Mutum 4 Sun Mutu, Wasu Sun Raunata da Yan Bindiga Suka Farmaki Wajen Jana'iza
- 'Mutane sun sake shiga tashin hankali bayan wanda suke ciki game da harin 'yan bindiga ana zaman makoki
- Rundunar ’yan sanda ta tabbatar da mutuwar mutane hudu tare da jikkata 15 a harin da aka kai wajen jana’iza
- Rahotanni sun nuna ’yan bindiga sun afka wajen jana’izar a kauyen Ezi, a Anambra, inda suka bude wuta kan masu makoki
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Awka, Anambra - Rundunar ’yan sanda ta yi magana kan harin da yan bindiga suka kai kan masu zaman makoki wanda ya jawo asarar rayuka.
Yan sanda a jihar Anambra sun tabbatar cewa an kashe mutane hudu yayin da wasu 15 suka jikkata a hari kan masu jana’iza a Ogidi.

Source: Original
'Yan bindiga sun kai hari kan masu jana'iza
Wani faifan bidiyo da The Nation ta gano ya nuna cewa kisan kan masu jana’izar ya faru ne a ranar Alhamis 11 ga watan Satumbar 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a kauyen Ezi da ke yankin Ogidi a karamar hukumar Idemili ta Arewa a jihar.
Majiyoyi sun nuna wasu daga cikin wadanda suka jikkata suna kwance a asibiti, bayan maharan sun bude musu wuta a wajen jana’izar.

Source: Facebook
Abin da yan sanda suka ce kan harin
Kakakin rundunar yan sanda, Tochukwu Ikenga, ya ce binciken farko ya nuna lamarin ya shafi rikicin kungiyoyin asiri da ke fafatawa a yankin.
Rundunar yan sanda ta kara da cewa an kaddamar da bincike don gano wadanda suka aikata harin tare da tabbatar da kama su domin hukunta su.
Ikenga ya kuma yi kira ga jama’a da su taimaka da bayanai kan gano maharan, tare da sanar da ’yan sanda idan akwai wani abu, cewar rahoton Daily Post.
A cewarsa:
“Bayan samun kiran gaggawa ranar 11 ga Satumba, ’yan bindiga da ake zargi da ’yan asiri sun kutsa wajen jana’iza a Ogidi, sun bude wuta kan mutane, inda mutum hudu suka mutu yayin da wasu 15 suka samu raunuka masu tsanani.
“’Yan sanda daga sashen Ogidi, karkashin DPO, sun isa wajen da sauri, suka kwantar da tarzoma, tare da kai wadanda suka jikkata asibiti, an samu nasarar gano harsashi 16 da aka harba a wajen.
“Kwamishinan ’yan sanda, Ikioye Orutugu ya yi tir da lamarin, tare da tabbatar da kudirin kawar da tashin hankali daga jihar.”
Rundunar ta kuma bukaci jama’a da su kasance masu kula da tsaro, tare da ci gaba da kai rahoton duk wani yanayi da ake zargi.
'Yan bindiga sun farmaki masallata a Katsina
Mun ba ku labarin cewa wasu yan bindiga sun kai hari kan wasu Musulmai da ke sallar Isha a jihar Katsina.
An tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a garin Matazu da ke Katsina, inda aka kashe wasu tare da jikkata da dama.
Hakan na zuwa ne yayin da wasu yankunan jihar ke sulhu da yan bindiga wanda ya sake sanya shakku kan maganar tattaunawa da yan bindiga.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

