Katsina: Yan Bindiga Sun Afka Wa Masallata, Sun Sace Musulmai a Sallar Isha, an Rasa Rai
- Duk da kokarin zaman sulhu da wasu yankuna ke yi a jihar Katsina, yan bindiga na ci gaba da kai hare-hare a jihar wanda ke shan fama da matsalolin tsaro
- Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa yan bindiga sun kai hari kan wasu Musulmai da ke sallar Isha a jihar da ke yankin Arewacin Najeriya
- An tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a garin Matazu da ke Katsina, inda aka kashe wasu tare da jikkata wasu wanda ya sake sanya shakku kan maganar sulhu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Matazu, Katsina - Har yanzu ana ci gaba da fusknatar hare-hare a jihar Katsina duk da cewa wasu yankuna na maganar sulhu.
Akalla kananan hukumomi hudu suka yi zama da yan bindiga a jihar domin samun sauki a wajen hare-haren yan bindiga.

Source: Facebook
Majiyar Bakatsina a shafin X da ke kawo rahotanni kan rashin tsaro a Najeriya ya ce yan bindiga sun farmaki masallata a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Maganar sulhu da 'yan bindiga a Katsina
Wannan sababbin hare-hare na zuwa ne yayin da ake ta maganar sulhu da yan bindiga musamman a jihar Katsina.
A baya-bayan nan, ana samun karin kananan hukumomi a jihar Katsina da ke kulla sulhu da jagororin 'yan ta'adda domin kawo karshe kashe su ba dare ba rana.
Akalla kananan hukumomi hudu ne suka kulla yarjejeniya da yan bindiga domin rage yawan hare-haren da ake kai wa wanda kuma wasu daga ciki sun nuna farin ciki game da lamarin.
Daga cikin kananan hukumomin da aka yi zaman sulhun akwai Jibia da Danmusa da Batsari da kuma karamar hukumar Safana.

Source: Original
'Yan bindiga sun farmaki masu salla a Katsina
An ce yan bindiga sun kai hari kan masallata yayin sallar Isha a garin Matazu da ke jihar Katsina a Arewa maso Yammacin kasar.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa yan bindigan sun kashe wasu mutane tare da jikkata wasu yayin harin da aka kai.
Majiyar ta ce:
“Daren jiya, ’yan bindiga sun kai hari garin Matazu a Katsina, lokacin sallar Isha, sun kashe wasu da jikkata masu ibada.
“Dole gwamnati ta dauki matakin gaggawa saboda hare-haren da ake kaiwa kan masu ibada a Arewa maso Yamma sun yi yawa.”
Hukumomin jihar Katsina ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba kan lamarin ba a lokacin da ake kawo wannan rahoto ga jama’a, cewar rahoton Daily Post.
'Yan bindiga na kare al'umma a Katsina
Kun ji cewa wasu mazauna karamar hukumar Jibia a jihar Katsina sun yaba da yadda aka samu kwanciyar hankali bayan sulhu da yan bindiga.
An yi sulhu da yan bindiga a wasu kananan hukumomi a jihar Katsina bayan fama da hare-hare musamman a yankunan karkara wanda ke jawo asarar rayuka da dukiyoyi.
Kamar a Jibia da ke jihar, ’yan bindiga da suka shiga yarjejeniya da al’umma yanzu suna kare kauyuka da dama da ke kusa da su domin tabbatar da zaman lafiya a tsakani.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

