NNPCL: Mele Kyari Ya Yi Magana bayan EFCC Ta Masa Tambayoyi kan Almundahana
- Tsohon shugaban NNPCL, Mele Kyari ya yi magana ga manema labarai bayan hukumar EFCC ta sake shi a Abuja
- Ana binciken Mele Kyari ne a kan zargin hada baki da karkatar da makudan kudi da suke da alaka da kamfanin NNPCL
- A baya kotun tarayya ta bayar da umarnin rufe wasu asusun banki da ake dangantawa da shi kan zargin da ake yi masa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon shugaban kamfanin man fetur na kasa (NNPCL), Mele Kyari, ya yi bayani bayan da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta yi masa tambayoyi.
Rahotanni sun nuna cewa EFCC ta kama Mele Kyari ne kan zargin almundahana a lokacin shugabancinsa.

Source: Facebook
Vanguard ta wallafa cewa Kyari ya isa hedikwatar EFCC da ke Jabi, Abuja, da misalin ƙarfe 2:15 na rana a ranar Larabar da ta wuce.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Maganar Mele Kyari bayan tambayoyin EFCC
Rahotanni sun nuna cewa an yi wa Mele Kyari tambayoyi ne kan zargin haɗa baki, karya ka'idar aiki da kuma karkatar da kudi.
Bayan kammala ganawar, Kyari ya shaida wa manema labarai cewa:
“Na yi nawa, sauran kuma ya rage na EFCC. Idan kowa ya yi abin da ya dace cikin gaskiya da mutunci, Najeriya za ta cigaba.”
Dalilin gayyatar Mele Kyari inji EFCC
Tambayoyin da aka yi wa Kyari sun biyo bayan ci gaba da bincike kan harkokin kuɗi da ake zarginsa da hannu a ciki.
Punch ta wallafa cewa tun a baya EFCC ta kai ƙara kotun tarayya da ke Abuja domin samun izinin rufe wasu asusun banki da ake cewa suna da alaƙa da shi.

Source: Facebook
A watan Agusta, mai shari’a Emeka Nwite ya bayar da umarnin rufe asusun banki huɗu a Jaiz Bank da ake alakantawa da Kyari.
Hukumar ta nemi kwanaki 60, amma kotu ta amince da kwanaki 30, tare da yiwuwar sabunta rufewar idan akwai buƙata.
Matsayin Kyari game da zarge-zargen
Ko da yake bai yi tsokaci sosai ba kan tuhumar da ake yi masa, Kyari ya dage cewa ya kamata a bar EFCC ta yi aikinta ba tare da katsalandan ba.
Ya ce shi ya riga ya yi na shi aiki wajen jagorantar NNPCL a lokacin da aka yi babban sauyi daga tsohon tsarin NNPC zuwa kamfanin kasuwanci.
Kyari, wanda aka nada a matsayin shugaban NNPC a 2019 sannan ya cigaba a matsayin shugaban NNPCL bayan sauyin tsarin a 2021 ya bar mukaminsa a Yulin 2025.
Har yanzu EFCC ba ta bayyana ko za a gabatar da tuhume-tuhume a gaban kotu ba, amma majiyoyi sun tabbatar da cewa binciken yana ci gaba.
Hukumar EFCC ta gurfanar da 'yan PDP
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa ta gurfanar da wasu 'yan PDP a gaban kotu.
Rahotanni sun nuna cewa an gurfanar da mutanen ne kar zargin amfani da kudi ba bisa ka'ida yayin zaben cike gurbi a Kaduna.
'Yar takarar jam'iyyar PDP da ta nemi kujera a majalisar wakilai a jihar Kaduna da jami'in yakin neman zabenta aka gurfanar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


