Netanyahu Ya Yi Barazanar Sake kai Hari Qatar, Ya Kafa wa Kasar Larabawan Sharadi
- Shugaban Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya ce ƙasarsa na iya sake kai hari Qatar idan ba ta kori Hamas daga ƙasarta ba
- Qatar ta yi tir da harin da Isra’ila ta kai a Doha, tana kiran shi take hakkin kasa da kasa da barazana ga tsaron ƙasar
- Hakan na zuwa ne bayan Donald Trump ya bayyana cewa bai amince da harin ba, yana mai cewa ba zai sake faruwa a Qatar ba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Qatar – Shugaban Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya yi gargadin cewa ƙasarsa za ta iya sake kai farmaki Qatar idan aka ƙi korar shugabannin Hamas daga ƙasar.
Wannan na zuwa ne kwanaki bayan Isra’ila ta kai wa wasu shugabannin Hamas farmaki a Doha, babban birnin Qatar.

Source: Getty Images
Rahoton CBS ya nuna cewa Benjamin Netanyahu ya sake wata barazanar kai hari da wasu zarge zarge wa Isra'ila.
Farmakin farkon da ya jawo mutuwar mutane da dama ya tayar da muhawara a duniya, musamman ganin Qatar ƙasa ce da ke da alaƙa ta kut-da-kut da Amurka.
Biyo bayan lamarin, a ranar Alhamis aka gudanar da jana'izar waɗanda suka mutu a Babban Masallacin Doha.
Harin Isra’ila da martanin Qatar
Isra’ila ta kai harin ne a ranar Talata inda ta ce ta kai farmaki kan shugabannin Hamas da ke gudanar da taro a Doha.
Wannan lamari ya girgiza dangantakar diflomasiyya, kasancewar Doha na zama cibiyar muhimmin tattaunawa tsakanin Hamas da sauran ƙasashe.
Qatar ta bayyana farmakin a matsayin “harin ta’addanci” da ya sabawa ka’idoji, tare da jaddada cewa ƙasarta ba za ta amince da irin wannan cin zarafi ba.
Matsayar Amurka da Trump kan harin
Amurka ta dade tana amfani da Qatar wajen shiga tsakani da Hamas domin tattaunawa kan tsagaita wuta.
Kasar ta kuma mallaki babban sansanin sojojinta a Gabas ta Tsakiya a Al-Udeid, inda daruruwan dakarun Amurka ke sansani.

Source: Getty Images
Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa Isra’ila ta sanar da Amurka kafin kai farmakin, amma ba ta yi haɗin kai da ita ba wajen tsara shi.
Duk da haka, Trump ya bayyana cewa burin kawar da Hamas yana da muhimmanci, amma ya tabbatar da cewa ya sanar da Qatar cewa irin wannan farmaki ba zai sake faruwa a ƙasarsu ba.
Netanyahu zai sake kai hari a Qatar?
Sai dai Netanyahu ya dage wajen kare matakin, yana mai cewa sun kai farmakin ne domin kama shugabannin da ya ce sun shirya kisan kiyashi a Isra'ila.
Rahoton Jerussalem Post ya nuna cewa ya yi wa Qatar barazana da cewa duk ƙasar da ta ba da mafaka ga Hamas ko ta ƙi miƙa su, Isra’ila za ta ɗauki mataki kai tsaye.
An kashe mai goyon bayan Isra'ila
A wani rahoton, kun ji cewa wani dan bindiga ya harbe dan gwagwarmayar da ke goyon bayan kisan kiyashi da ake Gaza.
Rahotanni sun bayyana cewa shugaban Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya yi Allah wadai da kisan da aka yi wa Charlie Kirk.
A daya bangaren, shugaba Donald Trump ya ce kisan abin takaici ne matuka kuma kuma zai dauki mataki kan wanda ya yi laifin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


