Matasa Za Su Wartsake, Gwamna Ya Kafa Tarihi bayan Naɗa Hadimai 1,200 a Jiharsa
- Gwamnatin Ogun ta kafa tarihi a jihar bayan nada hadiman gwamna na musamman mafi yawa a kan harkokin siyasa
- An nada mataimakan na musamman kan siyasa 1,200 domin inganta alaka da jama’a cikin mulki saboda kara kusanci da gwamnati
- Majiyoyi sun ce an yi haka domin yada ayyuka da amfanin dimokuraɗiyya a dukkan kananan hukumomin da ke jihar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abeokuta, Ogun - Gwamnatin jihar Ogun ta nada mataimaka na musamman kan harkokin siyasa fiye da 1,000 a jihar.
Gwamna Dapo Abiodun ya amince da nadin hadiman 1,200 domin su zama wakilai, su kuma ƙarfafa shiga jama’a cikin harkokin mulki a fadin jihar.

Source: Facebook
Mai ba da shawara na musamman kan yada labarai da dabaru ga Gwamna Dapo Abiodun, Kayode Akinmade, shi ya tabbatar da haka a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Musabbabin nada hadimai 1,200 a jihar Ogun
Akinmade ya bayyana wannan matakin nada hadiman a matsayin dabarar inganta dimokuraɗiyya da cudanya da al'umma tun daga tushe.
Ya ce:
"Domin cika alkawarin ta na zurfafa shiga harkokin dimokuraɗiyya da kuma faɗaɗa damar samun ribar dimokuraɗiyya.
"Gwamnatin Ogun ta naɗa mataimaka a bangaren siyasa 1,200 domin su zama jakadun kawo sauyi tare da ƙarfafa haɗin kan jama’a a fadin jihar."
Yadda aka fasalta nadin hadimai 1,200 a Ogun
A cewar Akinmade, mataimakan biyar daga kowace mazaba cikin mazabu 236 na Ogun za su tabbatar da shiga jama’a sosai, tare da haɗa gwamnati da talakawa.
Ya kara da cewa:
“Sababbin mataimakan kan harkokin siyasa za su tallafa wajen isar da amfanin dimokuraɗiyya, bayyana bukatun mazabunsu, tare da isar da bukatun ga gwamnatin jiha.
"Har ila yau, ana tsammanin masu mukaman za su mayar da martanin da gwamnatin ta yi game da bukatun yadda ya dace ga al'umma da suka tura korafinsu.

Source: Facebook
Rokon Gwamna ga sababbin hadimai da ya nada
Akinmade ya ƙara da cewa suna kuma da alhakin bayar da sahihan rahotanni daga gwamnati zuwa mazabu da kuma daga jama’a zuwa gwamnati kai tsaye.
Mista Akinmade ya jaddada cewa wannan shiri da daga cika alkawuran zaben Gwamna Dapo Abiodun na tafiyar da gwamnati mai mu'amala da kowa da kowa.
Gwamnatin ta kuma bukaci sababbin mataimakan su bayar da gudummawa wajen ci gaban mazabu, kananan hukumomi da kuma jihar gaba ɗaya.
Gwamna Abiodun ya maka Sarki a kotu
A baya, mun ba ku labarin cewa gwamnatin jihar Ogun ta gurfanar da sarkin Obafemi, Oba Taofeek Owolabi a kotu bisa zargin kwace da sayar da fili ba bisa ka’ida ba.
An ce Sarkin ya sayar wa wani mutumi wata gona a kan ₦75m, amma ya ki ba masu gonar kuɗinsu, sai ma ya tura masu 'yan daba suka yi musu cin mutunci.
Duk da gayyatar majalisar dokokin jihar da majalisar sarakunan gargajiya, Oba ya ƙi mika wuya, lamarin da ya kai ga gurfanar da shi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


