Boko Haram: Gwamnatin Yobe Ta Tsage Gaskiya kan Kisan Mutum sama da 80

Boko Haram: Gwamnatin Yobe Ta Tsage Gaskiya kan Kisan Mutum sama da 80

  • Gwamnatin Yobe ta karyata labarin kisan mutane 84 a ƙauyen Mafa, da ke ƙaramar hukumar Tarmuwa a jihar
  • Rundunar ‘yan sanda da gwamnatin jihar sun bayyana labarin a matsayin ƙarya da aka fitar domin yaudarar jama'a
  • Sun bayyana cewa labarin da aka ruwaito na kisan ya faru ne a bara, ba a kwanan nan ba kamar yadda ake wasu ke fada

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Yobe – Gwamnatin jihar Yobe ta yi watsi da wani rahoto da ya yi ikirarin cewa an kashe akalla mutane 84 a harin ‘yan bindiga a ƙauyen Mafa na ƙaramar hukumar Tarmuwa.

Wannan na cikin sanarwar da sakataren yaɗa labarai na shugaban ƙaramar hukumar Tarmuwa, Bulama Jalaludden da Daraktan yaɗa labarai na gwamna, Mamman Mohammed, suka fitar a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Shirin kifar da Tinubu: Peter Obi ya gana da Goodluck Jonathan a Abuja

Gwamnatin Yobe ta ƙaryata harin Boko Haram
Hoton gwamnan Yobe Mai Mala Buni Hoto: Mamman Mohammed
Source: Twitter

Tun da fari, Kwamishinan yaɗa labaran jihar Yobe, Abdullahi Bego ne ya fara ƙaryata labarin a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ƙaryata labarin hari Boko Haram a Yobe

Jaridar Punch ta wallafa cewa mahukunta a jihar Yobe sun bayyana rahoton a ƙazamin kisan a matsayin ƙarya, kuma marar tushe ko makama.

Rahoton da aka fitar ya ce kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Dungus Abdulkarim, na cewa wasu da ake zargin mayakan Boko Haram sama da 150 sun shiga ƙauyen a kan babura 50, dauke da bindigu.

An ruwaito cewa an kashe mutane 84 tare da gudanar da jana’izarsu a Babangida, hedikwatar ƙaramar hukumar, a ranar Laraba.

Amma daga baya, jaridar ta amince da kuskure, inda ta bayyana cewa abin da aka ruwaito ya faru a bara ne, ba a wannan shekara ba.

Gwamnatin jihar Yobe ta shawarci jama'a

A cikin sanarwar, Shugaban ƙaramar hukumar Tarmuwa ya bayyana takaicin yadda aka dawo da labarin da ya faru bara a matsayin wanda ya faru a makon nan

Kara karanta wannan

"Ina kan bakata," Abba Gida Gida ya yi maganar yadda ya tsira da kujerarsa

Ya ce:

“Babu wani hari da ya auku a Mafa ko a kowace unguwa a cikin Tarmuwa a watan Satumba 2025. Babu kuma wata jana’iza da aka gudanar kamar yadda aka ruwaito. Labarin duk ƙarya ne kuma ba shi da wani tushe.”

Ya bukaci jama’a su kwantar da hankalinsu, yana mai cewa hukumomin tsaro na ci gaba da aiki tare da shugabannin yankin don tabbatar da zaman lafiya.

Yan sanda sun ƙaryata hari a Yobe
Hoton Sufeton ƴan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

Haka kuma, mai magana da yawun gwamnan ya bayyana cewa rahoton ya jawo tashin hankali da damuwar zuciya ga jama’ar yankin ba gaira babu dalili. Ya ce:

“Ƙauyen Mafa a Tarmuwa da ma jihar Yobe gaba ɗaya na cikin kwanciyar hankali, kuma al’umma na ci gaba da harkokinsu cikin lumana. Rundunar ‘yan sanda, ofishin mai ba gwamna shawara kan harkokin tsaro da shugaban ƙaramar hukumar Tarmuwa dukkanninsu sun karyata wannan labari."

Gwamnatin ta bukaci jama’a da su yi watsi da rahoton baki ɗaya, tana mai cewa babu ƙamshin gaskiya ko ɗigo ɗaya a cikin labarin.

Kara karanta wannan

Kungiyar TUC ta ja daga, ta ba gwamnatin Tinubu kwanaki 14 ta janye harajin fetur

Boko Haram ta kashe sojoji a Yobe

A baya, kun samu labarin cewa wasu da ake zargin ‘yan Boko Haram ne sun kai hari mai tsanani kan sansanin sojoji a karamar hukumar Gujba, jihar Yobe.

A yayin mummunan harin, an kashe sojoji hudu, tare da lalata kayan aikin soja da dama a rundunar ta 27 dake Buni Yadi, lamarin da ya jawo zaman ɗar-ɗar.

Harin ya faru kasa da awa 24 bayan taron gwamnonin Arewa maso Gabas da suka yi a Damaturu, inda suka tattauna yadda za a ƙara kaimi wajen yaki da ta’addanci.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng