Gwamnan Bauchi Ya Kori Malamin Makaranta daga Aiki bayan Ya Aikata Babban Laifi

Gwamnan Bauchi Ya Kori Malamin Makaranta daga Aiki bayan Ya Aikata Babban Laifi

  • Wani babban malami a jihar Bauchi, mai suna Emos Joshua, ya rasa aikinsa bayan samunsa da laifin lalata da daliban makaranta
  • Hukumar ta ce Joshua ya karya dokokin aikin gwamnati, musamman sashe na 0327, da ya tanadi hukunci ga cin zarafin dalibai
  • Hukumar kula da ma’aikatan gwamnatin Bauchi ta kuma daukaka darajar wasu jami’ai, da karin girma ga ma’aikatan jinya 80

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Bauchi - Gwamnatin jihar Bauchi ta kori wani malamin makaranta mai suna Emos Joshua bisa zargin cin zarafin dalibai.

Joshua, wanda shi ne mataimakin shugaban kwalejin gwamnati da ke Azare, sashen ilimi, ya rasa aikinsa bayan hukuncin da hukumar kula da ma'aikatan gwamnati ta jihar Bauchi ta yanke.

Gwamna Bala Mohammed ya amince da korar wani babban malami saboda kamashi da laifin cin zarafin dalibai.
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed yana jawabi a dakin taron gidan gwamnati. Hoto: @SenBalaMohammed
Source: Facebook

An kori malamin makaranta a Bauchi

Mai magana da yawun hukumar CSC, Saleh Umar, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Bauchi, inji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: Gwamnati ta bankado ma'aikatan bogi a Bauchi, za su fuskanci hukunci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Saleh Umar, ya ce an amince da korar Joshua ne a zaman kwamitin hukumar CSC na 32 da aka gudanar ranar 11 ga Satumba.

Ya bayyana cewa abin da tsohon ma’aikacin ya aikata ya saba da sashe na 0327 (xxviii da xxix) na dokokin aikin gwamnati na jihar Bauchi da suka shafi cin zarafi.

Sanarwar ta ce an dauki wannan hukunci ne bayan an kammala duk matakan ladabtarwa da aka tanada a karkashin dokokin ma’aikata na 0317.

Sanarwar ta ce:

"An dauki matakin ladabtarwa a kan malamin ne bayan an bi duk matakan da suka dace kamar yadda sashe na 0317 na dokokin aikin gwamnati ya tanada."

Gwamnati ta daukaka matsayin wasu ma'aikata

Saleh Umar ya ce hukumar ta kuma daga darajar wasu mataimakan daraktoci biyu zuwa daraktoci a ma'aikatar tsare-tsare da raya kasa, a matakin aiki na 16.

Haka kuma, wani wani babban jami'in tsare-tsare ya samu karin mukami zuwa mataimakin darakta a matakin aiki na 15.

Kara karanta wannan

Mamakon ruwa ya 'daidaita jama'a a Kaduna, sama da mutum 500 sun rasa matsuguni

A daya bangaren kuma, ma’aikata 80 na bangaren jinya, ciki har da jami'an nasin (NO) da kuma Sufuritandan nasin (NS), sun samu karin girma daga mataki na 10 zuwa 14.

Kakakin hukumar ya ce an dauki wadannan matakan ne bisa ga shawarwari da aka samu daga hukumar kula da makarantu ta musamman ta jihar Bauchi, hukumar kula da sayayya da tsare-tsare ta jihar, da kuma hukumar kula da lafiya.

Gwamnatin Bauchi ta daga darajar wasu ma'aikata tare da kara girma ga ma'aikatan jinya 80.
Taswirar jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabashin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

'An yi adalci a korar malamin' - Shugaban CSC

Da yake tsokaci game da korar Joshua, shugaban hukumar CSC, Dakta Ibrahim Muhammad, ya bayyana cewa an yi duk abin da doka ta tanada wajen yanke hukuncin.

Jaridar Vanguard ta rahoto Ibrahim ya ce an bi tsarin da ya dace, kuma ya sake nanata aniyarsu ta tabbatar da adalci da gaskiya wajen gudanar da al'amuran ma'aikata.

A karshe, Ibrahim ya ce:

"Wannan mataki da aka dauka ba wai an yi shi ne domin hukunta malamin ba, sai don tabbatar da ladabtarwa da rikon amana a cikin aikin gwamnati."

Ya ce matakin ladabtarwa zai zama gargadi ga ma'aikata cewa bin dokokin aiki yana da matukar muhimmanci domin a samu ingantaccen aikin gwamnati mai cike da rikon amana.

Kara karanta wannan

Talauci ya addabi Sokoto, za a dauki ma'aikata domin rage fatara da yunwa

An dakatar da kwamishinan lafiya a Kebbi

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan Kebbi, Dr. Nasir Idris, ya amince da dakatar da kwamishinan lafiya na jihar, saboda sakaci da aiki.

Gwamnatin Kebbi ta kuma umarci kwamishinan da aka dakatar da ya ba da hujjojin da za su hana a dauki wasu karin matakan ladabartarwa a kansa.

Dakatarwar na zuwa ne jim kadan bayan da wani dan jarida ya wallafa bidiyon halin da asibitocin jihar ke ciki, inda majinyata ke kwanciya a gado ba katifu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com