da wasu bayin Allah a jihar Kaduna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan bindiga: Yadda jami'an tsaro ke samun nasara

Wannan ba shi ne karon farko ba da jami'an tsaro ke samun nasara musamman bayan samun bayanan sirri.

Ko a kwanakin nan ma, jami'an tsaro sun cafke wasu daga cikin yan bindiga wadanda suka kai hari kan masallata.

Rahotanni sun nuna cewa masu ibadar uku sun shiga hannun ‘yan bindiga yayin sallar Asuba a garin Dansadau, Zamfara.

An cafke 'yan bindiga a jihar Zamfara

Biyo bayan lamarin, jami’an tsaro sun cafke mutum shida da ake zargi da hannu a harin da ya faru a masallaci wanda ya yi sanadin mutane da dama.

Sojojin Najeriya sun kai hare-haren sama da ƙasa a yankunan inda suka yi nasara hallaka wasu daga 'yan ta'adda.

Jami'an tsaro sun kama matar dan bindiga a Zamfara
Taswirar jihar Zamfara da ke Arewa maso Yamma a Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Yadda aka kama matar tantirin 'dan bindiga

Majiyoyi sun tabbatar da cewa an kama matar ne a garin Kanoma da ke jihar Zamfara da ke fama da matsalar 'yan bindiga musamman a yankunan karkara.

Kara karanta wannan

Mutum 4 sun mutu, wasu sun raunata da yan bindiga suka farmaki wajen jana'iza

An bayyana cewa matar mai suna Fatima Isah Ile ta shiga hannun jami’an tsaro ne a cikin wani gini da ba a kammala ba.

An zarge ta da yaudarar yara tana sayar musu kayan aiki, ta na neman su sayo mata man fetur yayin da aka gano jarkoki uku na mai a wurinta.

Binciken farko ya gano cewa matar ita ce matar sanannen ɗan ta’adda, Isah Ile, wanda ake zargi da ayyukan ta’addanci a yankin.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa an miƙa wacce ake zargin zuwa ga Hukumar DSS domin ƙarin bincike da daukar matakan da suka dace.

'Yan bindiga sun hallaka mutane a Zamfara

A baya, kun ji cewa ‘yan bindiga sun kai harin ba zata wani yanki na karamar hukumar Gusau da ke jihar Zamfara inda su ka bude wa jama'a wuta.

Rahotanni sun bayyana cewa jama'a na tsaka da tafiyar da harkokinsu a yammacin Lahadi 7 ga watan Satumbar 2025, sai kawai su ka ji harbi ta ko ina.

Mutane sun dimauce, inda su ka rika gudun neman mafaka, amma duk da haka an salwantar da rayukan bayin Allah.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.