Tinubu Ya Ware Sarki 1 a Arewa, Ya Kwarara Masa Yabo kan Abubuwan Alheri da Yake Yi

Tinubu Ya Ware Sarki 1 a Arewa, Ya Kwarara Masa Yabo kan Abubuwan Alheri da Yake Yi

  • Shugaban kasar Najeriya, Bola Tinubu ya kwarara yabo ga Sarkin Nupe a jihar Niger kan kokarin da yake yi
  • Tinubu ya taya Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar murna bisa cika shekara 73 da kuma zagayowar shekaru 22 a mulki
  • Shugaban ya bayyana Sarkin a matsayin jagora mai son haɗin kai, zaman lafiya da jituwa a fadin ƙasar baki daya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya kira sunan basarake daya a Arewacin Najeriya inda ya yaba masa kan kokarin ya ke yi ga al'umma.

Tinubu ya yabawa Sarkin Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar bisa ga kokarin da yake yi na hada kan al'umma baki daya.

Tinubu ya taya Sarkin Nupe murnar zagayowar ranar haihuwarsa
Shugaba Bola Tinubu yayin taro a birnin Abuja. Hoto: @aonanuga1956.
Source: Twitter

Hakan na cikin wata sanarwa da hadiminsa a bangaren yada labarai, Bayo Onanuga ya wallafa a shafin X a yau Juma'a 12 ga watan Satumbar 2025.

Kara karanta wannan

Sanata Ndume ya 'gano' makircin masu kiran a kori hafsoshin tsaro, ya gargadi Tinubu

Takaitaccen tarihin Sarki Etsi Nupe

An haifi Alhaji Abubakar a 1952, kuma ya yi aiki a rundunar sojoji inda ya riƙe muhimman mukamai kafin ya yi ritaya a matsayin Birgediya Janar.

Ya hau karagar mulki a shekarar 2003 a matsayin Etsu Nupe na 13, abin da ya kafa tarihi ga masarautar Nupe tare da kawo sauyi a masarautar.

Tinubu ya taya Etsu Nupe murnar ranar haihuwa

Tinubu ya taya Etsu Nupe kuma shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya na Jihar Niger, Alhaji Yahaya Abubakar, murna bisa zagayowar haihuwarsa da shekaru 73.

Har ila yau, ya taya shi murnar cika shekaru 22 a karagar mulkin masarautar Nupe a jihar Niger.

Tinubu ya bayyana Sarkin a matsayin ɗan ƙasa nagari da kullum yake amfani da tasirinsa wajen bunƙasa haɗin kai, zaman lafiya da sulhu a ƙasar.

Tinubu ya yi magana kan tasirin Etsu Nupe a Najeriya
Shugaban kasar Najeriya, Bola Tinubu a Abuja. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Gudunmawar da Etsu Nupe ya bayar a Najeriya

Shugaban ya ce tabbas dattijon ya yi namijin kokari wurin tabbatar da zaman lafiya a tsakanin mabambantan addinai da ake da su a Najeriya.

Kara karanta wannan

Da gaske an kwace sarautar da Sarki ya ba Shugaba Tinubu a Arewa? Gaskiya ta fito

Sanarwar ta ce:

“Etsu Nupe ya bayar da gagarumin gudunmawa ga gina ƙasa, ya yi amfani da matsayinsa na girmamawa wajen bunƙasa haɗin kai, jituwa, haƙuri tsakanin addinai, zaman lafiya da sulhu a ƙasar.
“Tsayin daka, jarumtaka da gogewarsa a jagoranci sun kasance ginshiƙai wajen sauke nauyin da ke kansa a matsayin shugaban Masallacin Abuja da kuma shugaban kwamitin haɗin gwiwa na majalisar sarakunan gargajiya ta Najeriya."

Shugaban ya yi masa addu’ar samun tsawon rai, basira da kuma mulki mai ɗorewa cikin kwanciyar hankali da ci gaba ga masarautar Nupe.

Shugaba Tinubu zai yi jawabi ga yan kasa

A baya, mun ba ku labarin cewa gwamnatin tarayya ta fara shirya bukukuwan da za a yi a ranar 1 ga watan Oktoban 2025, watau ranar samun yancin kai.

Daya daga cikin abubuwan da aka tsara za a yi a ranar 'yancin shi ne jawabin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.

Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume ya kaddamar da kwamitin da zai jagoranci shirya bukukuwan wannan rana domin tabbatar da yinsa cikin nasara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.