Yawan Rayuka da Aka Rasa a Gaza bayan Mummunan Harin da Isra'ila da Ta Kai
- Rahotanni sun ce Isra'ila ta kuma kai hare-harena Gaza da ke Gabas ta Tsakiya wanda ya hallaka mutane da dama
- An ce harin ya hallaka mutum 50 a rana guda, lamarin da ya kara tayar da hankulan kasashe da dama
- Kasashen duniya ciki har da Birtaniya, Faransa da Jamus sun bukaci a dakatar da farmakin saboda asarar rayuka
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gaza - Sojojin Isra’ila sun kuma kai wani mummunan hari a Gaza wanda ya sake tayar da hankula.
An ce harin ya hallaka mutum 50 a Gaza a ranar Juma’a 12 ga watan Satumbar 2025 da muke ciki.

Source: Getty Images
Abin da Isra'ila ke nufi a Gaza
Rahoton France 24 ya ce hukumar kashe gobara ta yankin ta kai dauki game da hare-hare wanda suka tsananta.
Isra’ila ta ce tana shirin kwace birnin Gaza, cibiyar mafi girma a yankin, wanda ta bayyana a matsayin karshe sansanin kungiyar Hamas.
Majalisar Dinkin Duniya da kasashen duniya sun yi gargadi, suna cewa farmakin zai kara jawo tabarbarewar yanayin jin kai a Gaza.
Birtaniya, Faransa da Jamus sun fitar da sanarwa tare, suna kira da a dakatar da farmakin nan take, suna mai jaddada asarar rayuka da rushewar kayayyakin more rayuwa.
Hukumar kashe gobara ta Gaza ta ce mutum 35 sun mutu a cikin birnin, yayin da wasu 15 suka mutu a sauran wuraren Gaza.
Sojojin Isra’ila sun ce suna ci gaba da kai “hare-haren manyan gine-gine da cibiyoyin ta’addanci” domin karya karfin Hamas.
Rahotanni sun nuna cewa kasar Isra’ila ta fara kai hare-haren gine-ginen tsawo mako guda da ya wuce, tana ikirarin Hamas na amfani da su.
Hukumar kashe gobara ta ce harin guda daya a Arewa maso Yammacin Gaza ya kashe mutane 14, mafi yawan su yara da mata, cewar rahoton Aljazeera.

Kara karanta wannan
Netanyahu ya yi barazanar sake kai hari Qatar, ya kafa wa kasar Larabawan sharadi
“Mutane biyu kacal aka gano jikinsu duka, sauran duk sassan jiki ne kawai."
- Cewar wata majiya

Source: UGC
Halin da ake ciki a Gaza bayan harin Isra'ila
A asibitin Al-Shifa, an ga mutane suna yi wa gawarwaki salla, wadanda aka lullube da farin likkafani, ciki har da yara kanana.
Yawancin mazauna sun ce babu inda za su tafi, domin wuraren da aka umarce su su koma ma su ne Isra’ila ke kai hari.
Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta mutane miliyan daya ke cikin Gaza da kewaye, tana gargadi cewa kora su gaba daya zai iya haifar da bala’i.
Sojojin Isra’ila sun ce suna shirin “kara yawan agaji” a kudancin yankin don karbar wadanda suka tsere daga Gaza.
Isra'ila ta sake barazana kan Qatar
Kun ji cewa shugaban Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya ce ƙasarsa na iya sake kai hari Qatar idan ba ta kori Hamas daga ƙasarta ba.
Qatar ta yi tir da harin da Isra’ila ta kai a Doha, tana kiran shi take hakkin kasa da kasa da barazana ga tsaron ƙasar.
Hakan na zuwa ne bayan Donald Trump ya bayyana cewa bai amince da harin ba, yana mai cewa ba zai sake faruwa a Qatar ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

