Jama'a za Su Caba, Gwamna Abba Ya Mara wa Dokar 'Yancin Kananan Hukumomi baya

Jama'a za Su Caba, Gwamna Abba Ya Mara wa Dokar 'Yancin Kananan Hukumomi baya

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa lokaci ya yi na tabbatar wa kananan hukumoni 'yancin gashin kansu
  • Ya ce zai yi tsayin daka wajen ganin kananan hukumomi sun samu damar cin gashin kansu musamman ta fannin kudi
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa sabuwar dokar za ta bai wa kananan hukumomi cikakken 'yanci ci gaba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya tabbatar da cikakken goyon bayansa ga wata sabuwar doka da za ta bai wa kananan hukumomi 44 'yancin kai.

Gwamnan ya bayyana cewa yana kan bakar bai wa kananan hukumomi cikakken 'yanci da cin gashin kansu, musamman ta fannin juya kudinsu a jihar Kano.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun shiga uku, gwamna zai gina sabon sansanin sojoji na musamman a Kebbi

Gwamna Abba ya goyi bayan yancin kananan hukumomi
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Wannan na kunshe a cikin sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Juma’a a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Abba zai ba kananan hukumomin 'yanci

Sanarwar ta ce gwamnan ya bayyana goyon bayansa ne yayin da yake jagorantar taron majalisar zartarwa na 31 a Kwankwasiyya City.

A yayin taron, majalisar ta amince da mika kudirin dokar zuwa ga Majalisar Dokokin Jihar Kano domin fara nazari da bitar sa.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa wannan matakin zai taimaka wajen inganta harkokin mulki a matakin ƙasa da kuma gaggauta ayyukan ci gaba a al’umma.

Gwamna ya ce 'yancin kananan hukumomi zai taimaki jama'a
Hoton gwamnan Kano a bikin ranar ma'aikata Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Gwamna Abba ya bayyana cewa sabuwar dokar da ake kokarin kafawa za ta bai wa kananan hukumomi damar sarrafa dukiyarsu kai tsaye ba tare da tsangwama daga gwamnatin jiha ba.

Gwamnan Kano ya ce kananan hukumomi za su caba

A cewarsa, tabbatar da yancin zai rage jinkiri wajen aiwatar da ayyuka da kuma bada damar daukar matakai da suka dace da bukatun jama'a a matakin ƙasa.

Kara karanta wannan

Gwamna Uba Sani ya yi wa 'yan siyasa shagube, ya fadi bammbancinsa da su

Ya ce:

"’Yancin kananan hukumomi muhimmin ginshiki ne wajen tabbatar da nagartaccen mulki, ingantaccen lissafi da kuma kara hanzarta ci gaban al’umma."

Gwamnan ya kara da cewa wannan matakin wani bangare ne na zurfafa tsarin dimokuradiyya a jihar Kano, kuma yana da yakinin cewa 'yan majalisar dokoki za su goyi bayan kudirin.

A karshe, Gwamna Abba ya bukaci hadin kan kowa da kowa wajen ganin an cimma wannan buri domin dorewar ci gaba da gaskiya a tsarin mulkin kananan hukumomi a jihar Kano.

Gwamnatin Kano magantu kan ba mata tallafi

A wani labarin, mun wallafa cewa gwamnatin Kano ta ce wasu daga cikin mata marasa galihu da masu rauni ba su karɓi tallafin N50,000 ba bisa dalilan da suka shafi yawan masu cancanta.

Kwamishinan harkokin mata ta jihar Kano, Hajiya Amina Sani Abdullahi, wacce Daraktan bincike da tsare‑tsare na ma’aikatar, Yakubu Muhammad, ya wakilta ce ta bayyana haka ga manema labarai.

Kara karanta wannan

Bayan tsawon lokaci, gwamna ya tabbatar da fara tattaunawar sulhu da 'yan bindiga

Amma kuma, a cewar ta, gwamnatin Kano tana aiki tukuru don ganin an kai wannan tallafi ga duk wanda ya dace domin rage masu radadin rayuwar da su ke fama da shi yau da gobe.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng